Daraktan Sadarwa na Turkiyya ya yi kira ga Isra'ila da ta daina kai hare-hare kan fararen hula da 'yan jarida da ma'aikatan lafiya. / Photo: AA

Dakarun mamaya na Isra'ila sun kai hari kan tawagar TRT Arabi da 'yan jarida a ranar Lahadi a kofar gidan Isra Al Jaabis da aka tsare a Birnin Kudus.

Bayan kai harin, Daraktan Sadarwa na Turkiyya Altun ya ce, "A cikin rashin mutunta dokokin kasa da kasa, Isra'ila, tana kashe 'yan jaridan da ke jan hankalin duniya kan abin da ke faruwa a Gaza, tare da ci gaba da amfani da hanyoyin da ba su dace ba."

"Muna Allah wadai da gwamnatin Isra'ila, wacce a yanzu ta mayar da martani ga 'yan jaridar da ke yada labaran yadda ake musayar mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin, inda take kai musu hari da harsasan roba da kuma amfani da hayaki mai sa hawaye a kansu," kamar yadda ya rubuta a shafin X a ranar Lahadi.

Da yake kira ga Isra'ila da ta dakatar da kai hare-hare, musamman kan fararen hula Falasdinawa da 'yan jarida da ma'aikatan kiwon lafiya da ma'aikatan agaji, Altun ya ce, "Ya kamata Isra'ila ta bi dokokin kasa da kasa."

Ya bayyana cewa Hukumar Sadarwa ta sa ido sosai kan halin da ‘yan jaridun da Isra’ila ta kai musu hari ke ciki.

TRT World