Babu wata kasa da za ta kasance cikin aminci har sai idan Isra'ila ta bi dokokin kasa da kasa, in ji shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, yayin da yake tsokaci kan munanan ayyukan da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza na Falasdinu sama da wata bakwai, duk da umarnin da aka sa na dakatar da ita daga hakan.
"Babu wata ƙasa da za ta zauna lafiya sai dai idan Isra'ila ta amince da bin dokokin kasa da kasa kuma ta dauki kanta a matsayin wacce take bin dokokin," in ji Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba a wani jawabi da ya yi a zauren majalisar dokokin Turkiyya.
“Isra’ila barazana ce ba kawai ga Falasdinu ko Gaza ba, har ma da zaman lafiyar duniya da kuma bil’adama baki daya,” in ji shi, yana mai mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai ranar Lahadi a sansanin ‘yan gudun hijira a Rafah da ke kudancin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 45, da kuma tayar da gobarar da ta bazu cikin sauri ta cikin tantuna da wuraren kwana.
Kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Rafah
Erdogan ya soki gazawar tsarin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da hukumomi irin su Majalisar Dinkin Duniya wajen dakatar da ayyukan ta’addanci da ake ci gaba da yi a Gaza, inda aka kashe Falasdinawa sama da 36,000 tare da haifar da ɓarna da ƙaurace wa gidajensu da kuma yanayin yunwa.
"Mene ne amfaninku, Majalisar Dinkin Duniya, idan har ba za ku iya dakatar da yadda ake kisan ƙare dangi ba kai tsaye a kafafen watsa labarai a cikin ƙarni na 21 da muke ciki," ya tambaya.
"MDD ta gaza kare ko da nata ma'aikatan da masu aikin agaji, balle a yi maganar hana kisan ƙare dangi. Ba mutuntakar ɗan'adam ce kawai ta gushe ba a Gaza, har ma da daraja da karsashin MDD dun sun gushe." in ji Erdogan.
Da yake la'antar Ƙasashen Yammacin Duniya kan zargin hannu a yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, shugaban na Turkiyya ya ce: "Babu wani imani da ke ganin ya dace a ƙona fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba har lahira a cikin tantunansu. Duniya na kallon dabbancin da mai shan jini Netanyahu ke yi kai tsaye a kafafen watsa labarai.
Ƙasashen Yammacin Duniya suna da hannu a laifukan Isra'ila
"Ku ma Amurka hannunku duk shafe yake da jini; ku ma shugabannin gwamnatocin ƙasashen Turai kuna da hannu a laifukan da Isra'ila ke aikatawa," ya faɗa.
Erdogan ya ce ɗabi'u kamar "dimokuraɗiyya da 'yancin ɗan'adam da 'yancin fadin albarkacin baki da yada labarai da 'yancin mata da yara" duk sun lalace saboda "kisan gillar da ake yi wa bil'adama" a Gaza.
Shugaban ya kuma ce dole ne a hana kisan ƙare dangi da muguntar da Isra'ila ke yi ta hanyar "haɗin kan ɗan'adam kafin ayyukan Netanyahu da masu goya masa baya su fi ƙarfin kowa."
Ya ce: "Ana ta fahimtar yadda aƙidar tsananin son kafa ƙasar Isra'ila take a faɗin duniya. "Matasa sun fara ganin cewa aƙidar tsananin son kafa ƙasar isra'ila ta kauce wa doka, kuma ina fatan wannan juyin juya halin zai 'yantar da duniya daga wannan gurɓatacciyar aƙida."
Matsin lambar da Isra'ila ke yi wa Kotun Duniya
Shugaba Erdogan ya ce "Isra'ila na ƙoƙarin matsin lamba kan Kotun Shari'a da alkalai" yana mai cewa "dole ne a hana ta ruguza cibiya ta ƙarshe da ake sa ran samun adalci daga wajenta."
Ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa (ICJ), wanda a hukuncin da ta yanke na baya-bayan nan ya ba ta umarnin dakatar da ayyukanta a Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye ta a ranar 6 ga watan Mayu.
Kan batun rawar da ƙasashen Musulmai ke takawa a rikicin Gaza kuwa, Erdogan ya ce "Ina da abin faɗa kaɗan a kan duniyar Musulunci a nan: Me kuke jira wajen cimma matsaya? Allah zai kama ku da mu gaba ɗaya a kan wannan lamarin."
"Sai yaushe ne Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai za ta aiwatar da wani tsari mai ƙarfi da zai hana Isra'ila kisan ƙare dangi," ya tambaya. Sai yaushe ne al'ummar Musulman duniya za su kare ƴanci da martabar ƴan'uwanmu Falasɗinawa?"