Sakamakon wannan kokari na diflomasiyya, Iran a bara ta samu zama cikakkiyar mamba a kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) tare da shiga kungiyar BRICS. / Photo : AP

Mutuwar shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian sakamakon hatsarin helokwafta ya haifar da tambayoyi dangane da makomar manufofin ƙasashen waje na Iran a nan gaba da kuma takun saƙar diflomasiyya da ka iya tasowa.

A cikin kasa da shekaru uku a kan karagar mulki, Raisi ya ba da fifiko wajen raya manufofin ƙasashen waje na Iran dangane da dangantakar siyasa da tattalin arziki da kasashen da ba na Yammacin Turai ba, don rage matsin tattalin arzikin da Amurka ta ƙaƙaba wa Iran.

Don haka, gwamnatin Raisi ta bi sahun manufofin ƙasashen waje tare da farfado da manufarta ta ‘Look to the East’ wato 'Fuskantar Gabas', da kyautata huldar da ke tsakaninta da Rasha da Sin, tare da gudanar da ziyarar aiki a kasashen Latin Amurka da Afirka.

Sakamakon wannan kokari na diflomasiyya, Iran a bara ta samu zama cikakkiyar mamba a kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) tare da shiga kungiyar BRICS.

Bugu da ƙari, gwamnatin Raisi ta inganta dangantakar Iran da kasar Rasha sosai, musamman ta fuskar hadin gwiwa da goyon bayan soja, musamman ta hanyar samar da jiragen sama marasa matuka na Shahed a lokacin da ake ci gaba da rikici a Ukraine.

Dangane da siyasar yankin, Iran a shekarar 2023 ta samu ci gaba sosai wajen samun kusanci da Saudiyya ta hanyar shiga tsakanin da China ta yi.

Har ila yau, huldar diflomasiyyarta ta dangana da kasar Masar, inda aka dinga ganawa tsakanin jami'an Iran da shugaban Masar Abdel Fattah El Sisi. Wadannan yunƙurin sun wakilci dabarun sake kafawa da ƙarfafa tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya.

Duk da yake Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei da Rundunar IRGC ne suke da karfin iko a kan tsarin harkokin wajen kasar, rashin tsohon Ministan Harkokin Waje, Abdollahian zai fi shafar kasar a kan rashin Raisi.

Dan yake bayyana marigayin, dan majalisa mai raayin rikau, Ali Alizadeh ya bayyana shi da, Soleimanin difolomasiyya. Marigayin yana da goyon bayan runduna ta Islamic Revolutionary Guards Corps wato IRGC.

A lokacin da yankin Larabawa ke fama da rikice-rikice, shi ne ya shige gaba wajen kara karfin ikon Iran a yankin na Gabas ta Tsakiya. Idan aka kwatanta shi da wanda ya gada, Javad Zarif, zamanin Abdollahian ya fi mayar da hankali wajen alakar Iran da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Nada wani sabon Ministan Harkokin Waje mai kwarewa da sanin makamar aiki irin Abdollahian zai taimaka wa Iran wajen cigaban da take samun a bangaren diflomasiyya, musamman yunkurin gyara alakar kasar da Saudiyya da Masar.

Me ake zato?

Ana tunanin rasuwar Raisi da Abdollahian zai iya tasiri a kan harkokin diflomasiyyar kasar a bangarori hudu.

Na farko, tallafin da Iran ke ba wa hadakar kasar da Syria da wasu kungiyoyin yankin, wanda ake tunanin na taimakon tsaron kasar, zai kasance kan gaba.

Daga cikin tallafin nan akwai goyon bayan Bashar Assad a Syria, da Hezbollah a Lebanon da Hamas a Falasdinu da Popular Mobilization Forces a Iraqi da Houthi a Yemen.

Na biyu, matsayar Iran a game da batun Falasdinawa da tallafawarta ga Hamas zai cigaba a sabuwar gwamnatin.

Na uku, ana hasashen tattalin arziki da alakar sojin Iran, musamman da Rasha da China zai habaka.

Na karshe, tattaunawar da ake yi na dawo da yarjejeniyar nukiliya ba ta sauya ba. Don haka sabuwar gwmanati za ta daura ne daga inda aka tsaya a kan batun na nukiliya, musamman ganin Babban Zaben Amurka na kusantowa.

Ana sa ran tasirin wadannan sauye-sauyen diflomasiyya zai kasance da bangarori biyu; Zai kunshi cigaba, da kuma yin gyare-gyare ga wasu tsare-tsaren alakar kasar da kasashen waje. A bangaren cigaba, karfafa alakar soji tsakanin kasar da sauran kungiyoyi yankin yana da matukar amfani.

Tsare-tsaren harkokin wajen Iran tun bayan juyin juya halin Larabawa na 2011, sun fi mayar da hankali kan tabbatar da tsaron kasarta-tsarin da zai yi wahala a kauce daga gare shi.

Dadin dadawa, kara tabbatar da alaka da kasashen Rasha da China zai matukar taimakon sabuwar gwamnatin.

Kafin hatsarin jirgin saman da ya yi ajalin Shugaban Kasar, babban nasarar diflomasiyya na karshe a zamanin mulkin Raisi shi ne a lokacin bude dam din Qiz Kalesi da ke kan iyakar Iran da Azabaijan.

Tun bayan yakin Karababk gwamnatin Iran take bayyana adawa da bude iyakar Zangezur, wanda ke ba da damar wucewa kai tsaye tsakanin Azerbaijan da Nakkchivan, inda ake iya ketare Iran da Armenia.

Bude dam din ya karfafa gwiwar kasashen biyu a kan cigaba da tattauna batun alakar diflomasiyya a tsakaninsu. Idan sabuwar gwamnatin ta daura daga inda Raisi ya tsaya a kan diflomasiyya, za ta iya karfafa alakar Iran da Azerbaijan.

A tsarin siyasar Iran, Khamenei ne yake da karfin iko a kan komai da ya shafi kasar, sai kuma Rundunar da ita ma take da karfi sosai.

Wannan tsarin ne ya sa Shugaban Kasa ba shi karfin iko sosai. Don haka, duk da zaben sabon Shugaban Kasa da nada sabon Ministan Harkokin Waje, asalin alhakin lura da harkokin wajen kasar yana rataya ne a kan Jagoran Addinin Kasar da Rundunar IRGC.

Marigayan guda biyu sun tsaya a tsaka-tsaki ne, inda ba su dauki irin salon ba sulhu irin na tsohon Shugaban Kasa Mahmoud Ahmadinejad ba, ko kuma irin salon sasanci da kasashen Yammacin duniya irin na tsohon Shugaban Kasa Hassan Rouhani da Ministan Harkokin Wajensa Javad Zarif.

Majalisar Shura ta kasar ce za ta tantance yan takara da za su shiga Zaben Shugaban Kasar mai zuwa, wanda za a yi a ranar 28 ga Yunin.

Ana hasashen cewa majalisar shurar za ta fi matsala lamba wajen tantance yan takarar fiye da zaben baya, inda ake hasashen masu raayin rikau ne za su fi yawa a takarar, wanda ake domin hakan zai taimaka wajen samun saukin sauyin shugabancin da cigaba da tsare-tsaren da kasar ta fara.

Sai dai tsohon Shugaban Kwamitin Hulda da Kasashen Waje na Harkokin Tsaron Kasar, Seyed Hossein Mousavian, ya yi hasashen abubuwa guda biyu da za su iya faruwa a zaben.

Na farko shi ne masu raayin rikau za su cigaba da rike mulkin, wanda hakan zai kara jawo rashin aminci tsakanin kasar da kasashen Yamma.

Na biyun kuma shi ne tunanin watakila masu dan sauki daga cikin masu raayin rikau ne za su samu mulki, wanda hakan ne zai saukaka rashin tunanin da kallon da ake wa kasar.

Bayan haka, wasu na tunanin cewa Rundunar IRGC za ta cigaba da nuna karfin ikonta a kan duk wasu abubuwa da suka shafi harkokin ciki da wajen kasar.

Sabon Shugaban Kasar zai yi tasiri sosai wajen sauya akalar siyasar Iran a kan batutuwa masu mahimmanci kamar shirin nukiliya, dangantaka da Isra'ila, da tattaunawa da Amurka.

Sai dai kuma wata matsalar ita ce laakari da yanayin tsarin harkokin wajen Iran, inda ake tunanin za ta cigaba da halinta na dogewarta a kan abu maimakon bude kofar sasanci zai iya cigaba.

Haka kuma Sabon Shugaban Kasar zai sha fama wajen bibiyar wadannan manufofin na kasar bisa tsarin da Jagoran Addinin Kasar da Rundunar IRGC suka tsara domin tabbatar da manufofin da aka tsara sun cigaba.

Kasashen duniya dai za su zura ido domin ganin yadda akalar sabuwar gwamnatin za ta juya a game da harkokin wajenta ne a daidai lokacin da take da fama da matsaloli a ciki da wajen kasar.

TRT Afrika