Kasashe 24 ne za su fafata a gasar AFCON 2023. / Hoto: AA

Gasar cin kofin kasashen Afirka na iya zama gasar wasanni mafi daraja a Afirka. Amma kuma, duk da wannan matsayi, ana samun yawaitar rashin halartar 'yan kallo a filayen wasanni da ake buga gasar.

A yayin ake fara gasar a karo na 34 a Cote d'Ivoire, da yawa na tunanin wannan abu zai ci gaba da afkuwa.

Dalilan da suka sanya hakan sun shafi batutuwan rashin kayan more rayuwa da ma matsalolin kudade, siyasa da zamantakewa.

Matsalolin kayan more rayuwa sun shafi yadda kasashen Afirka da dama ba su da gine-gine da kayayyaki isassu da za su ja hankalin 'yan yawon bude ido da masu goyon bayan kwallon kafa daga dukkan nahiyar.

Kasashen Afirka ba su da layin dogo da ya hade su, wanda za su iya saukaka tafiye-tafiye a tsakanin kasashen nahiyar. Sakamakon, 'yan Afirka ba su da wani zabi da ya wuce na hawa jiragen sama don zuwa kasashen da ake buga wasannin. A nan ne batun kudi ya shigo, saboda farashin tikitin jirgin sama na da tsada sosai.

Misali, idan dan kasar Aljeriya zai je Cote d'Ivoire don halartar gasar AFCON, tafiyar mako guda zuwa da dawowa za ta cinye kusan Dinar din Aljeriya 146,000. Mafi karancin albashi a Aljeriya Dinar 20,000 ne.

Baya ga wadannan matsaloli da aka ambata a sama, yana da muhimmanci a ambaci cewa batutuwan a;'ada da zamantakewa ma na taka rawa sosai.

Da wahala ka ga wani dan Afirka ya tafi wata kasa a nahiyar. Hakan na faruwa ne sakamakon yanayi da kayan more rayuwa da ke nahiyar, amma hakan na da alaka da batun karbar visa.

Wani rahoto da Tarayyar Afirka ta fitar a 2018 ya bayyana 'yan Afirka za su iya zuwa kaso 22 na cikin kasashen nahiyar ne kawai ba tare da visa ba. Bayan shekaru shida, adadin dai bai wani sauya ba. Saboda haka, dan Aljeriya ba zai san komai game da Cote d'Ivoire, kamar yadda dan kasar Barazil zai san Paraguay ko Ecuador da ke Latin Amurka ba.

Dadin dadawa, yadda nahiyar ke yawan fuskantar matsalolin tsaro, siyasa da tattalin arziki, ana samun mummunan fahimta da tunani a kwakwale. Hakan sai ya sanya dan Afirka da ke da isassun kudade ma ya ji ba ya sha'awar zuwa wata kasa a nahiyar don goyon bayan kungiyar kasarsa.

A yayin da wata kasa ta karbi bakuncin gasar, 'yan kasashen da ke makotaka da ita na zuwa don goyon bayan 'yan wasansu.

Babban misalin bayarwa kan wannan shi ne a 2019, an buga gasar AFCON a Masar, wasan karshe da aka buga tsakanin Aljeriya da Sanagal ya samu 'yan kallo 25,000, adadi mafi yawa da aka samu a gasar, idan aka yi duba da lokutan da ba wai da Masar ake buga wasa ba. Mafi yawan 'yan kallon 'yan kasar Aljeriya ne, wadanda mutane ne da dama sun san Masar sun saba zuwa kasancewar su duk a arewacin Afirka kuma Larabawa.

Domin tabbatar da gaskiyar wannan batu, mutum zai iya kallon halartar 'yan Aljeriya idan aka ce an kai gasar Kamaru bayan shekara uku. Ba kowanne mai goyon bayan Aljeriya ba ne ya je kallon gasar ba.

Tabbas haka yake, dalilin haka ne ya sanya 'yan kasar Aljeriya da dama zuwa Masar a 2019 shi ne nasarar da kasarsu ta yi zuwa wasan karshe. Sai dai kuma, ba lallai a ga irin haka ba idan da a ce a Kamaru ne aka buga gasar da Aljeriya ta isa ga wasan karshe.

A yayin da irin wadannan dalilai suka hana 'yan Afirka tafiya zuwa wasu kasashe don goyon bayan 'yan wasan kasarsu, hakan ke sanya jama'ar wannan kasa da ake buga wasan ne ke zuwa kallo.

Haka kuma, wani misali na baya-bayan nan shi ne na 2019 AFCON a Masar, inda kungiyar kasa ta Masar ta samu magoya baya sosai har sama da 70,000 a wasanninsu, amma sauran wasanni suna samun 'yan kallo da ba su wuce 10,000 ba, kuma adadi matsakaici da AfricaNews suka bayyana shi ne na 5,000.

Sai dai kuma, batun farashin tikitin shiga kallon wasa ma na taka rawa kan su waye za su iya zuwa kallon wasan, a yayin da jama'ar kasar da ake buga wasannin da dama ba su da kudin sayen tikiti.

Jaridar Guardian ta Nijeriya ta bayyana a 2019 an sayar da tikitin gasar AFCON a Masar kan kudin da ya kama daga Naira 4,00 zuwa 53,000, da kuma daga Naira 2,150 zuwa 10,740 ga wasu wasannin, a kasar da mafi karancin albashi ya kama Naira 62,292.

A takaice dai, matsalolin kayan more rayuwa, siyasa, gudanarwa, kudade da al'adu da zamantakewa na kawo kalubale wajen jan hankulan masu goyon bayan kwallon kafa a yayin gasar AFCON.

Wannan na janyo 'yan kasar da ake buga wasa a cikinta ne suka fi kowa yawa. Amma kuma farashin tikitin ma ba ya bayar da dama ga dukkan 'yan kasashen da ke karbar bakuncin su halarci kallon wasannin.

Wannan yanayi na iya ci gaba a yayin da ake buga gasar AFCON a karo na 34.

Idan ana son magance wannan matsala, to dole ne nahiyar ta yi babban sauyi a fannin samar da kayan more rayuwa da ingancinta, wanda ba abu ne da za a iya samarwa a nan kusa ba. Kuma rage farashin tikiti ma zai kara yawan masu zuwa kallon gasar ta AFCON.

Marubucin wannan makala Yahya Habil, dan jarida ne dan kasar Libiya da ke mayar da hankali kan al'amuran Afirka a yanzu yana aiki da wata kungiyar bincike a Gabas ta Tsakiya.

TRT Afrika