"Baikin yakan tabo matsaloli daban daban da suka shafi duniya da kuma matsalolin jin kan bil Adama dake shafar  miliyoyin mutane yayin da yake kuma karin haske kan tasirin siliman,'' a cewar Altun. Photo: AA Archive

Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Fahrettin Altun ya gabatar da wani jawabi a Bikin Fina-finai kan Jinƙai wanda gidan talabijin na TRT World Citizen ya shirya, yana mai jaddada cewa alhakin warware matsalolin jinƙai ya rataya ne a wuyan ƙasashen duniya.

“Rahotanni da alkaluman da ake da su, duk da tasirinsu, ba su wadatar wajen fitar da marasa galihu daga ƙangin wahala ba; maimakon hakan, irin yadda ake nuna irin wadannan yanayin a cikin fina-finai ya kasance yana matuƙar taɓa ranmu,” ya faɗa a ranar Lahadi.

Altun ya bayyana muhimmanci nuna sahihin tausayi da ƙarfin iya ba da labari da kuma buƙatar amfani da wani salo na jinƙai wajen warware matsalolin da duniya da yankin ke fuskanta.

Ya ce alhakin dakatar da mutanen da ke da hannu wajen cin zalin ƴan’adam da jawo wahalhalu a fadin duniya ya rataya ne a wuyan dukkannin ƙasashen duniyar.

“Abin da ya ba mu ƙwarin gwiwar warware matsalolin agaji ba wai ta rage afkuwar bala’in ba ne kawai, ya haɗa har da na iya nuna tausayi da jinƙai ga dukkan ɗan’adam ɗin da ke cikin halin wahala.”

“Bikin Fina-finai kan Jinƙai,” wanda kafar watsa labaran TRT World Citizen ta shirya, da ke aiki a kan “abin da ya shafi jinƙai” don ya zama jagora ga ƴan ƙasa a faɗin duniya, a bana ma ya sake hado kan masu kallo da ƙwararru a masana’antar fina-finai.

Wannan ne karo na biyar da ake shirya gajeren bikin, da nufin fayyace batutuwan jinƙai na duniya da kuma bai wa ɗan’adamtaka muhimmanci ta hanyar mayar da hankali kan batutuwa kamar su yaƙi da rikici da annoba da ‘yancin mata da ƙaura da sauyin yanayi da gurɓatar muhalli da yunwa da fari da rashin muhalli da kuma talauci.

‘Matsalar Isra’ila'

Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Altun ya yi kira ga a sauya tunani a kan irin kallon da aka daɗe ana yi wa rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

Ya jaddada cewa batun da aka daɗe ana kallonta a matsayin “matsalar Falasɗinu,” kamata ya yi a ce ana kallonta a matsayin “matsalar Isra’ila.

“A yau, mun taru a nan ne don faɗa wa duniya sunan gaskiya na wannan matsala, wacce a tsawon shekaru ake kallonta a matsayin ‘matsalar Falasɗinu’.

Sunan batun ‘matsalar Isra’ila,” Altun ya ce, yana mai ƙarawa da “ba a Gabas ta Tsakiya ba kawai, ba a yankinmu ba kawai, amma wannan matsalar ta duka duniya ce.”

Ya ci gaba da cewa a yayin da Turkiyya ke ɗaukar matakai cike da ƙwarin gwiwa don magance waɗannan matsaloli, wasu sun ba da goyon baya a kan matsalar jinƙai, suna jaddada buƙatar gaggawa ta haɗin kan duniya.

“Wasu ƙasashen sun gaza nuna ƙarfin halin fuskantar wannan batu, suna ɗauke idonsu daga gare shi, amma Turkiyya tana kan gaba,” ya faɗa.

"Matukar aka yi watsi da matsalar Isra'ila, wannan rikicin da ke ƙara ta'azzara a tarihi zai ci gaba da yin barazana ga bil'adama."

Altun ya yi nuni da muhimmiyar rawar bayar da labari da fasaha wajen haɓaka fahimta da tausayawa ga wahalhalun da al’ummomin da ake zalinta ke fama da su.

Ya yaba wa bikin fina-finai TRT World Citizen saboda ƙoƙarin da take yi don ba da haske kan matsalolin duniya da rikice-rikicen jinkai ta hanyar kallon fina-finai.

Ya karkare jawabinsa da bayyana fatan cewa bikin, a matsayin wani shiri, zai ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da wadata da adalci da kwanciyar hankali a duniya, tare da hada kan masu shirya fina-finai da masu ba da labari don kara tasirinsa wajen magance matsalolin jinƙai da suka addabi duniya.

TRT World