Wannan wasan na zuwa ne bayan Nijerya ta sha kashi a hannun Benin ɗin a watan Yuni da ci 2-1. / Hoto: Getty Images

A ranar Asabar 7 ga Satumba ne Nijeriya za ta kece raini tsakaninta da Benin a wasan fitar da gwani na Gasar AFCON ta 2025.

Za a buga wasan ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo a Jihar Akwa Ibom.

Wannan wasan na zuwa ne bayan Nijerya ta sha kashi a hannun Benin ɗin a watan Yuni da ci 2-1.

Ƙasashe 48 daga faɗin nahiyar ta Afirka ne za su shiga wasan fitar da gwanin inda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF ta raba ƙasashen rukuni 12.

Nijeriya na cikin rukunin D a wasan fitar da gwanin inda sauran ƙasashen da ke cikin rukunin suka haɗa da Rwanda da Benin da Libya.

Bayan Nijeriyar ta kara da Benin ɗin a ranar Asabar, za ta kuma fafata da Rwanda a ranar Talata. Wannan wasan zai kasance wasa mai zafi tsakanin ƙasashen biyu.

Kocin Nijeriya na wucin gadi Augustine Eguavoen na da damar nuna bajintarsa ganin cewa Nijeriyar ta shafe sama da wata shida ba ta yi nasara a wasan ƙwallon ƙafa ba.

Haka kuma Nijeriyar na da damar samun nasara ganin cewa a gidanta za a kara. Sai dai kocin Benin na yanzu Gernot Rohr ya san ‘yan wasan Nijeriya ciki da waje, wanda hakan ƙalubale ne ga ‘yan wasan na Super Eagles.

TRT Afrika