Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi kira ga hadin kan duniya don kawo karshen wahalhalun da ake fama da su a Gaza tare da ƙarfafa batun kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da kuma sanya Birnin Ƙudus a matsayin babban birninta.
Da yake jawabi a wurin baje kolin "Wasiƙun fursunonin yaƙi na ƙungiyar agaji ta Red Crescent na gado na shekara 100 na Turkiyya" a ranar Talata, Fahrettin Altun ya tabbatar da cewa, mummunan halin da ake ciki a Gaza na zalunci da yunƙurin kisan kiyashi da Isra'ila ke aiwatarwa, lamari ne mai tayar da hankali da ya samo asali daga zalunci da cin zarafi da kuma fin ƙarfi na tsawon lokaci.
Altun ya bayyana irin jajircewar da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ke yi na kawo karshen zaluncin da ake yi a Gaza da kuma ƙarfafa kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, tare da sanya Birnin Ƙudus a matsayin babban birninta, bisa dokokin shekarar 1967.
Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin duniya, da su tashi tsaye wajen yaƙi da bala'in jinƙai da ake ciki a Gaza, tare da ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu na magance rikicin.
Da yake nanata cewa zaluncin da Isra'ila ke yi da kisan kiyashi da yunƙurin kisan ƙare dangi a Gaza, abubuwa ne da ke nuni zaluncin da aka ɗauki tsawon lokaci ana tafkawa, Altun ya ce Turkiyya na kokarin kawo karshen zaluncin da ake yi a Gaza cikin gaggawa tare da kafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta, "da kuma sanya Birnin Ƙudus a matsayin babban birninta, bisa kan dokokin 1967."
An shirya baje kolin "Wasiƙun fursunonin yaƙi na ƙungiyar agaji ta Red Crescent na gado na shekara 100 na Turkiyya" ne da hadin gwiwar Hukumar Sadarwa ta Fadar Shugaban Ƙasa da Hukumar Agaji ta Red Crescent, ta Turkiyya da kuma kafar watsa labarai ta TRT.
Jawabin na Altun ya fayyace aniyar ƙasar Turkiyya ta taka rawar gani wajen magance rikice-rikicen yankin da kuma ciyar da kuma tabbatar da adalci da zaman lafiya gaba a duniya.
"A karkashin jagorancin Shugaba Erdogan, Turkiyya ta sadaukar da kai ga jagoranci ta hanyar ba da misali, inda take bin tsarin manufofin kasashen waje da ya shafi al'umma wanda ke ba da fifiko ga kwanciyar hankali da zaman lafiya da tsaro," in ji shi.
"Wannan ƙasa, wannan yanki, da wannan wayewar da muka taso a kai su ne ainihin sakamakon gwagwarmaya da yaƙe-yaƙe da aka yi don kare haƙƙoƙi a cikin tarihi."
Ya yi kira ga al'ummar duniya da kungiyoyin ƙasa da ƙasa, da jihohi da su yi adawa da bala'in da ke faruwa a Gaza da kuma yin abin da ya dace, yana mai cewa Turkiyya za ta zama abar koyi ga manyan masu ruwa da tsaki na duniya da salonta na "na fifita buƙatun jama'a da saisaita manufofin kasashen waje bisa ma'aunin zaman lafiya da tsaro. ”
Tarihin Turkiyya na yaɗa zaman lafiya
Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan wacce ita ma ta halarci bikin bude baje kolin "Wasiƙun fursunonin yaƙi na ƙungiyar agaji ta Red Crescent na gado na shekara 100 na Turkiyya" da aka yi a babban ɗakin karatu na kasar, ta taɓo batun tunawa da gwagwarmayar kasa da Turkiyya ta yi da kuma muhimmancinta a tarihi.
A yayin jawabin nata, ta bayyana muhimmancin hadin kan Turkiyya mai ɗorewa, da ƙimarta a yankin, wanda ke fama da rikici, ta kuma nuna damuwarta game da bala'in da ke faruwa a Gaza, inda ta yi Allah wadai da matakin da sojojin Isra'ila suka dauka a matsayin babban cin zarafi da take dokokin kasa da kasa.
“Kamar kakanninmu, ba mu da wata manufa face ta dakatar da zubar da jini a Gaza da Ukraine da Birnin Ƙudus da Yemen da Baghdad da Aleppo da kuma Damascus.
"Zuciyarmu ba za ta amince da kisan gillar da ake yi wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, da kuma kashe yara ƙanana da mata da tsofaffi da ake yi da harsasai da bama-bamai a Gaza da Yemen da Somaliya da Birnin Ƙudus da kuma Arakan da sauran wurare,” in ji ta.
A karshe Uwargidan Erdogan ta jaddada aniyar Turkiyya ta kokarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da ake fama da rikici daban-daban a duniya.