Daga Tariq Abdul-Wahad
A makon da ya gabata, masu wasannin daga faɗin duniya sun isa Paris - babban birnin wata ƙasa wanda wani zai iya kuskuren cewa jagora ce wurin dimokuraɗiyya. Sai dai mun san komai. Mun san cewa Faransa ƙasa ce wadda ta yi mulkin mallaka kuma wadda tsufa ta yi wa gardama.
Kasa mai tabarbarewar tarbiyya wadda a zahiri take da karanci albarkatun kasa; ƙasa ce wadda take iƙirarin "Faransawa" na kan gaba wanda hakan a mafarkinsu ne. Sai dai wannan mafarkin da suke yi ne ke haifar musu da wariyar launin fata da tsare-tsarensu na ƙin jinin baƙi waɗanda ƙasar ke cusa wa 'ya'yanta.
An ƙi barin 'yan wasa mata Musulmai su saka kallabi a lokacin da suke gasar ta Olympics. Me ya sa? Saboda Faransa ta gaza a aikinta na mulkin mallaka.
Da a ce Faransa ƙasa ce mai dattaku, da za ta kalli sauran ƙasashen duniya ta sauraresu, ta kalle su sannan ta yi koyi da su. Sai dai a yayin da ƙasashen duniya suka zo har bakin ƙofarta, Faransa za ta ci gaba abin da take yi ta kuma rasa bikin baki ɗaya.
Domin ƙara wa ciwo gishiri, an bar Isra'ila tana alfahari inda 'yan wasanta za su wakilce ta a gasar a daidai lokacin da Isra'ilar ke aikata kisan kiyashi, yayin da 'yan wasan Rasha da na Belarus ba za su iya wakiltar ƙasar ba saboda shugabanninsu sun saɓa dokokin ƙasa da ƙasa.
Wannan munafuncin ba abin mamaki bane sannan kuma ba sabon abu bane. Tsawon shekaru, ƙasashen da ke mulkin mallaka na amfani da ƙarfinsu na siyasa a wurin da suke iyawa, inda suke amfani da kafofin watsa labarai domin cim ma burinsu.
Lamarin bai da babamnci da abin da ke faruwa a Faransa, inda take da kafar watsa labarai wadda masana ke ganin tana bayyana kaso 13 cikin 100 na ainahin abin da ke faruwa.
Masu sharhi kan wasanni wanda aka zaɓa suna bayyana ra'ayoyinsu a ɗakunan watsa labarai inda baƙin da suke gayyatowa ba sa faɗin gaskiya tare faɗin kalaman wariyar launin fata da na cin mutunci. C8, wadda ɗaya ce daga cikin kafofin watsa labarai ta Bolloré Group, ba da jimawa ba aka ci tararta euro miliyan 7.6 sakamakon katoɓarar da wani mai gabatar da shiri ya yi.
Barazana ga Musulunci
Menene masu sharhi suka firgita da shi, kuna iya mamaki? Musulunci. Yawanci kowace kafar watsa labarai abin da take mayar da hankali shi ne Musulunci - addinin da Jamhuriyar ta dauka bai dace da ɗabi'un ƙasar ba.
Yawancin kafafen yada labarai na Faransa, karkashin jagorancin wadannan tashoshi masu zaman kansu, sun tozarta Musulunci da Musulmai tare da dafin su. Kiyayyar Islama da ba ta da tushe ita ce ginshiƙin kafofin watsa labaru na Faransa, don haka ba abin mamaki ba ne cewa ta baza dafin a cikin al'umma.
Ta haramta amfani da gyale a 2004. Ba da jimawa ba, a 2023, ta haramta amfani da abaya a makarantun gwamnati. Kayan ninƙaya na mutunci wanda ake kira da "burkinis," su ma an haramta amfani da su.
An bayar da kudirin wata doka wadda ta haramta wa mata masu saka hijabi halartar tafiye-tafiyen makarantu da 'ya'yansu. Hukumar wasannin ƙwallon ƙafa da ƙwallon kwando ta haramta mata masu wasanni daga saka hijabi.
A yayin da take magana dangane da mata Musulmai masu wasanni, Dakta Haifi Tlili, wadda masaniyar ilimin zamantakewa kuma wadda aka ƙirƙiro ƙungiyar Basket Pour Toutes da ita ta bayyana cewa, "Ba a ganisu kuma suna tauye hakkin ɗan'adam."
Da sunan matsananciyar fassarar ilimin addini, al'ummar Faransa ta yi fice sosai wajen kyama. Tana da manufa guda biyu: na farko, al'ummar musulmi sun zama wata hanya da 'yan siyasa ke amfani da ita domin cim ma muradunsu na kishin ƙasa
Haƙinanin halayya
A bayyane take kan cewa Faransa na tsakiyar rikicin siyasa. Bayan Shugaba Emanuel Macron da gwamnatinsa sun rasa kujerunsu a majalisar Turai ga masu tsatsauran ra'ayi na National Rally party, Macron ya rusa majalisar dokokin kasar, wanda ya haifar da zaben majalisar dokoki nan take.
A wannan zaɓen, Jam'iyyar National Rally ta ci zaɓe a karon farko a wurin zaɓe da kaso 33.21 cikin 100.
Bayan mako guda, sai kariyar fuskar tasu ta fita inda Faransa ta nuna fuskarta ta ainahi maras kyau.
Masu tsatsauran ra'ayi sun ta buɗe bakunansu a kafofin watsa labarai da kuma kan tituna inda suke kalamai na wariyar launin fata marasa tunani.
Nasarar wata jam'iyyar da aka kafa sakamakon yakin duniya na biyu da masu goyon bayan 'yan Nazi na haduwa kan shugabancin Faransa. An kai wa wasu Faransawa wadanda ba fararen fata hari ba, yayin da wasu ke fargabar makomarsu a kasar.
Wannan maganar ta wuce inda ake tunani, Wani zai iya cewa wariyar launin fata a Faransa ta sauya zuwa wani sabon abu.
A yadda abubuwa suka sauya, masu sassaucin da masu matsakaicin ra'ayi sun yi ƙoƙarin toshe ƙuri'un masu tsatsauran ra'ayi ta hanyar cire ɗan takararsu na uku daga gundumomi.
Gamayyar masu sassaucin ra'ayi ta Green, da masu ra'ayin kwaminianci da masu ra'ayin gurguzu, da na "La France Insoumise", inda suka ci akasarin kujeru a zagaye na biyu tare da hana masu tsatsauran ra'ayi samun nasara.
Duk da cewa masu sassaucin ra'ayi ba su samu nasara a zaɓen ba, Macron da cacarsa ya nuna cewa a shirye yake ya yi amfani da san rai wurin cim ma burinsa a maimakon walwalar jama'a.
Sauya manufofi
Faransa a matsayinta na ƙasa na amfani da girman kai wurin mulkar jama'ar ƙasarta. Ko kuma aƙalla takan yi hakan. Sakamakon Emmanuel Macron na kan shugabancin ƙasar, an bayyana karara cewa duk wani ci gaba da Faransa ta samu wajen kafa kanta a matsayin dimokuradiyya ya ruguje.
Ba da jimawa ba, amfani da sashe na 49 na kundin tsarin mulkin Faransa ya jawo caccaka da zanga-zanga da kuma jawo caccaka har ma da tarzoma a gaban gidan Macron.
Wannan kudirin zai bayar da dama ga gwamnati ta tsallake majalisa da kuma tilasta amincewa da dokar ba tare da da ƙuri'a ba.
Ta hanyar shigo da wasu tsare-tsare irin waɗannan, ( wato amincewa da dokar ƙara shekarun ritaya), Macron ya ba mu tsoro game da ruhin gwamnatin da ya kafa: mulkin da ke ba da fifiko a fagen siyasa da aiwatar da sauye-sauye marasa farin jini cikin sauri maimakon tsarin dimokuradiyya da amincewar jama'a.
Bayan Jam'iyyar Macron ta rasa rinjaye a wani ƙaramin zaɓen Majalisar Tarayyar Turai, da ya sani bai rushe majalisar ƙasar ba.
Wasu na ganin ya ɗauki wannan matakin ne domin kawar da hankali daga abin da ke kan gaba; rushe majalisar zai hana kafofin watsa labarai yin sharhi game da rashin nasara a zaɓen. Sai dai bayan rushewar, ya sake shan wani kaye bayan da haɗakar masu sassaucin ra'ayi suka yi nasara.
Jam'iyar tasa ta rasa kujeru 84 a zaɓen. Amma duk da haka, ya jajirce, yana mai iƙirarin cewa masu sassaucin ra'ayi suna buƙatar cikakken rinjaye don kafa gwamnati. Jam'iyyarsa a 2022 ba ta samu cikakken rinjaye ba a lokacin da ya nada sabon Firaminista.
Buƙatar samun nasara a kowane lokaci a zaɓe ke sa Macron sauya manufofinsa a duk lokacin da ya samu dama saboda kada ya yi rashin nasara. Matsalar a nan ita ce bai kamata mutum ya rinƙa wasa da abin da mutane suke so ba.
Wasa ne mai hatsarin gaske a kasar da tuni aka yi hukuncin daurin rai da rai d ya haifar da juyin juya hali.
Amma mayafin mulkin mallaka yana dagawa; Ba za a sake yin shiru ko kuma yi wa jama’a amfani da masu mulki ba
Gasar Olympics ta shaida hakan, inda 'yan wasa da magoya bayanta ke rike da tutocin Falasdinu a matsayin juriya, ciki har da 'yan wasan ninkaya na Olympic Valerie Tarazi da Yazan al-Bawwab.