Wata tawagar jami'an Somalia ta tashi daga birnin Mogadishu zuwa Turkiyya, inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin Somaliya da Habasha.
Tattaunawar dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin warware taƙaddamar da ke tsakanin ƙasashen na Gabashin Afirka da ke maƙwabtaka da juna, kan yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da Addis Ababa ya sanyawa hannu da yankin Somaliland da ya ɓalle daga Somalia, lamarin da ya harzuƙa Mogadishu.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Somalia ta fitar ta ce, "tawagar ƙarkashin jagorancin ministan harkokin waje da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa Ahmed Moallim Fiqi Ahmed ta tashi zuwa Ankara babban birnin Turkiyya a ranar Asabar.”
“Tawagar da ke wakiltar gwamnatin Somaliya, ta samu goron gayyata a hukumance daga gwamnatin Turkiyya, kuma za ta halarci zagaye na biyu na tattaunawa da ƙasar Habasha, wacce gwamnatin Turkiyya ke karɓar bakunci,” a cewar sanarwar.
A ranar Litinin ne za a fara tattaunawar a Ankara, makonni uku gabanin yadda aka tsara tattaunawar tun da farko.
Shi ma ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya sanar a ranar Juma'a cewa za a ci gaba da tattaunawar.
Sanarwar ta zo ne mako guda bayan ya ziyarci Addis Ababa inda ya gana da Firaministan Habasha Abiy Ahmed.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da firaministan Habasha Abiy Ahmed ta waya dangane da alaƙar ƙasashen biyu, da rikicin yankin, da kuma ci gaban duniya.
Shugabanin biyu sun tattauna muhimman fannonin haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Habasha, inda suka yaba da yadda dangantakar ke ci gaba da haɓaka a tsakanin ƙasashen biyu, in ji Ofishin Sadarwa na Turkiyya a ranar Juma'a a cikin wata sanarwa ta X.
Samun damar teku
A yayin tattaunawar, Erdogan ya bayyana irin ƙoƙarin da Turkiyya ke yi na sasanta rikicin Somaliya da Habasha.
A watan da ya gabata ne Turkiyya ta fara yunƙurin shiga tsakani don sasanta rikicin Habasha da Somalia, inda aka yi tattaunawar farko a Ankara, inda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya karɓi baƙuncin ministocin harkokin wajen ƙasashen biyu.
Zaman tankiyar da ke tsakanin Somalia da Habasha ya samo asali ne daga yarjejeniyar shiga tashar jiragen ruwa da Addis Ababa ta sanyawa hannu a watan Janairu da yankin Somalia na Somaliland da ya ɓalle.
An yi yarjejeniyar ne don bai wa Habasha da ba ta da teku damar shiga teku ta yankin Somaliland, ita kuma za ta amince da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, matakin da Somalia ta ƙi amincewa da shi.