“Bai kamata ka je goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa ba, amma ka koma gida a akwatin gawa”. Photo: Rueters

Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da wasu 10 suka samu raunuka a lokacin da magoya baya suka yi yunkurin shiga filin wasa don nuna adawa ga Senagal, in ji wani jami’in shari’a da majiyar asibiti a ranar Litinin.

An samu turmutsutsun ne a ranar Asabar a Kwatano, babban birnin kasuwanci na Benin, a lokacin wasan neman cancantar halartar gasar cin kofin kasashen Afirka.

“An samu wani ibtila’i da ya janyo rasa rayukan mutum biyu”, in ji mai gabatar da kara na gundumar Benin Jules Ahoga.

Mutum guda ya mutu nan take, dayan kuma ya mutu a asibiti, in ji sanarwar da ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Nasarar zuwa gasar

Kungiyar kwallon kafar Benin ta fafata a gida da ta Senagal inda suka samu nasarar zuwa gasar cin kofin Afirka bayan an tashi wasan kunnen doki 1-1.

Wata majiya daga tarayyar kwallon kafa ta Benin ta tabbatar da mutuwar mutanen biyu.

Majiyar ta ce an bayar da umarnin a bude kofofin shiga filin wasan kyauta ga jama’a don samun saukin shiga.

Mai goyon bayan Benin Louis Nouwatin mai shekara 32 da lamarin ya rutsa da shi, ya dora alhakin turmutsutsu da take mutanen kan magoya bayan “Da suka yi turereniya don samun wajen zama”.

An tattake mutane

Ya ce “An tattake tare da tumurmutsa mu, abun ya gagari ‘yan sanda ma”.

“Bai kamata ka je goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta kasa ba, amma ka koma gida a akwatin gawa”.

An kai shida daga wadanda suka jikkata zuwa asibiti, sauran hudu kuma na wata karamar cibiyar kula da lafiya, majiyar ta shaida wa AFP.

A watan Maris din 2019 al’amarin makamancin wannan ya afku yayin wasa da Togo, inda mutum 1 ya mutu, wasu 13 suka jikkata.

TRT Afrika