Alakar Koriya ta Arewa da Iran ta zama babbar damuwa ga gwamnatocin kasashen Yamma. Shugabanni a Amurka da Turai na kallon alakar soji tsakanin Pyongyang da Tehran a matsayin barazana ga manufofinsu na siyasa a yankunan da kasashen biyu suke.
Bayan wata ziyara da wakilan Koriya ta Arewa suka kai Tehran, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce Washington "za ta yi amfani da duk wasu hanyoyi ciki har da saka takunkumai don ƙalubalantar wannan alaƙa."
Hadin kan Iran da Koriya ta Arewa ya fi ta'allaka ne kan muhimman manufofin kare kasashe da ikon yanke hukuncinsu, musamman kan tsaron kasa. Tsawon shekaru da dama, Koriya ta Arewa da Iran sun haɓaka ƙawancen musaya da kasuwanci.
Fahimtar wannan alaƙa ta kasashe biyu na mayar da mu ga Waki'ar Iran da Iraki (1980-1988). Tehran sun nemi ƙawaye a duk inda suke a duniya a lokacin mummunan yakin.
Koriya ta Arewa ta kafa kanta a matsayin mai samar da makamai ga Iran, a yayin da kasashen Larabawa da na Yamma da dama ke goyon bayan Baghdad.
Pyongyang na samar da makamai masu linzami samfurin SCUD B ga Iran da bayar da horo da shawarwarin ayyukan soji, kuma Koriya ta Arewa na daya daga cikin 'yan tsirarun kasashen duniya da suka taimaka wa Iran kai tsaye a lokacin yakin.
A 1989, shugaban kasar Iran na wannan lokacin (Shugaban Addinin Iran a yanzu) Ali Khamenei ya ziyarci Koriya ta Arewa inda ya kuma ce "idan manyan kasashe suka yi barazana ga kasashe masu tasowa, to su ma kasashe masu tasowar su yi musu barazana...A Koriya kun tabbatar da kuna da ƙarfin tunkarar Amurka."
Alaƙa da ta fi karkata ga makamai masu linzami
Tun bayan kawo karshen Yakin Iran da Iraki, kasashen biyu sun ci gaba da alaƙarsu mafi yawanci game da makami mai linzami. Koriya ta Arewa ta taimaki 'yan kasar Iran wajen haɓaka manyan makamai masu linzami ita kuma Tehran ta taimaki Pyongyang da makaman roka.
A baya, kasashen biyu sun hada kai wajen samar da jiragen ruwa na karkashin teku da na sarari, yayin da kuma suke musayar dabarun kauce wa radadin takunkuman Ƙasashen Yamma, da kuma tattauna yadda za su kai albarkatun mai na Iran zuwa Koriya ta Arewa ta hanyar amfani da China.
Koriya ta Arewa da Iran na daga cikin kasashe kaɗan da suka bayar da taimakon soji kai tsaye ga Rasha a yakin da take yi a yanzu haka da Ukraine.
"Kawancen na bisa doron neman mafita - duk kasashen na fuskantar takunkumai manya kuma an toshe su daga samun fasahar kere-kere daga wasu wuraren - sai dai kawai tsagwaron akida tunda Iran n riko da addini, ita kuma Koriya ta Arewa na adawa da addini,'' in ji John Feffer, daraktan mujallar 'Foreign Policy in Focus', yayin tattaunawa da TRT World.
"Kasashen biyu sun hade waje guda wajen zargin Yammacin Duniya, duk da cewa kashi mai yawa na jama'ar Iran na goyon bayan Ƙasashen Yamma a wasu fannoni.
Idan aka kalli bambancin da ke tsakanin kasashen biyu, rashin kawance ta fuskar akida, da nisan da ke tsakaninsu, hadin kan sojinsu ba ya saka wata babbar barazana ga Amurka da Yammacin Duniya, duk da dai batun sarrafa nukiliya, ciki har da na makamai masu linzami da ke iya zuwa kowacce nahiya, na iya sauya wannan ma'auni," in ji Feffer.
Kenneth Katzman, babban jami'i a Cibiyar Soufan ya fada wa TRT World cewa karuwar hadin kan soji tsakanin Koriya ta Arewa da Iran na iya kalubalantar manufofin Yammacin Duniya saboda ƙwarewar Pyongyang kan makamai masu linzami masu cin dogon zango, da kuma yiwuwar Tehran ta yi amfani da fasahar Koriya ta Arewa wajen habaka nata makamai masu linzamin ta hanyar da za ta sanya damuwa a zukatan gwamnatocin Yammacin duniya.
"Wata barazana ce a nan gaba saboda Koriya ta Arewa na da ƙwarewa kan samar da makamai masu linzami masu cin dogon zango. Iran ta bayyana cewar za ta dakata ga iyakacin mai nisan kilomita 2,000, wanda ya tattara yankinta amma ba zai wuce nan ba.
Amma Koriya ta Arewa ta bayyana ƙarara a yayin gwajin makamai masi linzami da yin dogon zango, manyan roka da ma masu bakin nukiliya. Hakan ya sa ake da tsoron wannan hadin kai zai taimaka wa Iran damar habaka nata kokarin," in ji Katzman.
Bambancin manufofin ƙasashen waje na Amurka da Rasha
Shugabancin Iran ya yi sauye-sauye saboda tabarbarewar alakarsu da Amurka da Tarayyar Turai tun da Washington ta yi zagon kasa ga Shirin Fahimtar Juna na Hadin Gwiwa(da aka fi sani da shirin nukiliyar Iran) shekaru shida da suka wuce kuma ta kakaba takunkumai masu tsauri a kan Iran.
Domin baude wa matsin lambar Yammacin Duniya, Iran ta koma ga "Kallon Gabas". Koriya ta Arewa ta zama daya daga cikin cibiyoyin cimma manufofin harkokin waje na Jumhuriyar ta Musulunci.
Mehran Kamrava, farfesa kan GWamnati a Jami'ar Georgetown d ake Qatar ya shaida wa TRT World cewa "A bayyana take karara muna kallon yadda rukunin kasashe ke hade wa - sun hada da Iran, China, Rasha da Jumhuriyar Koriya ta Arewa - wadanda manufofinsu suka ci karo da na Amurka da kawayenta.
"Sai dai kuma ana ganin wannan ba kalubale ba ne da za a yi watsi da shi cikin sauki ba."
Kamar yadda Feffer ke gani, makomar alakar Koriya ta Arewa da Iran za ta zama ta ta'allaka kan gogayyar kasashe da kuma motsin da Rasha ke yi a matakin kasa da kasa a lokacin da Cremlin ke neman hade kan karin kasashe a kawancen kasashen d ake adawa da Yammacin duniya da suka hada da Pyongyang da Tehran.
"Nasara a Ukraine, sai dai kuma Rasha na bayyana 'nasara' za ta baiwa wannan kawance damar habaka, wanda ke nufin babban hadin kai tsakanin Iran da Koriya ta Arewa a babban fage.
"Amma zai yiwu tare da dabarun diflomasiyya, Turai da Amurka na iya sake jan ra'ayin Iran ta yi mu'amala da Yammacin Duniya. Dawowar shugabanci mai son kawo sauyi, shugabancin ma sai ya canja.
"Amma tabbas dawowar Donald Trump zuwa Fadar White House zai sake kusantar da Iran. Koriya ta Arewa da Rasha ga juna," in ji Feffer.
Duba ga yadda hadin kai da ƙawancen suke, babu wata hanya na sanin tabbacin meye a cikin kundin alakar Koriya ta Arewa da Iran. Amma kuma kamar babu wata matsala idan aka ce sakamakon takunkuman da aka saka wa Pyongyang da Tehran zai sanya kasashen su ci gaba da zama tare.
A karkashin wadannan yanayi, shugabannin Koriya ta Arewa da Iran za su ci gaba da kallon wannan alaka a matsayin mai amfani ga manufofinsu.
"Ina tunanin matukar dukkan biyun suka ci gaba da kasance wa a karkashin takunkuman Amurka, Iran da Koriya ta Arewa za su ci gaba da hadin kai da tallafar juna.
"Koriya ta Arewa na bukatar mai da abinci, kuma Iran na bukatar fasahar kayan tsaro da ayyukan soji. Dukka biyun na iya amfana daga kwarewar dayan ta bangarori daban-daban," in ji Dr. Sina Azodi, farfesa kan Alakar Kasa da Kasa a Jami'ar Elliott, a wata tattaunawa da ya yi da TRT World.
Darussan da aka koya daga harin ramu wa da Iran ta kai wa Isra'ila
Kwararru sun yarda cewa Koriya ta Arewa ta yi zugum tare da sanya idanu sosai a ranakun 13 da 14 ga watan Afrilu lokacin da Iran ta kai harin ramuwa kan Isra'ila, sakamakon hari da Isra'ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran a birnin Sham kwanaki 12 kafin haka.
A yayin da Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami d ajirage marasa matuka a kan iyakar Isra'ila, inda Isra'ila d ataimakon Amurka, Birtaniya, Faransa da Jordan - suka lalata mafi yawan su tun suna sama.
A ra'ayin Feffer, an rawaito Pyongyang ta yi amfani da harin ramuwa na Iran wajen gwajin makamanta masu linzami don auna yadda suke tunkarar garkuwar makamai masu linzami, watakila da manufar kai irin wannan hari kan Koriya ta Kudu."
Nazarin nasa na shi ne idan aka yi duba ga yadda ra'ayin Koriya ta Arewa kan maƙwabciyarta ta Kudu ke kara munana da yadda Pyongyang ke watsi da duk wani yunkuri na samar da zaman lafiya da hade wa da juna, akwai yiwuwar Koriya ta Arewa na iya daukar wannan mummunan mataki.