Daga Charles Mgbolu
Ana iya cewa kalmar da ta dace da a kira gasar AFCON ta 2023 a bana wadda ke gudana a kasar Ivory Coast ita ce "ba a san maci tuwo ba".
Daga yadda mai masaukin baki ta ba da mamaki wajen farfadowa, da kuma yadda manyan kasashe suke shan kaye a hannun kanana, 'yan wasa da masoya kwallo sun fuskanci mababmbantan yanayi a kallon wasannin da aka buga.
An kammala matakin 'yan-16 ranar Talatar nan inda aka yi waje da kasar da ta fi kowace matsayi a ma'aunin kwarewa kwallo wajen FIFA, wadda ta je wasan dab da na karshe a kofin duniya na 2022, wato Maroko.
"Ba karshen duniya muka zo ba," in ji kocin Maroko Walid Regragui, wanda a kasar ne za a buga wasan AFCON mai zuwa.
"Ba mu kadai abin ya shafa ba. Da yawan manyan kasashe an cire su," a cewar Regragui.
Manyan kungiyoyi
Kalaman kocin Maroko gaskiya ce tsagoranta, saboda wannan gasar ta nuna yadda manyan kasashe suka gaza kusan gabadayansu.
Duka kasashe biyar da suka wakilci Afirka a gasar kwallon kafa ta duniya ta 2022, an fitar da su daga gasar AFCON ta bana. Tun a matakin rukuni aka fitar da Masar, Kamaru, da Ghana wadanda suke da kofuna 16 tsakaninsu.
Stephen Mbonu wani mai sharhin kwallo daga Nijeriya ya fada wa TRT Afrika cewa, 'Ina ganin kungiyoyinnan sun zo gasar ne ba tare da karfin gogewa a 'yan wasansu ba'.
'Ya kara da cewa, 'Kamar ba su shirya sosai ba a zahiri. Misali Maroko ta yi wasa mai kyau a rabin farko na wasa, amma sai suka sare. A yankin wasan na biyu sun nuna alamun kame-kame. Karfinsu ya gaza''.
Fitar da Senegal da Ivory Coast ta yi bayan bugun fenareti yana ci gaba da zama batun tattaunawa, inda aka bayyana cewa babu kasar da ta ci kofi kuma ta wuce matakin siri-daya-kwale, tun bayan Masar a 2010.
Mbonu ya ce, ''Game da Senegal, na kasa cewa komai. Watakila sakaci ne ya hana su cinye wasan a fili. Game da fenaretin kuma, da ma abu ne na sa'a''.
Fitar da zakaru
Tabbas, kasashe uku da suka ci kofin a baya-bayan nann duka an cire su, inda aka fitar da Aljeriya a matakin rukuni, a karo na biyu a AFCON, tun bayan lashe kofin da suka yi a 2019.
Mohamed Salah, da Riyad Mahrez, da Sadio Mane da Achraf Hakimi, huda daga cikin mafi girman 'yan wasan Afirka a yau, duka za su kalli sauran wasannin gasar ne a talabijin, idan ma za su iya hakan.
Wani abin lura shi ne babu daya daga cikin kasashen da suka kai matakin kwata-fainala a gasar bara shekara biyu da suka wuce a Kamaru, suka iya cimma wannan mataki a bana.
Wannan zai iya nuna cewa matakin fadada yawan kasashen gasar zuwa 24 – wanda aka fara yi daga 2019 a Masar – ya taimaka wajen ba wa kananan kasashe karfin gogayya.
Tsananin zafi
Wasu masoya a soshiyal midiya sun ce yanayin tsananin zafi a Ivory Coast ya yi lahani ga wasannin, inda aka yawaita zuwa hutun shan ruwa.
Mbonu bai amince da hakan ba: ''Yawancin kasashen Arewacin Afirka inda wannan zargi yake samo asali, suna da yanayin matukar zafi, kuma sun saba da zafin. Wannan bai kamata ya zama uzurin rashin tabukawa ba.''
Zancen cewa "babu sauran kanana kungiyoyi" da aka ji daga bakin kyaftin din Senegal, Sadio Mane ya yi yawo a duniya, kuma akwai gaskiya a zancen nasa.
''Cewa wata tawaga ta yi kokari a gasar baya, ba garanti ne na cewa za ta maimaita kokarin a gasar bana ba. ga misali Nijeriya ta ci kofin a 2013 amma ta kasa samun gurbin shiga gasar a 2015," in ji Mbonu.
Nijeriya, wadda ta fi kowa yawan mutane a Afrika ta nuna bajinta saboda cikin 'yan wasanta akwai gwarzon dan kwallon Afrika na shekarar bara, Victor Osimhen wanda ke jan ragamar tawagar.
Alamu sun nuna za su iya cin kofinsu na hudu a tarihi, shekaru 11 bayan wanda suka ci. Duk da dai akwai barazana a gabansu, idan an yi la'akari da yadda gasar take tafiya.
Korar koci
Ivory Coast kasa daya da ta da ke rukumin manya a kwallo, ta taba cin kofin sau biyu, na karshensu a 2015. Sannan suna da fifiko da ke zuwa da buga wasa a gida.
haka kuma babu kasa mai masaukin baki da ta ci gasar tun bayan Masar a 2006, sannan tawagar Ivory Coast sun yi ta fama kafin yanzu, inda suka sha kayen da ba su taba samu ba a a gida, wanda ya janyo suka kori kocinsu.
Angola, wadda take maki na 28 a Afirka, za su kara da tawagar Nijeriya ta Super Eagles, yayin da Guinea za ta fuskanci Jumhuriyyar Dimukradiyyar Congo.
Babban abin mamaki
Kasar da ta fi ba da mamaki ita ce Cape Verde, wadda 'yar karamar kasa ce da ke kan tsibiri a tekun Atlantic, wadda take da yawan al'umma 600,000.
Sun ci Ghana sannan suka yi canjaras da Masar a hanyarsu ta zuwa saman teburin rukuninsu, kafin su zo su fitar da Mauritania.
"Ka gani ba abu ne mai sauki ba ga manyan kasashen nan su iya cin wasanninsu," in ji kyaftin din Cape Verde, Ryan Mendes da yake magana da Canal Plus Afrique.
Ya kara da cewa "Suna da 'yan wasa da ke buga wa manyan kulob na duniya, amma mu da ake wa kallon kanana muna buga wasa da karfin zuciya".