Hare-haren isra'ila a Zirin Gaza na Falasdinu sun jima da haura iyakar kare-kai inda suka koma zalunci na karara da cusgunawa da kisan kiyashi da dabbanci, in ji Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
"Kar wanda ya yi tsammanin za mu yi shiru a yayin da ake aikata ta'annati a kan idanuwanmu," in ji Erdogan a yayin taron Majalisar Iyali da aka gudanar a Ankara a ranar Alhamis.
"Tabbas, tarihi na ajiye bayanan wadanda suke yin shiru a yayin da ake kashe yara kanana da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma wadanda suka yi magana a lokacin da ake wahala, da ma wadanda suka yi kokari don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."
Ya kara da cewa masu kallon kisan kiyashi a Zirin Gaza su kawar da idanuwansu daga wajen ne wadanda ya kamata su tuhumi kawunansu.
Da yake sukar Tarayyar Turai kan gaza samar da tsagaita wuta a Zirin Gaza, Shugaba Erdogan ya ce "Yara nawa ne za su sake mutuwa kafin Tarayyar Turai ta yi kira da a tsagaita wuta?"
"Bama-Bamai nawa ne za su fado kan Zirin Gaza kafin Kwamitin Tsaro na MDD ya dauki mataki? Shugaba erdogan ya tambayi MDD da ta gaza wani katabus."
Goyon bayan Tarayyar Turai ga Isra'ila
Kakakin Tarayyar Turai kan harkokin kasashen waje Peter Stano, a ranar Laraba ya ce Kungiyar ba ta yi kira da a tsagaita wuta ba saboda hare-haren da ake ci gaba da kaiwa daga bangaren kungiyar Hamas ta Falasdinawa masu tirjiya, inda ya sake jaddada goyon bayan Tarayyar Turai ga Isra'ila.
Erdogan ya ci gaba da cewa "Wadanda suka dinga yanke hukunci game da hakkokin dan'adam da 'yanci a lokacin da damar hakan ta samu, a yanzu suna biris da hakkin rayuwa na wadand aake zalunta a Zirin Gaza tsawon shekaru 19."
Ya kara da cewa tun bayan fara rikicin kusan makonni uku da suka gabata, sannan aka biyo bayan hakan da yanke ruwa da wuta zuwa Zirin Gaza, Turkiyya ta aika da sama da tan 200 na kayan agaji ga Zirin Gaza ta cikin Masar.
A 'yan kwanakin nan, ta dan bar 'yan kayan agaji 'yan kadan sun shiga yankin, wanda ba zai ishi mutum miliyan 2.3 da ke rayuwa a cikinsa ba.
Rikicin Zirin Gaza ya faro ne a lokacin da kungiyar Hamas ta fara kai Farmakan Ambaliyar Al Aksa kan Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba wanda suka hada da makaman roka da suka dinga fada wa iyakokin Isra'ila ta sama, kasa da ruwa.
Hamas ta bayyana cewa wannan farmaki martani ne ga yadda Yahudawa 'yan kama guri zauna suka kutsa kai Masallacin Ƙudus da kuma yadda suke cusgunawa Falasdinawa.
Sojojin Isra'ila kuma sun kaddamar da hare-haren kan mai uwa da wabi a Zirin Gaza, inda suka nufi makarantu, asibitoci, gidajen fararen hula d ama jerin gwanon motoci da ke kwashe jama'a.
Sakamakon rikicin, an kashe mutum kusan dubu 8,000 da suka hada da aƙalla Falasdinawa 6,546 da Isra'ilalawa 1,400.