Amurka na amfani da takunkuman tattalin arziki wajen kuntatawa kasashen duniya.. / Hoto: AP

A sama da shekaru 30 da suka gabata, takunkuman tattalin arziki sun zama hanyoyi mafi muhimmanci a fannin tattalin arziki da Amurka da kawayenta na Yamma ke amfani da su wajen kalubalantar abokan adawa.

Manufar ita ce a magance kalubalen kasa da kasa kan zaman lafiya da tsaro d aya shafi kawo karshen ikicin cikin gida da hare-haren kan iyaka, da ma kawar da barazanar yaduwar nukiliya da yawaitar keta hakkokin dan adam da ta'addanci.

Sun samu karfin gwiwa daga hadin kan kasashen duniya masu karfin fada a ji a lokacinda suke fatan kawo karshen yakin cacar baki a 1980, takunkuman farko sun fito ne daga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya kai ga kawo karshen mulkin farar fata 'yan tsiraru a Afirka ta Kudu, kawo karshen yake-yake a yankin Balkan, da Saliyo, Liberia da Angola.

A yayinda Amurka da Ingila ke kan gama a wancan lokacin, dukkan mambobin MDD sun amince da aiwatarwa da zartar da wadannan matakai.

A karkashin wadannan matakai, Amurka ta fadada irin takunkuman da take saka wa kasashe da kuma yawan kasashen da ta ke kakabawa.

A lokacin da shekarar takunkuman ta fara, an saka wa kasa da kashi goma na tattalin arzikin duniya takunkumi. A yanzu kusan daya bisa uku na tattalin arzikin na karkashin takunkumai.

Kazalika, a 2024 takunkuman tattalin arziki sun sun zama mafi muni daga cikin rikice-rikice takwas a duniya da suka janyo rikicin jin kai, kamar yadda kungiyar Cobcern Worldwide ta bankado kuma ana aiwatar da su a yankunan da ake manyan rikice-rikice 10 na duniya.

Manyan soke-soke

A shekaru 10 da suka gabata, an samu masu suka da yawa musamman ga Amurka kan yadda ita daya tilo take saka wa kasashe da daidaikun mutane takunkumai.

Suna kalubalantar tasirin takunkuman da mummunar illar da suke janyi wa hakkin dan adam da jin dadinsa.

Wani mai muhawara na cewa a yanzu Amurka ta skaa wa kasashen duniya 38 takunkumai saboda batutuwan da suka shafi ta'addanci da fataucin ɗan'adam, wannan na nufin ana yawaita saka takunkumin daga shugaban kasa ko majalisar dokoki. Kuma sun gaza cimma manufofinsu a shekarun da suka gabata.

Babbar shaidar da ke tabbatar da hakan shi ne yadda ake ta sakawa kasashe irin su Cuba, Venezuela, Iran da Koriya ta Arewa takunkumai kuma ba tare da cimma wata nasara ba.

Wani shi ma da yake sukar lamarin ya bayyana babbar illar takunkuman kan tattalin arziki da zamantakewar fararen hula d aba su ji ba ba su gani ba a wadannan kasashe.

Musamman saka takunkumai ga bankuna da hana su shiga kasuwannin kasa da kasa a dama da su na janyo tashin farashin kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki da ma ingancin rayuwa.

Wannan na yawan munana hakkokin dan adam a kasashen da azzulamn shugabani ke jagoranta.

Haka kuma, a al'ummun da suke shan wahala saboda yaki, takunkumai na saka shinge ga samar da kayan agajin jin kai ga 'yan ba ruwana da rikicin ya rutsa da su.

Takunkumai sun bazu da yaduwa a sannan duniya ta yadda alakarsu da sauran al'amuran duniya take da wuyar sha'ani.

Wadannan tuhume-tuhume na gabatar da gaskiya mai daci cewar rashin nasarar takunkuman da wahala na da illa ga manufofin Amurka a kasashen waje, suna lalata matsayinta d akarfinta a duniya.

Amfani da takunkuman da ya wuce ka'ida ya bayar da gudunmowa ga rarrabuwar kai a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Kazalika, takunkumai sun bazu da yaduwa a sannan duniya ta yadda alakarsu da sauran al'amuran duniya take da wuyar sha'ani.

Mafita

Domin ganin shugaban kasar Amurka da majalisar dokokin da za su zo a nan gaba don gyara wannan illa ta takunkumai da ba su da tasiri, ina da shawarwari guda uku.

Na farko shi ne a samar da wata hukuma mai zaman kanta da za ta yi nazari kan dukkan gwamnati d arawa da manufofin takunkuman ga manufofin Amurka a kasashen waje.

Amurka ta bi sahun Ireland wajen jagorantar Hukuncin kwamitin Tsaro na Mjaalisar Duniya mai lamba 2664 a watan Disamban 2022, wanda ya kirkiri rikicin jin kai ga kasashen da MDD ta saka wa kadarorinsu takunkumai, ko gwamnatocin da aka rike kudadensu.

Wadannan ayyuka na ci gaba, musamman matakin Kwamitin Tsaro na MDD mai lamba 2664, na samar da sabbin damarmaki ga shugabancin Amurka a fagen tattalin arziki.

Shawara ta uku ita ce shugabanni su nuna muhimmanci sosai ga alaka Amurka da kasashen da aka saka wa takunkuman tun daga lokacin da aka saka takunkuman.

Ci gaba mayar da wata kasa saniyar ware a matsayin ukuba na saba wa takunkumai, saboda yadda tattaunawa ke kawo sauyin siyasa, amma kuma hakan ya ta'allaka ga yadda aka yi ta, kamar yadda aka gani al'amura da yawa da ke faruwa.

A lokacinda ake mu'amalar diplomasiyya a yanayin da aka saka takunkumi, abinda zai faru shi ne Amurka ta yi alkawarin sassauta takunkumin don a biya mata bukatarta, idan har ma kasar da aka saka wa takunkumin ba ta amince cewar an yi galabata a kanta ba.

Tun da Amurka ce ta ke rike ds dukkan dama a irin wannan tataunawa ta sulhu, za a iya samar da yanayin sassauci da yakana a matsayin misalin fata mai kyau da zai sanya kasar da ake tattaunawar da ita ta ci gaba da tattaunawar.

Tsammanin sauyi

Haka kuma, dole Amurka ta sauya abubuwan da take tsammanin faruwarsu don yin nasara a irin wannan diplomasiyya.

Wajen da za a iya fara wa da shi shi ne maye gurbin tsarin da ake kai wanda ke janyo takunkumai su zama tushen ruguza alakar diplomasiyya.

Wannan na fara wa da tattaunawar masu shiga tsakani da shugabannin kasa da suka yi watsi da gaskiyar da suke yawna ji a cikin gida. An sha jin irin wadannan abubuwa daga majalisar dokokin Amurka kuma an sha tsare masu shiga tsakani a rikicin da ake yi a Amurka.

Wani kalami na bai daya da shugabannin gwamnatoci ke yi shi ne cewa a zauna a tattauna kan laifukan daya kasar na taimaka wa mummunar halayyar kasar da ake zargi da laifi.

Daukar sabbin matakan takunkumai na bukatar matukar mayar da hankali da kwarin gwiwa.

Amma a yayin hakan, Amurka na iya magance takunkuman da ke bayar da kunya irin su Cuba da yankunan Siriya da aka kubutar, da kuma sauran matakan kawo karshen takunkuman d aake ganin ba za su kawo karshe ba.

TRT World