Leeds - A yadda nake tafiya kan titi a kullum da ɗan ƙaramin yarona, akwai wani layi wanda ba gani da ke nuna cewa na juya na koma wurin da na fito.
Idan aka ƙetara wannan layin, akwai rukunin gidaje waɗanda akasarinsu fararen fata ne 'yan Ingila waɗanda ba su son Musulmai.
Wasu mutane a Birtaniya suna magana a kan "wuraren da ba a zuwa," waɗanda suke ganin wurare ne da Musulmai ke iko da kan titunan ta hanyar amfani da dokokin shari'a.
Sai dai babu mai magana a kan asalin wuraren da mata Musulmai a Birtaniya ba su da ikon zuwa, kamar ni.
Tun a makon da ya gabata bayan an caka wa wasu mata wuƙa a Southport da kuma rikicin da masu tsatsauran ra'ayi suka tayar wanda ya samo asali sakamakon labaran ƙarya da aka yaɗa kan wanda ake zargi da kisan, Axel Rudakabana mai shekara 17, wuraren da ba a zuwa sun ƙaru a aƙasarin Yorkshire, wanda shi ne garin da nake zama.
A ƙarshen makon nan, wata mata Musulma a Middlesbrough, da ke North Yorkshire, ta kasance wadda masu tsatsauran ra'ayi da ke zanga-zanga suka watsa wa acid.
Tun bayan nan, sai iyayena na mijina suka buƙaci kada na yi amfani da ababen sufuri na jama'a ko kuma na je Leeds ko kuma Wakefield, waɗanda su ne birane da suka fi kusa da ni.
Dokar kulle
A halin yanzu lokacin hutun makarantu ne na bazara a Birtaniya, haka kuma baya ga cewa na samu damar zama a gida da kuma shiga lambu idan ina buƙatar shan iska ko kuma wurin da yarona zai yi wasa, ba ko wace mahaifiya Musulmai ko baƙar fata ko 'yar nahiyar Asia da za ta iya haka ba.
Waɗanda ke zaune a gidaje waɗanda ba bene ba waɗanda ke da yara da yawa sun dogara ne kan wuraren wasa na unguwa ko kuma su bar 'ya'yansu su yi wasa a waje kan layi.
Haka kuma sun dogara ne kan abubuwan wasannin bazara da ɗakunan karatu da masallaci.
A halin yanzu zuwa waɗannan wurare domin shaƙatawa ya zama wani abin da ba zai yiwu ba, sakamakon titunan sun koma wuraren da ake cin mutunci da sata da ƙone-ƙone, inda masallatai suke zama wuraren da ake hari da kuma cinna wa wuraren karatu wuta.
A taƙaice, iyaye mata Musulmai irina da ke zaune a Birtaniya na jin tsoron rayuwarmu da ta 'ya'yanmu.
Tarzomar ta soma ne a Merseyside da ke arewa maso yammacin Ingila inda daga bisani ta ƙara bazuwa zuwa wasu birane da ke arewa maso gabashin Ingila, da Yorkshire da Midlands irin su Manchester da Hartlepool da Liverpool da Leeds da Rotherham da Tamowrth da Nottingham.
Waɗannan wurare ne waɗanda ke da ƙabilu da dama da kuma masu gudun hijira. Zuwa yau, wannan tarzomar ta ƙara bazuwa zuwa wuraren da suka haɗa da Belfast da ke Northern Ireland.
A ƙarshen mako, abokaina Musulmai da baƙaƙen fata da 'yan Asia sun rinƙa tura mani saƙonnin soyayya da goyon baya, inda duk ake yi wa juna fatan alkhairi kan a kasance cikin aminci idan za a fita.
Ana ta tura saƙonni ta Whatsapp inda ake bai wa mutane shawara kan lokuta da wuraren da za a tayar da tarzoma a gaba tare da bai wa 'yan'uwa mata Musulmai shawara kan su zauna a gida.
Wasu daga cikin Musulmai 'yan Birtaniya na cewa wannan ne ainahin abin da masu tsatsauran ra'ayin riƙau da ke zanga-zanga suke so.
Sai dai a matsayina na uwa, ba wai aminci na kaɗai nake dubawa ba. Dole ne na yi tunani kan yiwuwar yarona wanda ke da jinin Larabawa da kuma Asia a matsayin wanda za a iya kai wa hari.
Musantawa da kuma harzuƙawa
Tun da farko a ranar Litinin, Firaminista Keir Starmer ya bayyana cewa, "Ko mene ne dalilin da ya sa, wannan ba zanga-zanga ba ce.
Tashin hankali ne tsantsa, kuma ba za mu amince da kai hare-hare a kan masallatai ko kuma a kan al'ummar Musulmi ba."
Amma mutane da yawa a nan ba su so su amince da gaskiyar abin da ke faruwa a nan. Babu shakka waɗannan wasu ranaku ne mafi duhu da na yi rayuwa a cikin Birtaniya.
Makonni kadan da suka gabata, na rubuta wata kasida game da abubuwan da na fuskanta na karuwar wariyar launin fata da ƙyamar Islama a kan ababen haya na jama'a tun lokacin da aka fara yakin Gaza a watan Oktoban 2023.
Na haɗu da wani farar fata a shafukan sada zumunta wanda ya kira ni da "mai saurin fushi" tare da cewa babu wani abu a duniya wai shi ƙyamar Musulunci.
A halin yanzu muna fama da kai hare-hare kan ƙabilu a otel-otel da gidaje waɗanda akasarinsu Musulmi ne masu neman mafaka, da masallatai da mata masu saka hijabi. Sai dai 'yan siyasa da wasu kafafen watsa labarai na amfani da kalamai irin su "tarzoma" ko kuma "zanga-zangar ƙin jinin 'yan cirani" maimakon a kira ta da sunanta na - zanga-zangar ƙin jinin Musulmi da ta'addancin cikin gida. Wannan yana sa ni ji kamar ana harzuƙa ni a wani babban mataki.
Rikicin masu tsatsauran ra'ayi da kyamar musulmi a halin yanzu yana tunawa da duk abin da iyayena da surikina suka shaida kuma suka gani kafin na gani lokacin da suke zaune a Birtaniya shekarun da suka gabata.
Rayuwar iyayena ta yau da kullum ta sha fama da wariyar launin fata da ƙin jinin Musulmi tsawon shekarun 1980 da 1990 a Landan, wanda hakan ya ƙaru bayan faruwar harin 9/11.
Surukaina sun sha ganin tarzoma iri-iri daga ciki har da wadda aka yi a Leeds da Bradford a shekarun 1980, da kuma tarzomar da aka yi ta Dewsbury a 1989 da ta Bradford a 2001.
Ba zan iya tunanin yadda wannan zai iya tuna musu da firgicin da suka shiga ba.
Damuwa kan nan gaba
Na kasance ina yawan fatan alkhairi ga yadda ɗan ƙaramin yarona zai samu gobe mai kyau, cewa zai girma a cikin al'adu da yawa na Biritaniya wanda a ƙarshe zai kawar da wariyar launin fata gaba ɗaya.
Yanzu ina ƙalubalantar ikon gwamnatina wurin kawar da barazanar da ke ci gaba da karuwa ta masu tsatsauran ra'ayi da kuma tunanin ko a ƙarshe Biritaniya za ta shiga sahun sauran ƙasashen Turai waɗanda suka faɗa ƙarƙashin jam'iyyun siyasa masu tsatsauran ra'ayin mazan jiya.
Yayin da matasa ‘yan kasa da shekara 14 ke shiga cikin gungun masu tayar da tarzoma, ba na yin bege ga mutanen Ingila na gaba su zama masu kyamar wariyar launin fata.
Kwanaki takwas da suka gabata na tarzomar da aka tayar saboda ƙyamar Musulmi wata alama ce da ke nuna wani mataki na ƙin jinin Musulmi a faɗin Birtaniya.
Ina son sauran abokaina waɗanda suke magana kan cewa ba za su taɓa tunanin irin wannan na faruwa a ƙasashensu ba, lallai su farka daga mafarkin da suke yi tare da nuna goyon baya ga Musulmi da baƙar fata da 'yan yankin Asia da maƙwabta.
A daidai lokacin da nake fama da ranaku mafi muni a gare ni na ƙin jinin Musulunci, ina ta tunanin idan ɗana nan gaba zai fuskanci irin wannan lamarin.