Togo ta bayyana bayar da tallafin dala miliyan 1.5 ga Turkiyya sakamakon girgizar kasar da afku a kudancin kasar a ranar 6 ga Fabrairu.
Shafin yanar gizon Jumhuriyar Togo ya sanar da cewa “Togo ta bi sahun kokarin kasashen duniya” wajen bayar da “wannan tallafi da manufar warkarwa da sake gina yankunan da suka rushe” bayan afkuwar girgizar kasar da ta yi ajalin sama da mutum 50,000.
Ofishin Jakadancin Turkiyya a Togo ya yabawa kasar saboda wannan goyon baya da kawance da ta nuna.
Ofishin ya kuma kara da cewa a ranar 21 ga Maris Ofishin Jakadancin Togo a Ankara ya shiga ayyukan dasa bishiyoyi tare da mahukuntan Turkiyya.
AA