Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta doke takwararta ta Benin da ci 3-0 a wasan farko na neman shiga gasar kofin Afirka (AFCON) da za a yi a Morocco a 2025.
Ɗan wasan Nijeriya Ademola Lookman ne ya soma zura ƙwallo a fafatawar da suka yi a filin wasa na Goodswill Akpabio a Uyo da ke jihar Akwa Ibom ta kudu maso kudancin Nijeriya.
Ɗan wasan Nijeriya Ademola Lookman da ke jerin 'yan wasan da za su iya lashe kyautar Ballon D'or ne ya soma zura ƙwallo a fafatawar da suka yi a filin wasa na Goodswill Akpabio a Uyo da ke jihar Akwa Ibom ta kudu maso kudancin Nijeriya.
Bayan komawa daga hutun rabin lokaci ne Victor Osimhen ya ci ƙwallo ta biyu.
Lookman ya zura ƙwallo ta uku saura minti bakwai a tashi wasan.
Hakan ya sa 'yan kallo sun ɓarke da murna ganin cewa Nijeriya ta rama kashin da Benin ta ba ta a watan Yuni da ci 2-1
Nijeriya na cikin rukunin D a wasan fitar da gwanin inda sauran ƙasashen da ke cikin rukunin suka haɗa da Rwanda da Benin da Libya.
Yanzu dai Nijeriya za ta fafata da Rwanda a ranar Talata.