A Ranar Nuna Goyon Baya ga Al'ummar Falasdinu ta Duniya, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya jaddada goyon bayansa ga Falasdinu.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X a ranar Juma'a, ya ce: "A shirye muke mu yi namu bangaren, ba da hannunmu kadai ba, har ma da dukkan jikinmu, don dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da bude hanyar samun zaman lafiya mai dorewa."
Ya kuma kara da cewa, tun a rana ta farko Turkiyya take ta ɗaga murya na nuna adawa da ta'asar da ake yi a Gaza.
Da yake tsokaci kan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza, wanda yakin Isra'ila ya rutsa da su ya ce: “Idan muka ga yara suna jira a layin abinci tsawon sa’o’i a cikin ruwan sama da laka ga kwanon miya a hannunsu, zukatanmu suna karaya, shin duk wanda ke da zuciya in dai ba ta dutse ba ce a jikinsa, zai iya yin shiru a gaban irin wadannan abubuwa na masifa?
A ci gaba da jaddada goyon bayansa ga Falasdinawa a Gaza, Shugaba Erdogan ya bayyana tsananin tausayinsa ga wadanda ake zalunta yayin da ya kuma yi fatali da kawayen Isra'ila kan goyon bayanta da suke yi a yakin da Tel Aviv ke ci gaba da yi a Gaza.
"Zaluncin da ake yi wa mutane a Gaza da Falasdinu da Lebanon abu ne da ya dame mu duka, kuma hakan ya kamata. Goyon bayan zalunci ma zalunci ne. Kuma duk mai goyon bayan azzalumi goyon bayan zalunci yake yi," ya ce.
A yayin da yake tsokaci kan irin gagarumar rawar da Turkiyya ta taka a baya, ya bayyana rashin nuna son kai na kasarsa wajen tsayawa tsayin daka kan wadanda ake zalunta.
"Mu al'umma ce da a tarihi muka bude kofofinmu ga duk wanda aka zalunta, Yahudawa ko Kirista. A duniyar tunaninmu, ba a la'akari da asalin wanda aka zalunta ko akidar azzalumi".
Da yake ishara da mummunan yakin da Isra'ila take yi a Gaza shugaban na Turkiyya ya yi fatan kawo karshen abin da ya kira hauka.
"Muna fata wannan hali na hauka da ya mayar da yankinmu tamkar tekun jini tsawon kwanaki 420 karshe zai zo karshe."
Yayin da yake tsokaci kan muhimmancin sammacin da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi kan firaministan Isra'ila, ya ce matakin da babbar kotun MDD ta dauka na da muhimmanci wajen dakatar da zubar da jini.
“Kafin yanayin sanyi ya yi tsanani, kafin a sake zubar da jinin wasu marasa galihun, kafin iyaye su yi makoki da bakin cikin mutuwar ‘ya’yansu, kafin yara su zama marayu, kafin amana da cibiyoyi na kasa da kasa su kara lalacewa,” in ji shi a karshen sakon nasa yana fatan cewa ba a sake zubar da jini a Gaza ba.
The President also reiterated the need for an urgent and long-lasting ceasefire in Gaza.
Shugaban ya kuma sake nanata bukatar gaggauta tsagaita wuta mai dorewa a Gaza.
"A takaice dai, ya kamata a samar da tsagaita wuta mai dorewa a Gaza da wuri kafin bil'adama, tare da cibiyoyi da dabi'unsa, su kara yin asarar. Turkiyya ta kare hakan tun daga ranar farko kuma tana kan wannan turba har a yanzu."