Yayin da aka gudanar da ayyukan yaƙi da kungiyar Daesh har 1,162 tun daga 1 ga watan Yunin 2023, ya zuwa yanzu 'yan sandan Turkiyya sun kama mutum 2,402 da ake zargi, kamar yadda Ministan kasar ya bayyana. /Hoto: AA  

'Yan sandan Turkiyya sun kama mutum 47 da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar ta'addanci ta Daesh a manyan biranen ƙasar da suka haɗa da babban birninta Ankara da kuma Istanbul, a cewar wani saƙo da Ministan Harkokin Cikin Gida ƙasar Ali Yerlikaya ya wallafa a shafinsa na X.

An gudanar da samame na haɗin gwiwa ''Operation Bozdogan" ne a ranar Laraba a Adana da Bursa, wanda Hukumar Leken Asiri ta Ƙasar da kuma Sashen Yaƙi da Ayyukan Ta'addanci suka gudanar.

Daga cikin waɗanda aka tsare da ake zarginsu da alaƙa da Daesh akwai mutum 22 da aka kama a Istanbul, sai mutum ɗaya a Kirikkale da kuma mutum 15 a Ankara, sannan biyu a Adana, da kuma bakwai a Bursa.

Da yake jaddada ƙudurin samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa, Yerlikaya ya ce, "Domin zaman lafiya da haɗin kan al'ummarmu, ba za mu yi jinkiri wajen bai wa waɗannan 'yan ta'adda dama ba."

'Yaƙinmu zai ci gaba'

Ya kuma jaddada irin namijin ƙoƙarin da jami’an tsaron ƙasar ke yi, inda ya ce, “Za mu ci gaba da yaƙinmu ba tare da jinkiri ko tsagaitawa ba, tare da ƙoƙarin da jami’an tsaron ke yi.

Ministan ya bayyana cewa, a yayin da aka gudanar da ayyukan yaƙi da ƙungiyar Daesh har 1,162 tun daga ranar 1 ga watan Yunin 2023, ya zuwa yanzu 'yan sandan Turkiyya sun kama mutum 2,402 da ake zarginsu da alaƙa da ƙungiyar.

Turkiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fara ayyana Daesh a matsayin ƙungiyar ta'addanci, kazalika ƙasar ta fuskanci hare-hare da dama daga ƙungiyar.

Sama da mutum 300 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu ɗaruruwan mutanen kuma suka jikkata a aƙalla hare-haren ƙunar baƙin wake 10, da hare-haren bama-bamai bakwai, da kuma hare-haren makamai huɗu da ƙungiyar ta gudanar.

TRT World