Ranar Talata kasashen biyu za su sake karawa a wani wasan na sada zumunci/ Photo: Twitter/@ghanafaofficial

Tawagar ‘yan wasan kasar Ghana, Black Queens, ta lallasa takwararta ta Senegal, the Lioness, da ci uku da nema a wasan sada zumunta.

Gift Assifuah ce ta fara zura kwallo a ragar Senegal minti biyu da fara wasa bayan mai tsaron gidan Senegal ta yi kuskure wajen taba kallon inda Assifuah ta samu damar cilla kwallon cikin raga.

Senegal ta yi kokarin ramawa, amma Adama Alhassan da Janet Egyir, sun yi wa gidan Ghana katanga abin da ya hana yunkurin Senegal na zura kwallo a raga.

Grace Asantewaa da ke taka leda a Real Betis ce ta kara kwallo ta biyu yayin da ta yi kan ‘yan wasan Senegal hudu kuma ta buga kwallo saman mai tsaron gidan Lioness din, kuma kwallon ya kwana cikin ragar Senegal.

Ana dab da zuwa hutun rabin lokaci ne Gift Assifuah ta sake samun damar kara wa Senegal nauyin kwallaye lamarin da ya mayar da wasan 3-0.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwato cewar wasan sada zumuntar da aka yi a Accra ya kasance karo na biyu da tawagar kwallon kafar Ghana ke samun nasara a kokarinta na shirya wa gasar kwallon kafa ta duniya ta mata.