Isra'ila na aikata laifukan yaki a kan idon duniya baki daya. Kuma tana nuna zallan mummunar mugunta da kama-karya da mulkin wariyar launin fata, "in ji daraktan sadarwar. / Photo: AA

Isra'ila na gudanar da "wani mummunan kamfe na yaɗa labaran ƙarya" a yayin da take ci gaba da kisan kiyashi ta hanyar "aikata manyan laifukan yaƙi", in ji Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun.

Altun ya bayyana hakan ne a wajen taron Kimiyyar Sadarwa da Kasa da Ƙasa (ICOMS) da Jami'ar Sakarya da TUBİTAK ta shirya a ranar Litinin.

Isra'ila na aikata laifukan yaki a kan idon duniya baki daya. Kuma tana nuna zallan mummunar mugunta da kama-karya da mulkin wariyar launin fata, "in ji daraktan sadarwar.

Altun ya bayyana cewa Isra'ila tana "kokarin halattawa da yin kisan gillar da ba a iya gani" ga Falasdinawa da yaran da mata da tsofaffi da 'yan jarida da ma'aikatan kiwon lafiya a Gaza, a takaice dai ga dukkan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba "ta hanyar yaɗa labaran ƙarya."

"Amma ya kamata su san cewa sarai mun san masu ruwa da tsakin da ke ƙoƙarin tabbatar da munanan shirye-shiryesnu a Gaza da Falasdiny da kuma yankunan da ke kusa da mu kuma a shirye muke mu yi faɗa da su har sai mun ga abin da zai ture wa buzu naɗi," ya ƙara da cewa.

"Dole masu aikata kisan gilla a Gaza su girbe abin da suka shuka."

"Kamar yadda al'umma suke yin tir da su, to haka ma kotunan shari'a za su yi Allah wadai da su a yayin da ƙasashen duniya suka ƙaddamar da shar'a a kansu," in ji Altun.

Tashe-tashen hankula na ƙaruwa a yankunan Falasɗinu a yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza, tun bayan harin ba-zata da Hamas da ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Fiye da Falasdinawa 11,100 aka kashe da suka hada da yara da mata sama da 8,000 a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da ta kasa a Gaza tun watan da ya gabata.

Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila ya kusan 1,200, a cewar alkaluman hukuma.

TRT World