Matakin na shugaban Turkiyya na isar da sakon sabuwar niyyar gyara dangantakar da ta yi tsami a ‘yan shekarun nan game da sabanin manufofi a Siriya, hadin kanki a ayyukan soji, da takaddamar diplomasiyya. Hoto: Rueters

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump, bayan nasarar zaɓe da Trump ɗin ya yi, inda ya taya shi murna tare da bayyana fatan ƙarfafa haɗin-kai tsakanin Turkiyya da Amurka a shekaru masu zuwa.

A tattaunawar ta ranar Alhamis, kamar yadda wata sanarwa da aka fitar daga Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ta bayyana ta shafin X, Erdogan ya bayyana fatan Trump zai yi sabon wa’adin mulki mai amfani ga alaƙar Amurka da Turkiyya, yana mai jaddada muhimmancin haɗin-kai game da batutuwan yankinsu da duniya baki ɗaya.

A yayin da Gabas ta Tsakiya ke fuskantar manyan ƙalubale, daga yaƙe-yaƙe zuwa matsin tattalin arziki, Erdogan ya bayyana yiwuwar haɗin-kai tsakanin ƙasashen biyu wajen kawo zaman lafiya da magance matsalolin tsaro.

Matakin na shugaban Turkiyya na isar da saƙon sabuwar niyyar gyara dangantakar da ta yi tsami a ‘yan shekarun nan game da saɓanin manufofi a Siriya, haɗin-kanki a ayyukan soji, da diflomasiyya.

A matsayin su na kawaye a NATO, Amurka da Turkiyya na da tsohuwar alaƙar ayyukan soji da kasuwanci, amma suna fuskantar rikici kan manufofin Washington a Gabas ta Tsakiya, kamar yadda Amurka ke taimaka wa ‘yan ta’addar YPG da ke Siriya.

Ankara kuma ta soki Washington saboda kin bayar da hadin kai don kalubalantar kungiyar ta’adda ta FETO, wadda shugabanta ya mutu a Pennsylvania a watan da ya gabata.

Tattaunawar ta Erdogan da Trump ta yi nuni ga sha’awar bai-ɗaya ta shugabannin wajen sauya fasalin alaƙar Turkiyya da Amurka, inda dukkan ƙasashen biyu ke taka muhimmiyar rawa wajen magance rikici a Gabas ta Tsakiya, tare da kawar da matsalolin kan iyaka.

Masu sanya idanu na ganin wannan mataki a matsayin dama ga Turkiyya da Amurka wajen faɗaɗa buƙatun bai-ɗaya, sannan hakan na zama damar sake kusantar juna don biyan manyan buƙatun yankunansu.

TRT World