Zanga-zangar masu fafutikar ganin an kawo karshen yaki a Gaza a Nuwamban 2023. Hoto: AFP

Daga

Rania Awaad

A wata daya da rabi da ya gataba, mun ga karfin gwiwa da juriya, sannan a gefe guda kuma mun ga rashin mutunta alfarmar ‘yan'adam bisa yadda ake yi wa mutanen Falasdinu kisan kiyashi.

Da yawanmu da muke bibiyar lamarin, mun fada cikin tunane-tunane da damuwa a a kusan kullum, wanda ke jawo cikas ga harkokinmu na yau da kullum.

Duk da kokarinmu na zanga-zanga, da kauracewa kayayyakin Isra’ila da kuma yin kira da a dakatar da yakin, lamarin da alama ya fi karfinmu duba da yadda ake cigaba da kisan kiyashin.

Muna fargabar cewa duk abin da za mu yi, ba zai iya kawo wani canjin ba. Watakila akwai bukatar mu sauya salo, ta yadda za mu kara amon koke-koken Falasdinawa.

Ba mamaki za mu gaji, wanda daga kuma amma za mu ji cewa ba mu kyauta ba ne. Za mu raina gajiyar tamu idan muka kwatanta da ainihin abin da ke faruwa na yadda ’yan uwanmu Falasdinawa ke ciki na rashin tabbas din ganin gobe.

A taron tattaunawarmu na Maristan na kwanan nan a game da Falasdinawa, daya daga cikin baki masu jawabi Dokta Jess Ghannam ya yi wani jawabi mai muhimmanci a game da ainihin ma’anar matsalolin da ke shafar lafiyar kwakwalwar da ‘yan'uwanmu Falasdinawa da sauran al’ummarmu baki daya ke fuskanta saboda rashin adalci.

Wannan damuwar ba sabuwar aba ce duba da yadda muke rayuwa a wani yanayi da tsari da bai mutunta alfarmar dan'adam, ba adalci ba tausayi ga wadanda ake zalunta. Wannan bambanci kadai yana iya jawo bakin ciki babba da shiga damuwa-Ciwon da al’ummar da aka zalunta suke shiga saboda rashin adalcin da suke fuskanta.

Haka kuma akwai takaici ganin yadda wasu masu hankoron kare hakkin ‘yan Adam suka yi gum, da kuma yadda za mu iya cigaba da rayuwa da tunanin lamarin ba tare da jawo wa kanmu ko matsayinmu ko aikinmu cikas ba.

Wata matsalar da take addabarmu kuma ita ce yadda ake shiga tsaka mai wuya na gani kiri-kiri irin wadanann rashin adalcin ga al’umarmu, sannan a gefe guda kuma mutum ya kama bakinsa ya yi shiru kamar babu abin da ke faruwa.

Muna more rayuwarmu a matsayinmu na iyalai, ma’aikata ko dalibai a daidai lokacin da muke cigaba da jimamin rashin wadannan damarmakin ga Falasdinawa, ciki har da rashin ‘yancin zirga-zirga da tsaro da ilimi, damarmakin karo ilimi da neman aiki da sauransu.

Gaza. Hoto: AA

Haka kuma akwai bambanci tsakanin abin da muke gani ko muka sani da kuma abin da gama- garin mutane suka sani.

Yadda ake kara nuna tsana ga Musulunci, da yadda kafafen sadarwa ke nuna bambanci wajen watsa labaransu, da tace abin da za a nuna da kuma yanayin yadda siyasa ke taimakon ta’addancin da ake yi a Falasdinu duk suna cikin abubuwan da za su iya jawo mana damuwa a lafiyar kwakwalenmu.

Fushi da damuwa, idan har ba su isa inda ya kamata ba, kara yawaita suke yi, sannan su kara fadada damuwar da da yawanmu suke ciki.

Tunaninmu tamkar yare ne da muke gane bukatunmu. Misali, bakin ciki yana zuwa ne a sanadiyar rasa wani abu; kamar rasa natsuwar samun tsaro, ko rasa wadanda a baya muke zaton abokan arziki ne, ko rasa aminci a shugabanci.

Rasa wadannan abubuwan na nuna bukatar da ke akwai na nuna kauna ga masoyanmu da al’ummarmu da ma komawa ga Allah.

Wata damuwar da da yawanmu muka shiga a makonnin da suka gabata ita ce ta fushi.

Fushin na ganin yadda ake bari ko taimakawa wajen kisan kiyashin kananan yara da ba su ji ba, ba su gani ba ne, da kuma cigaba da bata sunan masu bayyana ta’addancin da ake yi. Fushi wani makami ne da ke sanya mutum daukar mataki, kuma cikin gaggawa.

Mutane sun yi tattakin a bar Falasdinawa su sha iska a Duban

Idan aka yi amfani da shi da kyau, duk wani yanayin da muke ciki yanzu zai iya mana amfani wajen neman adalci ga ‘yan uwanmu Falasdinawa.

Amma kafin hakan ya samu, dole mu fahimci yadda za mu yi amfani da yanayin da Musulmai na duniya suke ciki. Akwai ayar Qur’ani da ke cewa, “Allah ba Ya daura wa rai, sai abin da za ta iya.” (2:286).

Don haka za mu iya amfani da yanayin da muke ciki ya amfane mu ta hanyar bin hanyoyin da suke tafe;

1) Yawaita tunani mai kyau da sauran sauran hanyoyin da addinin Musulunci ya tanada na dauke damuwa. Wadannan hanyoyin an tabbatar suna rage damuwa, kuma an tabbatar suna kara samar natsuwa.

Neman agaji da rage damuwa ta hanyar addu’a da ibada da addu’o’i da karatun Qur’ani suna cikin wadannan hanyoyin.

Juriyar Musulman Falasdinu ya kara karfafa gwiwar Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba da dama a duniya wajen koya da karanta Kur’anin domin samun natsuwa da samu kwarin gwiwa da jagorancin rayuwa a lokacin da ake cikin tsanani.

Wa mata tana addu’a a lokacin da take rike da Qur’ani a Sallar Juma’a a Tehran. Hoto: Reuters

A wajen wadanda ba Musulmi ba, wasu hanyoyin tunane-tunane na zuciya da jiki suna taimakawa wajen rage damuwa da lafiyar kwakwalwa ta hanyar daidaita damuwa da neman sauki.

Tunane-tunanen zauciya da sauran hanyoyin rage damuwa na zuviya sun kunshi mayar da hankali wajen kula da yanayin numfashi da yadda mutum yake ciki a wannan dan tsakanin, kuma zai taimaka wajen rage gajiya, kula da damuwar da dauke gajiyar dadawa ana fuskantar rikice-rikice.

2) Mayar da hankali kan kula kai a matakin daidaikun mutane da ma al’umma a kan fafutikarmu.

Wannan zai taimaka wajen rike amanar da ke tsakaninmu na kula da lafiyarmu da ta al’ummarmu da ma ta Falasdinawa. Za a yi haka ne ta hanyar amincewa lallai kowane mutum yana irin tunaninsa, don haka kowane mutum yana bukatar mu’amala mai kyau da tausayi.

Kada ta takura wa kanka wajen yin abubuwa daban da sauran da kuke tare da su. kada ka bar tunanin wasu ko fargabar abin da za su fada ta hana ka neman agaji a duk lokacin da kake bukatar hakan.

Ka tuna cewa juriya na bukatar dagewa wajen kula da kanka sosai. Neman agaji daga mutanenmu na hanyoyin samar da waraka da addu’o’i za su taimaka wajen rage radadi da damuwa, wanda zai taimaka wajen samun karin juriya.

3) Kasancewa tare da al’umma na sa mutanen garin, wato wadanda suke da iyalai da abokai a Falasdinusu karfafi juna wajen tsallake bala’in da suke ciki.

Wannan zai karfafa gwiwar mutanen tare da taimakawa wajen fahimtar juna da karfin hada kai waje guda.

Dadin dadawa, Allah Ya albarkaci mutanenmu da karfin hali. Za mu iya tattarawa tare da amfani da matsayinmu da muke ciki, da iliminmu, da bangarorin da muke aiki da kwarewarmu da sauransu wajen taimakon Falasdinawa.

Idan muka hada karfi da karfe, za mu iya nema wa Falasdinawa adalci ta bangarori da dama.

Ta hanyar hadin kai, za mu iya tattarawa tare da gabatar da al’adunmu sannan mu bayyana darajarmu wadda a yanzu ke fuskantar barazana daga wasu kafafen sadarwa.

Muna da hakkin bayyana labarinmu da kanmu da bayar da tarihinmu da al’adunmu yadda muke so, sannan a gani, a kuma fahimce mu cikin sauki.

4) Muhimmantar da abubuwa masu dorewa ta hanyar yin abubuwan da za su taimaka wa Falasdinawa.

Duk da cewa bukatunmu sun bambanta, wannan tsarin zai kunshi yadda za mu tattauna da juna wajen samun waraka da ilimantar da juna ta hanyar lura da inda muke da kuma yiwuwar kawo sauyi.

Ka tuna cewa sauyi mai ma’ana na bukatar lokaci, duk da kokarinmu da muke yi, muna bukatar juriya domin samun nasara.

Duk da radadin da muke ciki, ko kuma saboda shi radadin, mun fahimci akwai bukatar fafutikar nemewa Falasdinawa adalci da kuma hada kai wajen karfafa wa juna gwiwa.

Mun fara hada karfinmu waje guda domin neman karin bayani a game da furucin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na cewa ana “kashe fararen hula ba gaira ba dalili” da ke aukuwa a “waje mai tarihi” saboda amfani da makamai da ba a taba ganin irinsa ba tun a shekarar 1977.

Mun hada kai baki dayanmu wajen neman adalci, muna amfani da muryoyinmu da dukiyarmu wajen neman kawo karshen yaki da cin zarafin mutane.

Falasdinawa na bukatar mu fito fili mu bayyana kanmu a wannan bigiren na yaki da rashin adalci, ta hanyar shirya kanmu da kara wa juna juriya.

Uwa uba kuma, muna daukar darasi daga karfin imanin Falasdinawa a rayuwarmu wajen gwagwarmaya.

Domin cigaba da wannan kokari, dole mu gano bukatunmu ta yadda za mu cigaba da rike amanarmu da ke tsakaninmu na ganin an kwato wa Falasdinawa ‘yanci.

Marubuciyar tana godiya da gudunmawar abokan aikinta na bangaren lafiyar kwakwalwa na Muslim Mental Health da Islamic Psychology Lab da ke Jami’ar Stanford: Heba Khan da Mawdah Albatnuni da Haneen Hammad da Nadira Baig suka bayar.

Marubuciyar, Dokta Rania Awaad M.D Farfesar lafiyar kwalkwalwa ce a tsangayar koyon likitanci ta Jami’ar Stanford, inda take rike da mukamin darakta a Cibiyar Kula da Lafiyar Kwakwalwa ta Musulmi wato Muslim Mental Health & Islamic Psychology Lab kuma jagorar wajen ibadar jami’ar.

A cikin gari kuma, ita ce shugabar Kungiyar Maristan.org, kungiyar da ke taimakon Musulmi, kuma ita ce daraktar Gidauniyar Rahman wadda ke taimakawa wajen ilimantar da ‘ya’yan Musulmi mata.

Kafin ta karanci likitanci, ta yi karatun addinin Musulunci a Damascus da Syria, inda take da shahadar karatun Ƙur’ani da shari’a da sauran bangarorin ilimomin addinin Musulunci da kimiyyarsa.

Togaciya: Ba dole ba ne ra’yin marubuciyar ya zama daidai da ra’ayi ko ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT World