Bala'in jinƙai da ake ciki a Lebanon yana ƙaruwa da gaggawa a kowace rana.
A cikin makonni biyu da suka gabata, hare-haren bam da Isra'ila ta kai, ya raba kusan mutum miliyan 1.2 da gidajensu, tare da tilasta wa sama da mutum 175,000 tserewa zuwa maƙwabciyarta Syria.
Akwai yiyuwar adadin zai ƙaru yayin da Isra'ila ke ƙara kai farmaki a kudancin Lebanon, lamarin da ya sa Firaminista Najib Mikati na riƙon ƙwarya ya yi gargadin cewa zai iya zama "ɗaya daga cikin lokuta mafi hadari" a tarihin kasar.
Rikicin ya afku ne a wani muhimmin lokaci. Tuni Lebanon ta fuskanci gurguncewar tattalin arziki kuma talauci ya ninka fiye da sau uku cikin shekaru goma da suka gabata.
Ko da yake Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani rahoton gaggawa na jinƙai na dala miliyan 426, ana ci gaba da yin tashin gwauron zabi na sake gina kasar.
Yayin da Isra'ila ke fadada yakin da take yi na kai hare-hare ta sama, akalla 'yan kasar 115,000 ne ke samun mafaka a matsugunan gwamnati. A yayin da ake fargabar tsawaita gudun hijira na ƙaruwa, shin Lebanon za ta iya jure wa rikicin jinƙai? Kuma shin Gabas ta Tsakiya za ta iya ba da ita?
Akwai dalilai da yawa da ya sa duniya ke buƙatar shiga tsakani kuma ta dakatar da sabon rikicin ƙaura daga yaɗuwa.
Matsalar lafiya da abinci
Lebanon na fuskantar hanya mai wahala a gaba don shawo kan rikicin ƙaura.
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa na kawo gurguntaccen tsarin kiwon lafiya na Lebanon cikin tsananin damuwa.
Akwai matukar bukatar daukar sabbin yara sama da 300,000 da suka rasa matsugunansu yayin da Isra'ila ke kai hare-hare kan rufe cibiyoyin kiwon lafiya da dama.
Rikicin zai shafi Turai ma. Akwai yiwuwar sake rufe kan iyakar Lebanon da Syriakamar yadda aka yi a shekarar 2015, lokacin da aka tilasta wa mutane kusan miliyan guda tserewa daga yakin Syria zuwa nahiyar.
Hare-haren na Isra'ila sun riga sun sa sansanonin 'yan gudun hijira na Labanon sun fara cika taf, kuma yanayin ya zama mai wahala wajen neman mafaka a maƙwabciyarta Syria. Wannan lamari na iya wargaza manufofin ƙaura masu "tsauri" na Turai tare da ƙara yawan 'yan gudun hijira da za su dinga bi ta hanyar teku mai haɗari.
Yawancin yara da iyalai sun dogara ne da irin wannan damar ta ƙaura don samun abinci mai gina jiki da tallafin kariyar yara.
Amma yayin da aka tilasta musu yin mafaka a matsugunan da ba su da wadata, hukumomin agaji na kasa da kasa na fuskantar wani aiki mai tsanani na miƙa taimakon lafiya ga wadanda ke wajen asibitoci.
Ko da a ce akwai cibiyoyin kiwon lafiyar da lamarin bai shafa ba, to tuni yawan 'yan gudun hijirar Syria miliyan 1.5 ya gajiyar da tsarin, kuma hare-haren Isra'ila kan ma'aikatan kiwon lafiya yana kawo cikas ga masu ba da agajin farko wajen ba da fifiko ga sabbin 'yan gudun hijira.
A ɓangaren samar da abinci kuwa, ƙalubalen kasar Lebanon na ƙaruwa. Sabbin mutanen da suka rasa matsugunansu na ƙara matsin lamba kan matsalolin samar da abinci a ƙasar, kuma abincin da aka tanada na tsawon watanni uku zai ƙare nan ba da jimawa ba.
Ko da yake Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (UFP) ta yi alkawarin samar da agajin gaggawa na dala miliyan 105, amma akwai alamun ba za su isa ba.
Misali, da wuya taimakon ya samu kafin karshen shekara, wanda hakan ya sa UFP da ƙawayenta ke buƙatar su ƙara ƙaimi yayin da Isra’ila ke ƙara sa dubban mutane yin hijira saboda hare-harenta.
Hare-haren da Isra'ila ke kai wa a kudancin ƙasar zai iya sa samar da abinci ya yi wahalar isa ga dukkan garuruwa da ƙauyukan da ke fama da rikicin.
Idan ba a tabbatar da kai kayayyakin da ake buƙata zuwa yankunan tsakiya da arewacin Lebanon ba, matsananciyar yunwa na iya ruruwa ta shafi sama da adadin mutum miliyan 1.1 da take shafa a wannan shekara.
Domin kawo ƙarshen bala'in jinƙai, dole ne Turai da manyan yankuna su yi amfani da ƙarfinsu na tattalin arziki da diflomasiyya a kan Isra'ila.
Ba a shirya wa kwararar 'yan gudun hijira ba
Ka yi la'akari da Siriya. Tuni dai ta fuskanci matsalar ‘yan gudun hijira mafi girma a duniya kuma sama da ‘yan Syria miliyan 7 ne suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin da aka kwashe shekaru ana yi.
Yayin da akasarin al'ummarta ba su da tallafin jinƙai, ta yaya dubban sabbin iyalai da suka rasa matsugunansu za su nemi mafaka daga maƙwabciyarta Lebanon?
Don haka, rikicin kan iyaka da ya kunno kai yana barazana ga zaman lafiyar kasar ta Lebanon. Bayan haka, akwai babban rashin jin daɗin jama'a ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta Labanon, wadda ta yi ƙoƙarin magance matsalar tattalin arzikin ƙasar ko kuma sanya ƙasar cikin matsanancin talauci.
Yanzu yayin da dubban 'yan Lebanon da suka rasa matsugunansu ba su da tabbacin ko za su samu lamunin komawa gidajensu, gwamnati na fuskantar barazanar raguwar farin jini tare da ba da kyakkyawan fata na tallafin sake ginuwa.
"Tserewa daga Kwarin Bekaa a gabashin Lebanon "yana ɗaya daga cikin mafi wahalar shawarar da na taɓa yankewa a rayuwata," Hanan 'yar shekara 33 ta shaida wa Hukumar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya a ƙarshen Satumba.
"Ina rayuwa a kullum cikin fargabar cewa za a ruguje gidana, kuma ina damuwa da 'yan'uwana da suke can."
Hakurin ƙasashen yankin yana ta ƙarewa shi ma. Tallafi ga 'yan gudun hijira ya ci gaba da raguwa a Gabas ta Tsakiya saboda ƙaruwar gajiyawa tare da tsawaita gudun hijira.
Yawancin ƙasashen Larabawa kuma ba sa son rage yawan 'yan gudun hijirar Lebanon da ke tsere wa yaƙin.
Hukumomin ba da agaji na kasa da kasa kuma suna ba da kyakkyawan fata yayin da suke fafutukar fuskantar gudun hijira a lokaci guda a Syria da Gaza. Idan babu isasshen tsari na samar da sauƙi, akwai haɗarin gaske cewa iyalai za su iya ƙoƙarin neman mafaka har zuwa Turai.
A cewar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sabbin masu neman mafaka za su iya yin la'akari da wannan zabin, yana mai jaddada yawaitar bala'in gudun hijira a yankin.
Yin abin da ya dace a kan lokaci don kawar da tashin hankalin na iya taimakawa wajen daƙile wannan bala'in, kuma dole ne Turai ta tsaurara matsayinta game da Isra'ila don samun nasara.
Darussan da aka koya daga yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza sun nuna cewa Tel Aviv ka iya ƙara rura wutar rikicin ƙaura a Lebanon.
A cikin shekarar da ta gabata, Isra'ila ta tilasta kwashe mutane da dama a Gaza, inda ta raba kusan ɗaukacin mutum miliyan biyu da yankin.
Sake korar mutane da Isra'ila ta yi a yankin Khan Younis na Gaza a watan Yuli wata hujja ce: umarnin ya share fagen sake kai farmakin da ke barazana ga kariya ga kusan mazauna yankin 250,000.
A halin yanzu da alama ana samun irin wannan yunkuri a Lebanon. Tsawaita odar ficewa daga kudancin Lebanon na ba da damar kai hare-haren da za su iya haifar da sabbin yanayin gudun hijira a duk lokacin da aka uzzura.
Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan cibiyoyin kiwon lafiya sun jawo tarnaƙi ga samun hanyoyin tserewa da kuma ma'aikatan agaji, inda hakan tuni ya hana kai agajin gaggawa ga al'ummar da abin ya shafa a Lebanon, lamarin da ya sa da wuya a magance rikicin ƙaura da ya faru a baya cikin dabara.
A ƙarshe, hare-hare masu zafi da ƙarancin tallafin yanki da gurgunta tsarin kiwon lafiya sun taɓarɓarar da zaɓin da Lebanon ke da shi don fuskantar wannan rikicin da ba a taɓa gani ba.
Marubucin Hannan Hussain marubuci ne kuma babban ƙwararre ne a cibiyar bincike ta Initiate Futures, da ke Islamabad. Shi masanin Fulbright ne na tsaro na kasa da kasa a Jami'ar Maryland, kuma ya tuntubi Cibiyar Sabbin Layukan Dabaru da Manufofi a Washington. An sha wallafa ayyukan Hussaini a cibiyar Carnegie Endowment for International Peace, Georgetown Journal of International Affairs, da Express Tribune (abokiyar hulɗar International New York Times).