Gwamnatin Holand za ta taimaka wajen sake gina yankunan Tukiyya da girgizar kasa ta lalata

Gwamnatin Holand za ta taimaka wajen sake gina yankunan Tukiyya da girgizar kasa ta lalata

Ministan Harkokin Kasuwancin Kasashen Waje na Holand Schreinemacher ya ziyarci yankin Hatay na Turkiyya.
Kasashen duniya daban-daban na nuna goyon baya ga Turkiyya/ Photo: AA

Ministan Kasuwancin Kasashen Waje da Hadin Kan Cigaba na Holand Liesje Schreinemacher ya bayyana aniyar kasarsa na bayar da gudunmawa don sake gina yankunan da girgizar kasa ta lalata a Turkiyya.

Da yake bayyana bakin cikinsa game da ibtila’in, Schreinemacher ya jaddada cewar Holand da ma duniya baki daya sun shirya bayar da gudunmawa wajen sake gina yankunan na Turkiyya.

Ministan ya kuma ziyarci Masallacin Sarimiye, Cocin Katolika ta Antioch da kuma Masallacin Habibi Najjar mai dimbin tarihi wadanda su ma girgizar kasar ta lalata.

A ranar 6 ga Fabrairu ne tagwayen girgizar kasa masu karfin awo 7.7 da 7.6 suka auka wa lardunan Turkiyya 11 na Adana, Adiyaman, Diyarbakir, Elazig, Hatay, Gaziantep, Kahramanmaras, Kilis, Malatya, Osmaniye, da Sanliurfa.

Girgizar kasar ta shafi sama da mutane miliyan 13.5 a Turkiyya.

AA