Nijeriya za ta kara da Moroko a gasar cin Kofin Afirka ta ‘yan kasa da shekara 17 ranar Laraba.
Karawar da za su yi a filin wasan Stade Mohammed Hamlaoui da ke garin Constantine a kasar Aljeriya, za ta iya bai wa Nijeriya damar kai wa matakin kusa da na karshe idan tawagar ta yi nasara.
“Ina sa ran wasan ya kasance mai cike da dabaru da kuma wahala domin kasar Moroko ce take kan gaba a rukunin bayan ta yi nasara da ci biyu a wasanta na farko,” in ji Kocin Nijeriya, Unduka Ugbade.
Nduka Ugbade, wanda ya buga wa Nijeriya gasar cin Kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekaru 16 a China a1985 da kuma gasar cin Kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 da aka yi a Saudiyya a 1989, ya ce yaransa za su yi kokarin doke Moroko.
Nijeriya ta doke Zambiya a wasanta na farko da ci daya da nema yayin da Moroko ta doke Afirka ta Kudu da ci biyu da nema a wasannin farko da suka yi a rukuninsu na B.
Sau biyu tawagar Golden Eaglets ta taba lashe gasar cin Kofin Afirka, AFCON, ta ‘yan kasa da shekaru 17, a 2001 da 2007.
Ra’ayin ‘yan Nijeriya game da shekarun ‘yan wasa
An dade ana korafi game da yadda ‘yan wasan da ake gabatarwa a irin wannan gasa ta yara suke da kamannin manya.
Amma a wannan karon wasu ‘yan Nijeriya suna yabawa da kamanta gaskiya wajen gabatar da kananan yara a tawagar Golden Eaglets ta wannan gasar.
“Na yi matukar murna. Wadannan tabbas ‘yan kasa da shekara 17 ne,” a cewar Ahmed Ayinde a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Yara kanana ne sosai,” in ji Pamela Taye Ilekhuoba a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Shi kuwa T Barz cewa ya yi “E, yara ne. Ina fatan za mu samu ‘yan wasan tsakiya masu kyau daga cikinsu.”
Da misalin karfe biyar agogon Nijeriya ne za a yi karawar tsakanin Nijeriya da Moroko.