Kakakin 'yan sandan jihar Anambra ne ya fitar da sanarwar./Hoto: Nigeria Police Force

Jami'an 'yan sanda a Nijeriya sun sanar da ceto wasu ma'aikatan tashar wasanni ta Supersport, mallakin kamfanin Multichoice na Afrika ta Kudu, waɗanda suka je ƙasar don wasan Nijeriya da Libya da za a yi a maraicen Juma'a.

Hukumar 'yan sandan ta faɗa ranar Juma'a cewa ta ceto ma'aikatan gidan talabijin ɗin, waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar Anambra, bayan sun baro jihar Legas, kan hanyarsu ta zuwa Akwa Ibom kallon wasan.

Ma'aikatan dai za su je ɗaukan wasan neman cancantar buga gasar ƙwallon ƙafa ta AFCON, da za a yi a tsakanin Nijeriya da Libya a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Yankin kudu maso gabashin Nijeriya yana fama da matsalar tsaro, wanda gwamnatin ƙasar ke ɗora alhaki kan 'yan-aware da ke ƙoƙarin ɓallewa daga Nijeriya, wanda yawancinsu 'yan ƙabilar Igbo ne.

Kakakin 'yan sandan na jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya ma'aikatan da aka ceto 'yan bindiga ne suka kame su ranar Laraba, lokacin da suke tafiya ta cikin jihar Anambra, wanda dandali ne na 'yan-aware ɗn.

"Wata rundunar haɗin gwiwa ta tsaro ta yi nasarar ceto ma'aikatan jarida shida waɗanda aka yi garkuwa da su yayin da suke tafiya daga Legas zuwa Uyo, kan titin Isseke-Orlu Road a garin Ihiala," cewar Ikenga.

Saidai, kakakin ya sanar da cewa a halin yanzu, ana ci gaba da aikin neman ma'aikaci na bakawai da aka sace.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce tashar Supersport ba ta fitar da sanarwa kan batun ba zuwa yanzu.

'Yan bindga da masu garkuwa da mutane a yancin kudu maso gabashin Nijeriya suna kai hari kan jami'an tsaro da jami'an gwamnati.

TRT Afrika da abokan hulda