Victor Osimhen ne ya soma ci wa Nijeriya kwallo a minti 19 da soma wasan/Hoto: Super Eagles Twitter

Tawagar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagles ta yi nasarar samun gurbin zuwa gasar cin kofin nagiyar Afirka ta 2023 wato Africa Cup of Nations (AFCON).

Tawagar ta yi nasara ne bayan ta doke tawagar kwallon kafar Sierra Leone da ci 3 -2 a wasan da suka yi a filin Samuel Kanyon Doe da ke Monrovia, kasar Liberia, ranar Lahadi.

Sai dai har yanzu tawagar tana da sauran wasa guda da za ta fafata.

Dan wasan Nijeriya da ke murza leda a Napoli, Victor Osimhen, shi ya soma zura wa Eagle kwallo a minti 19 da soma wasa. Shi ne kuma ya zura kwallo ta biyu.

Kelechi Oheanacho ne ya ci wa Super Eagle kwallo ta uku abin da ya sa ta samu gurbin zuwa gasar ta cin kofin nahiyar Afirka.

TRT Afrika