'Yan Nijeriya sun yi ta Allah-wadai da yadda tawagar Super Eagles ta kasar ta sha kaye daga hannun 'yan wasan kasar Guinea-Bissau

Tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles tana neman daukar fansa a kan takwararta ta Guinea-Bissau bayan da aka Nijeriyar daya a wasan da suka fafata a Abuja ranar Juma’a, na neman shiga gasar cin kofin Afirka (AFCON).

Duk da cewar ‘yan Nijeriya ne suka fi rike kwallon a wasan da aka yi a Abuja, ‘yan Guinea-Bissau sun samu damar zura kwallo a ragar Nijeriya ta kafar Mama Samba Balde, minti 29 da fara wasa.

Sakamakon ya sa Guinea-Bissau ta koma saman teburin rukunin A, yayin da Nijeriya ke biye da ita da maki 6.

Da yake magana da manema labarai bayan an gama wasan, kocin Nijeriya, Peseiro ya dora alhakin rashin nasarar Nijeriya kan alkalin wasa, yana mai cewa idan dai ban da rashin sa’a, ‘yan wasan Nijeriya sun yi wasa da kyau.

Har ila yau, wasu jaridun Nijeriyar sun ambato kocin tawagar kasar yana cewa shi yana da kwarin gwiwar cewar Nijeriya za ta dauki fansar abin da aka yi mata a Abujan.

Tuni dai ‘yan wasan Nijeriya suka bi ‘yan Guinea-Bissau din gida don su sake karawa a Bissau, babban birnin kasar, a wasan da za a yi ranar Litinin da karfe biyar na yamma agogon Nijeriya.