Turkiyya da Nijeriya sun sake bude wani sabon shafi na karfafa dangankata da diflomasiyyar da ke tsakaninsu.
A Abuja babban birnin Nijeriya, an gudanar da wani muhimmin taro tsakanin Ma’aikatar Cigaban Matasa da Wasanni ta Tarayya, Tarayyar Matuka kwale-Kwale ta Nijeriya da Kwararrun Likitocin Turkiyya karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Yanmis, kwararren likitan kashi, kula da raunukan wasanni da cututtukan gabobi.
Hadin kan mai matukar muhimmanci na zuwa a yayin bayar da tabbaci ga kasar game da karbar bakuncin Wasannin Kwale-Kwale a Abuja a 2024.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Cigaban Matasa da Wasanni ta Tarayya Isma’ila Abubakar da ya samu wakilcin Amaka Ashiofu ya yaba wa yunkurin kwararrun likiocin Turkiyya na habaka kula da lafiya ga ‘yan kasashen waje a Nijeriya.
Ya ce wannan mataki zai bayar da goyon baya ga ayyukan kula da lafiya ga gasar da za a gudanar a watan Nuwamba, kuma hakan ya dace da kokarin gwamnatin Tararayyar Nijeriya na samun masu zuba jari wajen cigaban harkokin wasanni.
A nasa jawabin, shugaban Tarayyar Masu Wasa da Kwale-Kwale ta Nijeriya Admiral Festus ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa ya zama wani sabon shafi ga harkokin wasanni da huldar kula da lafiya.
Festus wanda tsohon Ministan Sufuri ne a Nijeriya ya kuma ce zuba jari na kai tsaye da Tukiyya ta yi a Nijeriya zai sauya fasalin harkokin wasanni a kasar.
Ya yaba da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a bangarorin tattalin arziki da kasuwanci da ilimi da ayyyukan soji da wasanni da zamantakewa.
Tarayyar Wasannin Kwale-Kwale ta Kasa da Kasa ce ta bai wa Nijeriya damar karbar bakuncin gasar Wasannin Kwale-Kwale a yayin Gasar Tuka Jiragen Ruwa ta Admiral Porbeni da aka yi a Abuja.
Gasar ta samu halartar Shugaban Masu Wasan Kwale-Kwale na Duniya Thomas Konietsko da shugabannin Kungiyar Wasannin Olympic ta Afirka da ka gudanar a Jabi da ke Abuja.