Kasar Kamaru ta kira golan Manchester United Andre Onana domin buga wasan neman gurbi a Gasar Cin Kofin Afirka da kasar Burundi wanda za a buga a ranar Laraba.
An dakatar da golan ne a lokacin da ake wasan farko na Gasar Cin Kofin Duniya tsakanin Indomitable Lions din da Switzerland sakamakon rashin jituwa da golan ya samu da kocin na Kamaru Rigobert Song.
Sai dai ganin cewa Kamaru na son ta yi nasara a wasan neman gurbin shiga Gasar AFCON wadda ake yi a Ivory Coast, Song ya bukaci Onana ya dawo da buga wasan.
Masu rike da kofin na AFCON wato Senegal na daga cikin kasashe 15 wadanda suka samu gurbin shiga gasar, inda ya rage saura gurbi tara a cike wanda ake sa ran cike shi a cikin kwanaki bakwai da za a dauka ana wasanni.
Bari mu duba rukuni shida wadanda ke da guraben da ba a cike ba.
Rukunin A
Ganin cewa sun kwaci maki daya tal daga wasanni biyu da ta buga da Gambia, hakan ya sa Kamaru wadda ta lashe gasar AFCON sau biyar ta shiga cikin tsaka-mai-wuya a rukunin da ya rage saura kungiyoyi uku bayan da aka cire Kenya.
“Muna cikin wani hali,” kamar yadda Song ya tabbatar, wanda tsohon dan wasan Liverpool da West Ham ne kuma ya ci gasar AFCON a lokacin yana dan wasan har sau biyu.
Ganin cewa babu wani filin wasa na kasa da kasa a Burundi, hakan ya sa Swallows din suka karbi bakuncin Kamaru a Tanzania inda a haduwarsu ta karshe suka yi rashin nasara da ci 1-0 inda Karl Toko Ekambi ya ci kwallon.
Rukunin E
Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka ta samu dama ta biyu domin samun gurbin shiga gasar a karo na biyu amma sai kasar ta tabbata da doke Ghana wadda ta lashe gasar sau hudu.
Da a ce ta samu nasara kan Angola a Yunin da ya gabata da ‘yan wasan na Wild Beast sun kafa tarihi.
Sai dai an fitar da golan na Wild Beast Dominique Youfeigane wanda daga baya aka ci su 2-1.
Wata babbar matsala ga ‘yan wasan na Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka ita ce rashin keftin dinsu wanda dan wasan tsakiya ne Geoffrey Kondogbia wanda aka raunata a lokacin da yake buga wasa a sabon kulob dinsa na Marseille.
Rukunin F
Tanzania na da maki uku gaba da Uganda wanda hakan dama ce a gare ta domin tafiya tare da Aljeriya wadda tuni ta samu gurbi a gasar.
Sakamakon Aljeriya za ta kasance a gida, za ta iya doke Tanzania inda Uganda za ta samu makin da yake daidai da na Tanzania idan ta doke Nijar, wadda take wasanta na gida a Maroko.
Rukunin G
Mali na daga cikin kasashen da suka samu gurbi inda a halin yanzu ta bar Congo Brazaville da Gambia su fafata domin samun gurbi.
Gambia ta karbi bakuncin Congo a Maroko sakamakon suna daga cikin kasashen Afirka da dama da ba su iya wasa a gida saboda rashin filin wasa mai girma da ya cika sharuda.
Gambia ta yi kokari matuka a gasar AFCON ta 2021 inda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe, inda ta samu maki uku kan Congo, wanda hakan ke nufin kunnen doki kadai ya isa ya sa ta samu gurbi.
Rukunin I
Wannan ne rukunin da aka fi fafatawa inda maki uku kadai ya raba Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Mauritaniya da Gabon da Sudan inda baki dayansu suke neman gurbi biyu.
Ana ganin Kongo da Mauritaniya su ne za su kai ga gaci sakamakon duka a gida suke fiye da Sudan da Gabon.
Kungiyar kwallon kafa ta Kongo ta farfado sosai a karkashi njagorancin kocin nan na kasar Faransa Sebastien Desabre bayan sun yi rashin nasara a wasannin neman gurbi har biyu – inda Gabon ta ci ta a gida da kuma waje a Sudan.
Rukunin L
Fafatawa tsakanin Mozambique da Benin a Maputo ita za ta zama raba gardama kan wa zai tafi Ivory Coast tare da Senegal wadda ta samu nasara a rukunin.
Mozambique na da maki biyu a gaban Benin, wanda hakan ke nufin ko kunnen doki aka yi Mozambique ta samu nasara, inda Benin dole ne ta ci wasa kafin ta yi nasara domin shiga gasar a karo na biyar.
Benin din wadda ke karkashin jagorancin Gernot Rohr, ba ta samu nasara a wasa ko guda ba.
Suna cikin rashin jituwa tun bayan da kunnen doki ya zama nasarar 3-0 sakamakon Rwanda na da dan wasa wanda bai cancanta ba.