Firaministan Hungary Viktor Orban a kwanan nan ya karɓi baƙuncin shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno a Hungary. Photo: AFP By Fuat Sefkatli

Daga Fuat Sefkatli

Yankin Sahel na Afrika a baya bayan nan ya zama waje mafi ɗaukar hankali ta fuskar ƙaruwar zaman ɗarɗar a siyasar yanki, wanda ya siffantu da ƙaruwar ayyukan ƴan'ta'adda da kuma gogayya tsakanin manyan ƙasashen duniya.

Biyo bayan juyin mulki a Mali, da Burkina Faso da kuma Nijar, an lura rundunar soji da suka daɗe, musamman na Faransa da Amurka sun gushe, abin da ya bai wa Rasha damar samun wajen zama. Rundunar Bayar Da Horo Ta Tarayyar Turai (EUTM), da ta soma aiki a 2013 ta kammala wa'adinta na shekara 11 a watan Mayu.

Wacce ta ƙunshi ƙasashe mambobin Tarayyar Turai guda 22 da kuma ƙasashe huɗu da ba mambobin Tarayyar Turai ba, rundunar bayar da horon ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta ƙarfin dakarun rundunar sojin ƙasar Mali da kuma sashenta na bayar da horo.

EUTM ya yi aiki tare da rundunar yaƙi da ta'addaci ta Faransa mai suna Operation Barkhane.

Ayyukan soji na ƙasashen yammacin duniya, musamman waɗanda Faransa da Amurka suka jagoranta, sun gaza samun goyon bayan a cikin yankin.

Dambarwar siyasa da ta soji da suka biyo bayan juyin mulkin ya haifar sun haifar da abin da bai taƙaita ga ƙin jinin yammacin duniya ba kaɗai, har ma da nuna mummunar adawa da tasirin da ƙasashen yamma ke da shi ta fuskar zamantakewa da siyasa da al'ada.

Babban abun da ya haifar da ficewar manyan ƙasashen yamma daga yankin shi ne ƙawance tsakanin ƴan siyasa da sojojin ƙasashen yankin guda uku.

Abin tun farko ya fara ne a matsayin wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Burkina Faso, da Nijar da kuma Mali, daga bisani ya zama Kungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Sahel.

Tunda aka kori ƙawayen yammacin duniya da aka saba hulɗa da su, sai suka koma da ayyukansu na soji ƙasashe masu makwabtaka, da suka haɗa da Chadi da sauran ƙasashen Afrika ta Yamma.

Bugu da ƙari, yanayin tsaro da ke bayyana bayan shekaru 12 ya haddasa wani muhimmin nazari a tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai.

Saboda matsayinta na uwar gijiyar mulkin mallaka, a tarihance Faransa ta wuce gaba a aikin kiyaye zaman lafiya da bayar da agajin jin ƙai a Afrika.

Sai dai kuma, an tilasta mata ta janye daga yankin a wani ruɗani na take haƙin ɗan'adam da kuma zarge zarge kan tsoma baki al'amuran ƙasashe masu cikakken iko.

Yayin da ake ci gaba da tafka muhawara kan wace ƙasa ce ko wane ƙawance ne zai iya cike gurbi sannan kuma ko a shiga al'amuran yankin Sahel masu sarƙaƙiya da ɗaure kai, sai ga firaministan Hungary Viktor Orban kwanan nan ya karɓi baƙuncin shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno a Hungary.

Bayan tattaunawarsu, Orban ya sanar da shirin tura sojoji kimanin 200 zuwa Chadi.

Saboda muhimmancinta a siyasar yanki, Chadi ta zamo wata muhimmiyar ƙawa a shirin Tarayyar Turai na yaƙi da kwararar baƙin haure biyo bayan taɓarɓarewar yanayin tsaro, da dambarwar siyasa da kuma dalilai na tattalin arziƙi a yankin na Sahel.

Saboda haka, Orban, har ila yau, ya jaddada muhimmancin rawar da Chadi za ta taka wajen yaƙi da kwararar baƙin haure.

Abu mafi muhimmanci, a yankin da ke fama da rashin kwanciyar hankali da rashin tabbas, Chadi ta kasance ƙasa ɗaya tilo da za ta iya zama ƙawar ƙasashen yammacin duniya, idan aka kalli abin ta fuskar siyasar yanki.

Furucin da Orban ya yi da kuma shirin tura sojojin ya nuna cewa Hungary na iya zama babbar ƙawa daga ƙasashe mambobin Tarayyar Turai wajen cike giɓin yanki da siyasa da Faransa ta bari a yankin Sahel.

Turai da siyasar duniya

Hungary, wacce a yawancin lokaci ba ta cika jituwa da ƙasashe mambobin Tarayyar Turai kan batutuwan siyasa da tattalin arziƙi da kuma na soji ba, ta assasa batun ƴancin cin gashin kai da na yanke shawara a siyasar ƙasashen Turai, musamman ma tun soma yaƙin Rasha da Ukraine.

Yayin da take jaddada zama ƴar ba -ruwanmu a rikice rikicen duniya, Hungary na kira ga a ci gaba da hulɗa da Rasha ta hanyoyin diflomasiyya, sannan ta buƙaci a samu sauyin cikin sauƙi a dangantaka bayan yaƙi.

Sanannen abu ne, firaminista Orban shi kaɗai ne shugaban Turai da ya kai ziyara Rasha tun ɓarkewar yaƙin.

Wani babban cigaba da ya jaddada matsayin Hungary a muhimmin lokaci a siyasar duniya shi ne ɗarewar ta kan karagar shugabancin Majalisar Tarayyar Turai.

Wannan muƙamin ya bai wa Budapest wata dama wacce ba kasafai ake samun irinta ba, ta gabatar da manufofinta na ƙasashen waje mafi muhimmanci, a tattaunawa a Tarayyar Turai.

A iya tsawon wa'adin shugabancin nata, Hungary tana da yadda za ta yi, ta tsara ajandar Tarayyar Turai, don ta dace da nata manufofin kan siyasar yanki. Bugu da ƙari, wannan lokacin zai iya bai wa Hungary damar yin amfani da matakai masu ƙarin karsashi da hangen nesa.

Yayin da tasirin sojin Tarayyar Turai a Afrika ke disashewa, matakin Orban na tura dakaru Chadi, ya nuna burin Hungary na ƙarfafa matsayinta a cikin Tarayyar Turai da kuma jaddada matsayinta na zama babbar mai-faɗa-a-ji, wajen bayar da kyakkyawar gudummawa a Manufofin Tarayyar Turai Kan Tsaro Da Kariya.

Muhimman buƙatu a yankin Sahel

Matakin na Hungary na tura sojoji babban birnin Chadi na N'Djamena, ya bayyana manyan muhimman batutuwa da dama.

Na farko shi ne damar maye gurbin da raguwar tasirin Faransa a Afrika ya samar, yana nuna Hungary a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa a cikin da'irar manufofin siyasar yanki na Tarayyar Turai.

A matsayinnsa na babbar hanyar kwararar baƙin haure daga ƙasashen Afrika yamma da sahara zuwa tekun Mediterranean da kuma tsallakawa ƙasashen Tarayyar Turai, yankin Sahel na ci gaba da kasancewa muhimmi ga kula da tsaron iyakokin ƙasashen Turai.

Yin watsi da wannan yankin zai iya haddasa matsalolin tsaro da na ƙaura nan gaba. Wani muhimmin bangare shi ne ƙaruwar sha'awar da Hungary take da ita, ta kai wa ga dinbin albarkatun ƙarƙashin ƙasa da yankin ke da su, da suka haɗa da ɗanyen mai, da zinariya, da kuma sinadarin Urainium.

Tattalin arziƙinta da ke bunƙasa da kuma ƙaruwar tasirinta tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai, sun sa Hungary na kallon raba ƙafa wajen samar da damarmakin tattalin arziƙinta a matsayin muhimmi.

Samar da damar shigar kamfanonin Hungary cikin kasuwanni Afrika babban dalili ne na wannan yunƙuri a fannin sojin. Bugu da ƙari, Hungary na son daidaita dangantakarta tsakanin Gabas da Yamma.

Idan ta samu gindin zama a Afrika, Hungary za ta iya samun ƙarin hulɗa da Rasha da China, waɗanda ke faɗaɗa tasirinsu a yankin - Rasha ta hanyar rundunar tsaro ta Wagner Group da kuma sabuwar rundunar tsaro ta African Corps, ita kuma China ta al'amurra na tattalin arziƙi.

Sai dai waɗannan matakan suna tattare da manyan ƙalubale. Saɓanin ayyukan kiyaye zaman lafiya ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Turai, tura sojoji zuwa Chadi da Hungary ta yi, shi ne aikinta Irin wannan na farko, abin da ke haifar da damuwa game da kayan aiki, da tsare-tsare da kuma sadarwa a yankin da harsunan da hukuma ke amfani da su sune Larabci da Faransanci.

Bayan wannan, rashin kwanciyar hankali a Chadi da ma sauran yankin Sahel na iya kawo rarrabuwar kai na cikin gida a cikin rundunar sojin ƙasar Hungary sannan kuma ya haifar da matsala wajen ɗaukar sabbin sojoji aiki.

Duk da waɗannan damuwoyin, Tarayyar Turai ta yi maraba da shirin na Hungary, inda jami'an Tarayyar Turai ke cewa yana da muhimmanci ƙarin ƙawaye na ƙasa da ƙasa su ƙulla dangantaka da Chadi.

Ana yi wa tura sojoji yankin Sahel da Hungary ta yi kallon matakin da ya dace, musamman ma da yanzu ƙarfin faɗa-a-jin Rasha ke ƙaruwa.

Muhimmin matakin da Hungary ta dauka na shiga Chadi ya nuna girman burinta na ƙarin taka rawa a cikin kungiyar Tarayyar Turai da kuma a matakin duniya.

Yayin da ta ke ƙoƙarin daidaita hulɗa tsakanin Gabas ta yamma, da samu albarkatun ƙarƙashin ƙasa da kuma magance matsalolin baƙin haure, Hungary na kafa kanta a matsayin jigo wajen daidaita manufofin tsaro na Tarayyar Turai.

Amma dai kalubale wajen kayan aiki da kuma rikice rikicen yankin zai iya zama matsala babba. Yadda Hungary ta tunkari waɗannan matsalolin zai nuna nasararta ta lokaci mai tsawo a yankin Sahel da kuma a cikin siyasar yanki ta Turai.

Marubucin, Fuat Emir Şefkatli, mai bincike ne mai zaman kansa da ya ƙware kan batutuwan da suka shafi Afrika ta Arewa

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar tunani ko ra'ayoyin tsarin iditocin TRT Afrika.

TRT Afrika