Fidan ya bayyana aniyarsa ta gudanar da wadannan tarukan akai-akai don ciyar da hadin gwiwar yankin gaba. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya sake jaddada goyon bayan Turkiyya kan tsare mutuncin ƙasa da haɗin kan Bosnia da Herzegovina.

“Matsayarmu a bayyane take ga duka ɓangarori a Bosnia da yankuna. Ina ƙara jaddada goyon bayanmu ga tsare mutuncin kasa da kuma haɗin kan siyasa a Bosnia Herzegovina,” in ji Fidan a wata wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da takwarorinsa na Bosnia da Croatia a birnin Dubrovnik na Croatia a rnar Asabar.

Yayin da yake jaddada cewa Bosnia da Croatia na da muhimmanci ga ɗorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Bosnia da yankin, Fidan ya ce sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da ci gaban siyasa a Bosnia da ayyukan hadin gwiwa a yayin ganawar tasu.

“Muna fatan (ayyukan) za su bayar da gudun mawa ga ci gaban tattalin arziƙin yankinmu,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

A yayin da yake bayyana damuwar Ankara game da kalaman raba kan jama'a da ayyukan da ake yi a Bosnia, Fidan ya ce samar da yanayi na sulhu yana da matukar muhimmanci ga ci gaba.

"A ƙarshe, mun tabo batun ayyukan samar da ababen more rayuwa a Bosnia da Croatia," in ji shi.

Yayin da ya bayyana cewa taron ya yi armashi sosai inda aka yi musayar ra'ayi da juna, Fidan ya bayyana aniyarsa ta gudanar da wadannan tarukan akai-akai don ciyar da hadin gwiwar yankin gaba.

Tsari Uku na Shawarwari

Fidan da Ministan Harkokin Wajen Albaniya Igli Hasani sun haɗu a birnin Dubrovnik na kasar Croatia, a gefen taron ministocin harkokin wajen Turkiyya-Bosnia da Herzegovina da Croatia na Tsari Uku na Shawarwari, in ji ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya a saƙon da ta wallafa a shafinta na X.

Bayan ganawarsa da Hasani, Fidan ya gana da Ministan Harkokin Wajen Bosnia da Herzegovina Elmedin Konakovic.

Bayan ganawarsa da Konakovic, Fidan ya kuma haɗu da Ministan Harkokin Wajen Croatia Gordan Grlic Radman.

Fidan ya je Croatia ne domin halartar wani taron ranar Asabar na tsarin ba da shawarwari tsakanin Turkiye da kasashen Balkan na Croatia da Bosnia da Herzegovina.

Ma'aikatar ta kara da cewa, zai kuma yi wata tattaunawa tsakaninsa da wasu ƙsashen a gefen taron, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.

TRT World