Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Masoud Pezeshkian ya gabatar da jawabi bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a gaban majalisa a birnin Tehran na Iran a ranar Talata, 30 ga watan Yuli. / Hoto: AP Archive

Daga Ata Şahit

A ranar 11 ga watan Agusta, sabon zaɓaɓɓen shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya gabatar da sunayen mutanen da yake so a ba ministoci a gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman ƙuri'ar amincewa.

Dangane da dokar Iran, kakakin majalisar ƙasar zai karanta takardar gabatarwa ta shugaban ƙasar, inda bayan haka sai sauran takardu su biyo baya waɗanda za a miƙa su ga kwamitocin da suka dace domin dubawa.

Waɗannan kwamitocin an kafa su ne domin tantance cancanta da takardu da asali da kuma shawarar bayar da ma'aikatar da ta dace ga kowane minista tare da gabatar da bincikensu ga kakakin majalisa. Haka kuma za a buga takardun wannan rahoto tare da miƙa su ga duka mambobin majalisa domin bitarsu.

Mako ɗaya bayan gabatarwar ta gwamnati, za a yi zama daban-daban a majalisa domin tafka muhawara dangane da tsare-tsare da shirye-shirye na gwamnati tare da gudanar da ƙuri'ar amincewa dangane da ministocin.

A cikin wannan lokacin, ministocin da aka zaɓe su za su aika da shirye-shiryensu ga kwamitocin da suka dace da kuma mayar da martani dangane da duk wata buƙata daga mambobin kwamitin.

Matakin dai zai kai ga samun kuri'un amincewa da kowane minista, sannan kuma za a kada kuri'ar amincewa ga daukacin majalisar ministocin kasar.

Majalisar ministocin da Pezeshkian ke son kafawa

Gabatar da sunayen ministoci da shugaban ya yi ya jawo zazzafar muhawara a kafofin watsa labarai na Iran, inda akasarinsu suke mayar da hankali dangane ko yanayin waɗanda aka zaɓa a ministoci ya zo daidai da alƙawarin da Pezeshkian ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe dangane da irin mutanen da zai yi aiki da su.

Musamman ma, matsakaitan shekarun mambobin majalisar ministocin ya kai kusan shekara 60. Mace daya ce kawai aka zaba, kuma majalisar ministocin kasar mai rinjayen ‘yan Shi’a ba ta da wakilcin ‘yan Sunna.

Idan aka yi la'akari da manyan kalaman da ya rinƙa yi dangane da sauyi, da alama majalisar ministocin da ake son kafawa ta yi kama da mai matsakaicin ra'ayi, ta karkata ga ra'ayin mazan jiya maimakon wacce aka yi alkawarin kawo sauyi.

Hakan ya jawo caccaka daga masu ra'ayin kawo sauyi na ƙasar, inda Iranian Reform Front ta aika da wasiƙa ta caccaka ga Pezeshkian. "A matakin da aka bi na kafa sabuwar gwamnati, a tabbatar cewa hanyoyi marasa kyau ba su kai ga cire mutane masu basira ba da kuma sakawa jama'a sun yanke ƙauna daga matakin da suka ɗauka na zaɓenka," in ji wasiƙar.

Azar Mansoori, wadda ita ce shugabar ƙungiyar ita ma ta bayyana ra'ayinta a shafinta na X, inda ta ce, "Akwai buƙatar wannan majalisar ta ministoci ta zama wata alama ta sauyi, ba wai ci gaba da abin da ake yi ba."

Adawa da aka yi da zaɓen ministocin da Pezeshkian ba a ƙungiyar Reform Front kawai ta tsaya ba, shi ma tsohon ministan harkokin waje Mohammad Javad Zarif ya yi murabus, wanda Pezeshkian ya naɗa a matsayin mataimakin shugaban tsare-tsare.

Duk da cewa ci gaban da ake samu a yanzu na nuni da irin ƙalubalen da Pezeshkian ke ƙara samu dangane da sunayen ministocin da ya gabatar a ƙarƙashin mulkinsa, masu matsakaicin ra'ayi da masu ra'ayin mazan jiya na gwamnatinsa ba abin mamaki ba ne a gare su.

A wata tattaunawa ta baya-bayan nan, Pezeshkian ya bayyana cewa ministocinsa za su ƙunshi mutanen da Jagoran Addini ya amince da su.

Wani bincike da aka yi kan yanayin siyasar cikin gida ta Iran ya nuna cewa, kalubalen farko da gwamnatin Pezeshkian ke fuskanta, sun hada da rashin jituwa tsakanin gwamnati da al'umma, da batutuwan da suka shafi halacci, matsalar ruwa da muhalli, karancin makamashi, da kuma matsalolin hijira.

Daga cikin wadannan, ana iya cewa batun halaccin shi ne ya fi daukar hankali.

Idan aka yi la’akari da alakar da ke tsakanin gwamnati da al’umma a Iran za a ga cewa wannan tazarar ta kai matsayi mafi girma a tarihin jamhuriyar.

Wannan ya ƙara fitowa fili a raguwar da aka samu ta fitowar masu zaɓe.

Matsalolin manufofin ƙasashen waje

Daga cikin manyan matsalolin da ya zama dole Iran ta magance a manufofinta na ƙasashen waje shi ne yadda ake mayar da ita saniyar-ware a harkokin ƙasa da ƙasa. A yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Iran, Pezeshkian ma ya faɗi hakan.

“Babban abin da ke jagorantar aƙidar manufofinmu na ƙasashen waje shi ne kare muradun al’ummar ƙasar Iran.

“Manufar tsare-tsarenmu na ƙasashen waje ba wai kawai mu rayu ba ne; muna so ne mu cimma dalilin da suka sa muka zo duniya da yin rayuwa mai amfani, ta hanyar samar da damarmaki don bunƙasar al’ummarmu. Ba ma so mu ci gaba da kasancewa saniyar-ware a duniya.”

A taƙaice, Pezeshkian ya sha alwashin bibiyar manufar ƙasashen waje da ta yi daidai da abin da aka saba da shi a duniya. Ware Iran da ƙasashen duniya ke yi na wakiltar wani muhimmin batu da ke tasiri kai tsaye a siyasar cikin gidan ƙasar.

Wannan matsalar dai ta samo asali ne daga takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata. Don haka, da wuya Iran ta cimma wani gagarumin ci gaba, matukar ba a warware batun wadannan takunkumin na Amurka ba.

Wani bincike da aka yi kan manufofin harkokin wajen Iran cikin shekaru 20 da suka gabata ya nuna cewa batun takunkumin ya kasance babban abin da aka fi maida hankali a kai.

Babban dalilin wannan takunkumi shi ne damuwar da kasashen duniya suka nuna dangane da shirin nukiliyar Iran.

Da yawa daga cikin malaman na Iran suna ganin cewa rashin magance wannan lamari da kuma takunkumin da ake ci gaba da yi shi ne babban cikas ga ci gaban kasar.

Sun yi iƙirarin cewa wannan lamari ya zarce tasirin tattalin arzikin, wanda ya shafi yanayin siyasar cikin gida na Iran da kuma yanayin tsaro na yankin.

Tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar Sayyed Abbas Araghchi, wanda Pezeshkian ya gabatar masa a matsayin ministan harkokin wajen kasar, ya shahara wajen jajircewarsa ta tattaunawa da kasashen duniya da kuma goyon bayansa mai ƙarfi ga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015, wadda tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi watsi da shi bai daya.

A mahangar Araghchi, rashin mutunta yarjejeniyoyin kudi da ka'idojin kudi na duniya suna kawo cikas ga kasancewarta a fagen tattalin arzikin duniya a zamanin da ke da alaka da tsarin duniya inda ka'idojin kasa da kasa ke matukar tasiri kan ayyuka da manufofin kasa.

Don haka wajibi ne Iran ta magance wannan batu ta hanyar tattaunawa. Araghchi yana ɗaya daga cikin ƴan mutane kaɗan da ke da ikon farawa da kuma cimma nasarar kammala irin wannan tattaunawa.

Ya samu karbuwa a wajen masu sassaucin ra'ayi kuma ya samu amincewar Jagoran Addini na Iran.

Lallai, nadin Araghchi a matsayin ministan harkokin waje na nuni da aniyar Iran zuwa ga samun aƙall matsakaicin manufofin kasashen waje.

Shin Araghchi zai iya yin nasara a inda wasu suka gaza? Wannan ita ce muhimmiyar tambayar miliyoyin daloli da Iran ke neman gina makomarta a karkashin sabon shugaban.

Ata Şahit babban mai gabatar da shirye-shirye ne a TRT.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayoyin marubucin su kasance daidai da ra'ayoyi da manufofin edita na TRT Afrika.

TRT World