Likitocin Koriya ta Kudu za su kula da mazauna yankunan da aka samu girgizar kasa a Turkiyya

Likitocin Koriya ta Kudu za su kula da mazauna yankunan da aka samu girgizar kasa a Turkiyya

Ma’auratan sun bayyana godiyarsu ga Turkiyya saboda taimakon da ta ba su a lokacin yakin Koriya.
Jama'a na ci gaba da murmurewa a yankunan da girgizar kasa ta afku a Turkiyya/ Photo: AA

Wasu ma’aurata likitoci Victoria da Paul Cho ‘yan kasar Koriya ta Kudu sun sadaukar da kawunansu wajen bayar da taimako ga al’ummar yankin Iskenderun na lardin Hatay da girgizar kasa ta shafa a Turkiyya.

Likitocin sun bayyana godiyarsu ga Turkiyya saboda taimakon da ta bai wa kasarsu a lokacin yakin Koriya, kuma sun rufe asibitinsu na jihar California ta Amurka inda suka tafi Turkiyya don taimaka wa wadanda girgizar kasar ta shafa.

Likitocin na duba mutanen yankin ta hanyar amfani da dabarar ‘Acupuncture’ da ake amfani da wata ‘yar allura a cikin jikin mutum.

Likitocin da suka kware wajen kula da marasa lafiya, na aiki a budadden asibitin da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Turkiyya ta kafa a yankin Iskenderun.

A tattaunawar su da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Paul Cho, mai shekaru 65, ya bayyana cewa bayan da suka samu labarin aukuwar girgizar kasar ne sai suka yanke shawarar tahowa Turkiyya.

Ya tunatar da cewa Turkiyya ta aika da sojoji zuwa kasarsa don bayar da gudunmawa a yakin Koriya.

Ya ce “Turkiyya ta taimaka mana, ba za mu taba mantawa ba, hakan ya sanya muka zo nan.”

A ranar 6 ga Fabrairu ne tagwayen girgizar kasa suka auku a kudu maso-gabashin Turkiyya inda sama da mutane dubu hamsin suka rasa rayukansu a larduna goma sha daya da ke yankin.

AA