Dakarun tsaron Turkiyya sun samu nasarar kama mambobin kungiyar ta'addanci ta FETO biyu.
A farmakin da Hukumar Leken Asirin Turkiyya tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaro ta Kasa ta Turkiyya suka shirya tare da kaiwa, an kama 'yan ta'addar FETO biyu da aka bayyana sunayensu da Mustafa Bircan da Mustafa Tan.
Tan da Bircan na aiki sosai a reshen kungiyar ta'addar FETO a Aljeriya.
Bayan farmakin na hadin gwiwa an gano cewa mambobin na FETO biyu, Tan da Bircan ne ke da alhakin kula da ayyukan kungiyar a Aljeriya, inda suke ci gaba da tabbatar da reshen kungiyar na Amurka na aiki tare da na Aljeriya, suna kuma bai wa kungiyar kudade.
Farmakin na hadin gwiwa da aka kai cikin nasara na bayyana kokarin mahukuntan Turkiyya wajen kakkabe 'yan ta'addar FETO a duk inda suke a duniya.
Ana sa ran 'yan ta'addar biyu da aka kama za su gurfana a gaban kotun Turkiyya saboda hannu da suke da shi a ayyukan ta'addanci.
Wace kungiya ce FETO?
Kungiyar ta'addanci ta FETO da shugabanta da ke Amurka Fethullah Gulen ne suka yi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 15 ga Yuli, 2016, wanda ya yi ajalin mutum 251, aka jikkata wasu 2,734.
'Yan ta'addar FETO sun dinga ayyukan neman kifar da gwamnati ta hanyar zuba mambobinta a hukumomin Turkiyya da suka hada da rundunonin soji da 'yan sanda, da bangaren shari'a.
Amurka na bayar da kariya ga 'yan ta'adar FETO da yawa, wadanda mafi yawan su suka gudu daga Turkiyya bayan sun gaza ƙwace iko da kasar da suka so yi ta hanyar yunkurin kifar da gwamnati da sojojinsu suka yi.
Fethullah Gulen ne mamban kungiyar FETO da aka fi nema ruwa a jallo, kuma yana zaune a Amurka tun shekarar 1999.