Turkiyya ta kama ƴan ta'addar Daesh 20 a birnin Istanbul da wasu sauran garuruwan kasar.
An yi kamen ne bayan umarnin da aka samu daga ofishin Mai Gabatar da Kara na Istanbul kan a kama mutum 14 da ke da alaƙa hedkwatar Daesh da ke Dashisha a arewa maso-gabashin Siriya, in ji majiyoyin tsaron da suka nemi a ɓoye sunayensu saboda ba a ba su damar magana da kafafan yada labarai ba.
Ministan Harkokin Cikin Gida na Turkiyya Ali Yerlikaya a ranar Larabar nan ya fitar da sanarwa ta shafin X cewa "Ƴan sandan Turkiyya sun kama mutum 20 a larduna bakwai yayin kai farmakin "Bozdogan-26" da ake ƙaddamarwa kan ƴan ta'addar Daesh."
Ya jaddada cewa "Tare da addu'o'i da goyon bayanku, ba za mu ja da baya ba a yayin da muke ci gaba da zage damtse wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da goyon baya ga kasarmu har sai an ga bayan dan ta'adda na karshe."
Farmakai bayan harin coci
Turkiyya ya tsananta kai farmakai kan 'yan ta'addar daesh bayan da kungiyar ta kai hari kan cocin 'yan Italiya a watan Janairu a lokacin bauta tare da kashe mutum guda.
Tun 1 ga watan Yunin 2023 jami'an tsaron Turkiyya ke kaddamar da farmakai kan 'yan ta'addar Daesh inda aka kama sama da su dubu biyu
Turkiyya ta kasance kasa ta farko a ta ayyana Daesh a matsayin kungiyar ta'adda a 2013, ta fuskanci hare-hare da dama daga kungiyar.
Sama da mutum 300 ne suka mutu yayin da wasu daruruwa suka jikkata sakamakon hare-haren na 'yan ta'addar Daesh da suka hada da na kunar bakin waje 10, na bam bakwai da na bindigu hudu.