Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin wasannin Nijeriya suke bi, daga ciki har da kungiyar Super Eagles.
Daga cikin bashin da za a biya, har da kudaden da manyan kociya ke bi na albashinsu wanda ya kai watanni 15. Haka kuma akwai alawus-alawus da kuma alkawura da aka yi wa manyan ‘yan wasa maza da mata da ‘yan kasa da shekara 20.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da babbar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ke shirin soma wasa a gasar AFCON wadda za a fara a cikin watan nan na Janairu.
Tun a bara sai dai kungiyar ta Super Eagles ta yi barazanar kin buga gasar ta AFCON kan kin biyanta hakkokinta.
Masu sharhi dai sun sha danganta rashin rashin karsashi da a wasu lokuta ‘yan wasan na Nijeriya ke nunawa a wasannin nasu da rashin biyansu hakkokinsu da suka dace wanda hakan ke kara sanyaya musu gwiwa.