Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zanta ta waya da Shugaba Hassan Sheikh Mohamoud na Somalia, inda suka tattauna kan dangantaka tsakanin Turkiyya da Somalia, da kokarin yaki da ta’addanci da kuma lamuran duniya da na yankin.
A lokacin zantawar da suka yi ranar Juma’a, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya tana tare da Somalia a yakin da take yi da ta’addanci kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da inganta.
An yi tattaunawar ne kan dangantaka tsakanin Turkiyya da Somalia, da yaki da ta’addanci da kuma batutuwan duniya da na yankin.
Shugaba Erdogan ya bayyana fatansa na ganin an kawo karshen tashin hankali tsakanin Somalia da Ethiopia a wani yanayi na mutunta iyakar kasar Somalia.
Shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi kan batutuwa daban-daban, suna masu jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin Turkiyya da Somalia wajen tunkarar kalubalen da ke gabansu tare da ba da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiyar yankin.
Turkiyya ta damu game da yarjejeniyar da Ethiopia da Somaliland suka kulla
Ranar Alhamis Turkiyya ta fitar da sanarwar goyon baya da kare martabar iyakokin Somalia bayan wata yarjejeniya da Ethiopia da Somaliland suka kulla wadda za ta bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwan Somaliland da ke Tekun Maliya.
"Yarjejeniyar Fahimtar Juna don Hadin Kai da Aiki Tare da aka sanya hannu a kai a Addis Ababa a ranar 1 ga Janairu, 2024 tsakanin Jamhuriyar Ethiopia da Somaliland, ba tare da sani da yardar gwamnatin Somalia ba, na sanya damuwa," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a wata sanarwa da ta fitar.
Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da Shugaban Kasar Somaliland Muse Bihi Abdi ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Litinin.
Ethiopia da ba ta da iyaka da teku ta sanya hannu da yankin Somaliland da ya balle daga Somalia, don amfani da Tashar Jiragen Ruwa ta Berbera.