Ghana ta dawo wasan bayan zura kwallo da ta yi a cikin rabin lokaci. Hoton CAF

Ghana ta yi nasarar samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin nahiyar Afirka AFCON na 2023 bayan da ta doke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ci 2-1 a ranar Alhamis.

‘Yan wasan Black Stars na ji suna gani aka fitar da su a gasar bayan zura kwallon rabin lokaci da dan’ wasan kungiyar 'Big Cats' Louis Mafouta da yi.

Ko da yake dan wasan West Ham Mohammed Kudus ya tsallake rijiya da baya, bayan nasarar zura kwallo da ya yi a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a daf da tafiya hutun rabin lokaci.

Murnar magoya bayan kungiyar a gida ya karu bayan maye gurbinsa da aka yi da Ernest Nuamah wanda ya buga kwallon karshe a wasan da ya kai ga ci 2-1.

Ghana ta hade da Angola, wacce ta tashi canjaras a karawarta da Madagascar a gasar rukunin E na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON.

Angola wacce ba ta yi nasara ba har sau uku a wasannin gasar AFCON, na bukatar maki daya ne kacal don samun tikitin shiga gasar, a wannan karon ta yi rawar gani wajen samun makin da ya bata gurbin da take nema.

Ita ma Tanzania ta samu tikitin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka bayan nasarar da ta samu ta doke Aljeriya a wasansu da aka tashi da canjaras a ranar Alhamis.

‘Yan wasan kungiyar Taifa sun yi kokari wajen zura kwallo a ragar kungiyar Desert Warriors wanda ya kai su ga samun maki daya da ake bukata don kai wa matakin shiga gasar.

Tun da aka fara gasar sau uku kadai Tanzaniya ta taba buga wasa. Hoto CAF

A yanzu dai, Uganda ta samu gagarumar nasara wajen doke Nijar da ci biyu mai ban haushi a wasannin share fage da suka buga, sai dai duk da hakan ba ta kai ga samun tikitin shiga gasar ba.

Tuni dai Tanzaniya ta samu makin da ya kaita ga zuwa ta biyu a rukunin F, inda Uganda ke a matsayi na uku sannan nasarar da ta samu a kan Nijar bai yi wani tasiri ba.

Tunisiya a nata bangaren ta rufe kamfen dinta na neman tikitin shiga Gasar AFCON bayan doke Botswana da ta yi da ci 3 mai ban haushi a ranar Alhamis.

Tun da farko dai Kungiyar Carthage Eagles ce ke kan gaba a gasar, wanda a yanzu take neman kammala zagayen rukunin J.

Matsayin da Tunsiya ke ganin zai iya kai ta ga samun nasara wajen zama ta daya a rukunin J.

TRT Afrika