Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" don nufin an kashe ko kama dan ta'adda ko ya miƙa wuya. / Hoto: AA Archive

Turkiyya ta “kawar da” ‘yan ta’addan PKK/YPG bakwai a arewacin Iraƙi da Syria, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta bayyana.

“Zaratan dakarunmu na Turkiyya sun kawar da ‘yan ta’addan PKK/YPG 3 waɗanda aka gano a yankin da ake gudanar da Operation Euphrates Shield da Peace Spring a arewacin Syria, sannan aka kawar da ‘yan ta’addan PKK huɗu waɗanda aka gani a yankin da ake gudanar Operation Claw-Lock,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X ranar Lahadi.

A shekarar 2022 ne Turkiyya ta ƙaddamar da Operation Claw-Lock domin kai samame a maɓoyar ‘yan ta’addan PKK a Metina da Zap da ke arewacin Iraƙi da kuma yankin Avasin-Basyan.

Nasarorin da aka samu na yaƙi da ta’addanci

‘Yan ta’addan PKK sun yi fice wurin amfani da arewacin Iraƙi kusa da iyakar Turkiyya a matsayin wata maɓoya domin kitsa hare-haren ta’addanci a Turkiyya da Syria.

Tun daga 2016, Ankara ta ƙaddamar da wasu shirye-shirye uku waɗanda suka yi nasarar daƙile ta’addanci a kan iyakar ƙasar da Syria domin guje wa taruwar ‘yan ta’adda da kuma wanzar da zaman lafiya.

Shirye-shiryen sun haɗa da Euphrates Shield (2016), Olive Branch (2018), da kuma Peace Spring (2019).

A cikin sama da shekaru 35 na ta'addancin da ta yi kan Turkiyya, ƙungiyar ta'adda ta PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda - ta ɗauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata, yara da jarirai. YPG shi ne reshen ƙungiyar na Siriya.

Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" don nufin an kashe ko kama dan ta'adda ko ya miƙa wuya.

TRT World