Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada cewa, ba za a iya yin biris ga farfagandar watsa labaran ƙarya da Isra'ila ke yaɗawa ba, domin irin wannan halin ko in kula na iya haifar da a dinga ganin kamar laifukan da ƙasar ke aikatawa daidai ne.
Da yake jawabi a wani taron da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya shirya a ranar Talata, Altun ya bayyana cewa, “Tare da irin wadannan abubuwan, da ayyukan da muke yi a fagen, da kuma hotunan da muke tattarawa, za mu rubuta bayanai kan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi ba a matsayin ‘zargi’ ba amma a matsayin ‘tabbatacciyar shaida, da tabbatattun laifukan yaƙi.' Yunƙurinmu yana kan wannan al'amari."
"A yau Isra'ila na aikata wani babban laifi na kisan ƙare dangi a Gaza. Isra'ila ta aikata kuma tana ci gaba da aikata manyan laifuka da dama da aka sanya su a karkashin yarjejeniyar Rum, musamman kisan kiyashi."
"Kisan ƙare dangi ba wai aikin kashe jama'a ba ne kawai. Kisan ƙare dangi wani babban hari ne akan zahiri da ruhin mutane. Isra'ila ba kawai tana kashe mutanen da ke zaune a Gaza a lokaci guda ba ne, har ma da yin kisan ƙare dangi na al'adu don lalata rayuwar kafatanin yankin," in ji shi.
"Isra'ila na ƙoƙarin kawar da wanzuwar mutane gaba ɗaya da su da al'adunsu. Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Rafah, inda ta kori mutane a 'yan kwanakin nan, babban misali ne na manufofinta na kisan kare dangi," Altun ya faɗa.
Babban jami'in ya kuma ja hankali kan muhimmancin littafin da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya wallafa mai ɗauke da hotunan da ke tabbatar da laifukan da Isra'ila ke aikatawa a Gaza, wanda aka gabatar da shi ga kotun ƙasa da ƙasa (ICJ).
Farfagandar watsa labaran ƙarya
A yayin da yake jaddada ƙoƙarin da Isra'ila ke yi na ɓoye kisan kiyashin da take yi a Gaza, Altun ya ce: "A saboda wannan dalili Isra'ila na ci gaba da gudanar da yaɗa farfagandar watsa labaran ƙrya, wanda ita kanta gwamnatin ƙasar ta shirya, domin kare zalunci da rashin tausayin da take nuna wa Falasdinawa, musamman a Gaza."
Ya ƙara da cewa, "Idan muka rasa hankali, to za a maye gaskiya ne da labaran ƙarya. Idan muka rasa hankali, to za mu zo mu daina ganin laifukan Isra'ila tare da hana hukunta ta."
"Cibiyarmu ta yaƙi da labaran ƙarya ta gano farfaganda kusan 200 da Isra'ila ke yi tun daga ranar 7 ga Oktoba," in ji Altun, yayin da yake magana kan Sashen Yaƙi da Labaran Ƙarya na Cibiyar Sadarwar ta Turkiyya. Altun ya tuna cewa kai tsaye Isra'ila na kai hari tare da kashe 'yan jaridar da ke kokarin isar da gaskiya a yankin.
"Ba arashi ba ne a ce kashi 75 na 'yan jaridan da aka kashe a shekarar 2023 sun rasa rayukansu a Gaza."
Ya ƙara da cewa, ya zuwa yanzu, Isra'ila ta kashe 'yan jarida 130 a lokacin da suke bakin aiki, ciki har da wani mai ɗaukar hoto na kamfanin dillancin labaran Turkiyya Anadolu, Montaser Al Sawaf. "Za mu yi iya kokarinmu don hana ayyukan Isra'ila da nufin ɓoye gaskiya da karkatar da gaskiya daga cin nasara," in ji Altun.
"Abin takaici, yayin da muke yin wannan kokarin, wani ɓangare mai yawa na kafofin yaɗa labaran Yammacin Duniya kuma suna aiki tuƙuru wajen ƙin bayyana kisan kiyashin da Isra'ila ke yi."
Isra'ila ta kaddamar da wani mummunan hari a Gaza bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba. Harin da Isra'ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 29,000 tare da jikkata wasu fiye da 69,000.
Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya tilasta wa kashi 85 cikin 100 na al'ummar yankin tserewa daga gidajensu sakamakon tsananin ƙarancin abinci da ruwan sha da magunguna, yayin da kashi 60 cikin 100 na ababen more rayuwa na yankin suka lalace, a cewar MDD.
Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Wani hukunci na wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukan kisan kiyashi tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jinƙai ga fararen hula a Gaza.