Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce wadannan zarge-zargen wani bangare ne na kokarin da Isra'ila ke yi na boye ayyukan da take aikatawa. / Hoto: AA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi Allah wadai da wani saƙo da Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz ya wallafa a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan kan shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ta bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na Isra'ila na ɓoye laifukanta.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a ranar Talata ta ce "Muna daukar wannan matsayi na rashin mutuntawa da Ministan Harkokin Wajen Isra'ila ke yi wa mai girma shugaban kasarmu a matsayin wani lamari da za a ji shi ne kawai daga bakin ƙasar da ake zarginta da kisan kiyashi."

Yayin da take suka da kakkausar murya a shafukan sada zumunta, ma'aikatar ta ce: "Irin wannan ƙazafi da ƙarya wani ɓangare ne na ƙoƙarin Isra'ila na ɓoye laifukan da ta aikata."

Turkiyya ta ƙara da cewa, za ta ci gaba da fafutukar tabbatar da zaman lafiya da adalci.

Isra'ila, wadda ta yi fatali da ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman tsagaita wuta cikin gaggawa, ta fuskanci tofin Allah-tsine a tsakanin kasashen duniya a ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Fiye da Falasdinawa 37,700 aka kashe tun daga lokacin a Gaza, yawancinsu mata da yara, kuma kusan wasu 86,400 sun jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Sama da watanni takwas da yakin Isra'ila a Gaza, inda yankuna da dama suka zama kufai a cikin yankin da aka yi wa ƙawanya da hana shigar da abinci da ruwan sha da magunguna.

Ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Duniya, wanda hukuncin na baya-bayan nan ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da kai hare-hare a kudancin birnin Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye shi a ranar 6 ga watan Mayu.

TRT World