Daga Firmain Eric Mbadinga
Nau'in abinci da ake binne su, sun kasance wasu muhimmin bangare na irin abinci da manoma ke samarwa, suna sauƙaƙa ire-iren nau'ikan abinci masu gina jiki da ake bukata, dalilin hakan ya sa ake daɗa samun bukatar neman sabbin irinsu masu inganci.
Masu aikin bincike a Burkina Faso sun samu nasara bayan shafe tsawon wasu shekaru suna aikin gwaje-gwaje kan wani sabon nau'in dankali, wanda mai zaki ne da yake da dandano ko kuma cika cikin dan'adam.
Masu binciken sun ce sabon nau'in dankalin hausan mai launin ruwan goro na dauke da sinadirai fiye da na sauran irin da aka sani, sannan ana bukatar tsawon watanni uku ne kacal wajen shuka da girbe shi, kazalika ba shi da wata illa ga lafiyar dan'adam.
An gabatar da sabon nau'in dankalin ne a Cibiyar 'De Recherche en Sciences de la Santé a Bobo-Dioulasso' a cikin watan Nuwamban a matsayin daya daga cikin hanyoyin da za a iya magance matsalar rashin abinci.
"Ko da yake har yanzu ba a kai ga kiyasta yawan amfanin gonan da za a samu a kowace hektar nau'in sabon dankalin ba, a cewar Dakta Koussao Somé wanda ke jagoranta bincike ga Ma'aikatar ilimi mai zurfi na kasar,''
A cewar Dakta Somé, dankalin zai iya mai da gurbin matsalar rashin alkama da kasashen waje ke fuskanta.
Kalubalen dogaro da kai
A shekarar 2024, batun samun wadataccen abinci zai kasance wani babban kalubale ga mafi yawancin gwamnatocin Afirka wadanda ke ware albarkatu masu yawa don shigo da kayayyaki daban-daban da kasashen waje.
Shekaru biyu da suka gabata, Bankin Faya Kasashen Afirka ya yi nuni da cewa, wannan yanayin na shigo da kayayyaki ya samo asali ne tun a shekarun 1980, sannan an yi hasashen ''dogaro da Afirka ke yi wajen shigo da abinci zai kai dalar Amurka biliyan 110 nan da shekarar 2025.''
Wannan yanayi na dogaro da abinci, musamman kayayyakin da ake nomawa, ya zama tashin hankali ga hukumomi da masana tattalin arziki da kuma al'ummar kimiyya a Afirka.
Game da wannan koma baya da aka samu, Dakta Somé ya bayyana kwarin gwiwar binciken tawagarsa bisa ga halin da ake ciki.
Yana mai kari da cewa makasudin binciken shi ne bai wa al’ummar Burkina Faso miliyan 20 damar samun wani nau'in dankali mai zaki da aka saba samu a kasuwanni.
A cewar tawagar Dr Somé, irin noman da tawagar suka tsara tare da yanayin girbansa yana da matukar kyau ta fuskoki da dama.
"Mun fahimci cewa dankalin da ake samu a Burkina Faso galibi farare ne wadanda nau'insu ba su da inganci ga lafiya dan'adam, a hakan ne yasa, muka yanke shawarar samarwa mutane dankalin da za su ci mai inganci," a cewar Dakta M M, wani babban mai bincike kan kwayoyin halitta da inganta tsirrai a yayin hirar da TRT Afrika ya yi da shi.
Dokta Somé, wanda aka ba shi lambar yabo na "Chevalier de l'ordre du mérite de l'Étalon" don karrama aikinsa a shekara 2002, ya bayyana cewa a farkon binciken da tawargarsa suka yi ne suka yanke shawara kan cewa akwai yiwuwar a inganta farar nau'in dankali mai zaki da ake da shi ta hanyar amfani da wasu dabaru na kimiyya.
Masu binciken Burkina Faso sun zabi sinadarin bitamin A da iron da zinc da iodine da kuma beta-carotene a matsayin abubuwan da za su inganta nau'in farin dankalin.
Tsarin gwaje-gwaje
La'akari da cewa za a iya noman sabon nau'in dankalin tare da fitar da shi zuwa kasashe da ke makwabtaka da Burkina faso, masana kimiyyar sun gudanar bincike kan noman irin a dakin gwaje-gwaje.
"Mun samo nau'o'in irin ne daga Cibiyar Dankali ta kasashen waje, wacce kuma ta ke aiki kan dankali mai zaki da kuma abokan aikinmu a yankin Gabashin Afrika.
Mun san cewa wadannan nau'in sun dace da yankinsu da suka samo asali da yanayin lokacin shuka da girbaisu da kuma yanayin kasa da dai sauransu," in ji Dakta Somé.
Ya kara da cewa sun yi amfani da "wadannan nau'u'kan ne a matsayin ainihin tushe iri na dankalin da muke hada su da nau'in namu na gida tare da fatan cewa kwayoyin halitta da suke da shi mai dauke da sinadarin bitamin irin su beta-carotene za a shiga cikin sabon nau'in dankali mai zakin."
An fara aiwatar da tsarin ne a shekara ta 2008, wanda ya dauki Darka Somé da tawagarsa mai mutum 11 tsawon shekaru shida don samun sakamakon farko da ya kai su ga karshen binciken.
Masu binciken sun sami damar samar da irin dankalin mai zaƙi guda biyar, wadanda duka suka samu amincewa.
"Mun gano cewa nau'o'in iri na shekarar 2014 da aka samu sun dace da asalin tushen halittarsu, suna da launi mai kyau da isasshen sinadarin beta-carotene, amma matsalar da suke da shi ita ce ta saurin kamuwa da cututtuka," in ji Dokta Somé.
Bisa ga wadannan sakamakon da aka samu, masu binciken suka fara aiki tare da kudurta cewa za su cimma sakamako a shekarar 2018 wanda zai faranta musu rai.
Nau'ika uku na sabbin irin dankalin sun fito da ingantattun iri kusan irin na 2014 tare da iya jurewa daukar cututtukan.
''A yanzu mun kai wani mataki game da bunkasa tsarin iri, sannan mun kara inganta gwaje-gwaje na noman in- vitro, mun samar da tsarin da ya dace wanda zai ba da damar yin noman ire-iren irin dankalin hausawa da yawa," kamar yadda Dakta Somé ya shaida wa TRT Afrika.
An horar da manoman yankin da dabarun da za su dace don noman wannan sabon iri na dankalin, sannan sun amfana da bangaren bayan girbi ma.
Kazalika an shigar da Cibiyar Nazarin Kimiyya da Fasaha ta kasar da sashen fasahar abinci na kasar cikin wadannan tsare-tsaren.
"Idan ka zo Burkina Faso a yau, za ka samu nau'in dankali mai zaki launin kalar lemu da aka sarrafa, cikin har da suka hada da soye da biskit da biredi da ruwan sha na dankali,'' in ji Dakta Somé.
Dakta ya kara da cewa Idan aka hada burodi da garin dankalin, zakinsa ya kai kwatankwacin kashi 35 cikin 100 na alkama.
Bayanai da aka tattaro daga mutanen da suka dandana sabon nau'in dankalin ya nuna ingancinsa.
Mun gamsu “Idan aka yi la’akari da sha’awar da manoma da ‘yan siyasa da likitoci da sauran al'umma suka nuna kan nau'in dankalin.
Mutane suna kara samun abubuwa kala-kala da irin wannan iri, idan yaro ya ci giram 135 kacal na wannan dankalin da shinkafa kullum, hakan ya ishe shi samun sinadarin bitamin da jiki yake bukata,” in ji Dakta Somemé.
Sabbin batutuwan da suka dauki hankalin tawagar masu binciken dankalin sun hada da samar da yanayin dorewar nau'in irin abinci da ake binne su 100 bisa 100 ba tare da sauya ƙwayoyin halittunsu ba.
Baya ga dankalin mai zaki, Dakta Somé da tawagarsa na masu binciken suna aiki a kan sauran nau'in abinci da ake binne su kamar doya da manioc da sauran nau'in dankali iri daban-daban don inganta dandanonsu da aikinsu na gina jiki