Turkiyya tana ta ƙoƙarin ganin an taimaki al'ummar Gaza wadanda suka shafe shekara 17 cikin uƙubar takunkumai. Hoto: AA Archiv

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya soki Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya UNSC, kan gazawarsa wajen tabbatar da kudurin da zai ba da damar shigar da kayan agaji zuwa cikin Gaza ta Falasɗinu, a yayin da ake fama da hare-haren da Isra'ila ke kai wa.

Kwamitin Tsaron, "wanda ya zama ba shi da tasiri gaba ɗaya, ya sake gazawa wajen yin aikin da ya rataya a wuyansa," kamar yadda Erdogan ya bayyana a shafinsa na X ranar Laraba, kwana ɗaya bayan da wani harin sama da Isra'ila ta kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 500.

"Mummunan harin" da aka kai asibiti ya sa "kisan kiyashin da ake yi a Gaza ... ya shiga wani matakin," a cewar Erdogan, yana mai yin Allah wadai da wadanda suka kai harin "wanda take haƙƙin ɗan'adam ne kuma daidai yake da kisan ƙare dangi a kan al'ummar Gaza."

Shugaban ƙasar Turkiyyan ya kuma yi Allah wadai da Ƙasashen Yamma da kakkausar murya, "waɗanda ba sa barin ko-ta-kwana idan aka zo batun haƙƙoƙin ɗan'adam da ƴancinsa," don ƙin ɗaukar kowane irin mataki na magance wahalhalun da Falasɗinawa suke sha, maimakon haka "sai suke ƙara rura wutar lamarin."

"Waɗanda suka ƙara rura wutar abin da kalamansu da suka yi tun ranar 7 ga watan Oktoba, tamkar su ne suka kai harin kisan kiyashin na jiya tare da wadanda suka kai harin," in ji Erdogan.

Ya kuma sake jan hankula kan "laifukan yaƙin" da Isra'ila ta yi a cikin kwana 12 da suka wuce, yana mai jero harin bama-baman da aka kai kan "mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da suke ƙoƙarin yin ƙaura zuwa wajen da aka ce 'ya fi aminci,' ƙofofin kan iyaka da masallatai da makarantu da kuma wuraren zaman fararen hula."

Erdogan ya kuma yi wa kafafen watsa labaran ƙasashen duniya tas waɗanda ya ce "suna rige-rigen nuna cewa kisan kiyashin da aka yi an yi shi da hujja ta hanyar yin munafunci a labaransu."

Ƙoƙarin da Turkiyya ke yi

A yayin da yake sukar Ƙasashen Yamma, Erdogan ya yaba wa Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai OIC, kan taro na musamman da ta kira a birnin Jiddah.

Taron "ya bayyana irin jajircewar ƙasashen Musulmai a wannan lokaci da cin zalin Isra'ila ke ƙaruwa, da yadda take tare da Falasɗinawa da kuma goyon bayan da take bai wa fafutukar Falasɗinawan," ya ce.

Turkiyya ta daɗe tana taimakon al'ummar Gaza waɗanda suka shafe shekara 18 suna cikin takunkumai.

"Zuwa yanzu, na yi tattauna ta wayar tarho da shugabannin ƙasashe 18 da na gwamnatoci a matakai daban-daban," a cewar Erdogan, yana mai cewa Turkiyya ta aika jirage uku cike da kayayyakin agajo zuwa yankin, tare da hadin kan hukumomin Masar.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa Turkiyya "za ta ci gaba da aiki don tabbatar da tsagaita wuta don a samu shigar da kayan agaji, da kuma samar da zaman lafiya na dindindin.

TRT World