Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada muhimmancin karfafa alaka da kasar Girka ta hanyar fahimtar juna, da hadin gwiwar tattalin arziki, da musayar al'adu.
Altun ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wata hira da jaridar Girka Ta Nea, inda ya yi magana kan muhimman batutuwan yankin da kuma takaddamar da ba a warware ba.
“Ci gaban al'ummomin da za su zo nan gaba ya dogara ne kan karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
“Haɓaka fahimtar juna, faɗaɗa damammakin ciniki, zurfafa dangantakar jama’a, da ƙoƙarin samun wadata tare zai amfanar da kowa,” in ji Altun.
Ya kara da cewa, "Ta hanyar ba da fifiko ga wadannan manufofin, za mu iya tabbatar da cewa wadanda ke son kawo cikas ga ci gaba da toshe hanyar hadin gwiwa da zaman lafiya sun koma gefe.
Dangane da inganta hadin gwiwar al'adu, Altun ya bayyana goyon bayan Ankara na mayar da sassaken duwatsu na Parthenon Marbles zuwa Girka tare da yin kira ga mutunta juna dangane da batutuwa masu muhimmanci kamar tekun Aegean da kuma Turkawa marasa rinjaye a Girka.
“Yana da kyau al'ummar Girka su fahimci cewa tekun Aegean ba tafkin Girka ba ne, kuma Turkiyya wadda ke da hanyar ruwa mai tsawo tana da hakki da wannan teku da kuma muhimman muradu a yankin," in ji shi, inda ya jaddada buƙatar warware lamura cikin zaman lafiya a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Dangane da Turkawa marasa rinjaye da ke Girka, jami'in na Turkiyya ya kuma ce: “Turkawa marasa rinjaye na neman a amince da shugabannin addinin da suka zaba a hukumance da kuma 'yancin bayyana kabilarsu ba tare da fargaba ba ko tsoron wani abu da ka iya biyowa baya, kamar dai yadda ‘yan Girka marasa rinjaye da ke a Turkiyya ke da ‘yanci.”