Zuba jari da ake yi a sabbin kamfanonin fasahar suna taimaka wajen ci gaban tattalin arziki. Hoto: Reuters      

Daga Yahya Habil

Ba abu ba ne boyayya cewa bunkasar sabbin kamfanonin fasaha yana tasiri a nahiyar Afirka a 'yan shekarun nan.

Hada da ci gaba da karuwar adadinsu, sabbin kamfanonin fasaha a Afirka suna sauya irin kallon da ake yi wa nahiyar da kuma canja tunanin mutane.

Abu mafi muhimmanci shi ne sun kasance suna taka muhimmiyar rawa kan ci gaban tattalin arzikin nahiyar, kamar yadda suka samar da ci gaba kan tattalin arzikin kasashe da dama, wanda hakan ya kara fito da batun yiwuwar tattalin arzikin nahiyar ya bunkasa sosai.

Jama'ar da ke nahiyar Afirka galibi matasa ne masu son harkokin kasuwanci. Kimanin kaso 60 cikin 100 na 'yan Afirka matasa ne 'yan kasa da shekara 25, wanda hakan ya sa nahiyar ta zama nahiyar da ta fi kowace yawan matasa a duniya.

Wannan ya sa ake ganin za a iya cin gajiyar adadin matasan da take da su wajen kirkire-kirkire da kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arzikin Afirka.

Yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale kamar rashin aikin yi da talauci, wasu kasashe suna amfani da basira da kuma karfin matasa don samar da ci gaba ga sauran kasashen nahiyar kuma gyara komadar tattalin arziki.

Sabbin kamfanonin fasaha na Afirka suna samar da ayyukan yi da kudin haraji da masu zuba jari, abin da ke samar da kwarin gwiwa a nahiyar.

Adadin ayyukan da kananan kamfanonin fasahar ke samar ya karu, abin da ke nuna yadda suke tasiri ga tattalin arzikin kasashen Afirka.

Sabbin kamfanonin fasahar suna karkata zuwa wasu kamfanoni a fannin makamashi da aikin gona da kiwon lafiya da sufuri wadanda suke taimakawa wajen bunkasar tattalin arziki.

Bangaren fasahar zamani na taimaka sosai ga tattalin arzikin Afirka. Hoto: Reuters

Kamfanonin suna samar da kudin shiga da kawo masu zuba jari wadanda abubuwa da za su kawo ci gaba da bunkasar tattalin arzikin Afirka.

Kasashen Afirka kamar Kenya da Rwanda da kuma Nijeriya su ne kan gaba wajen yawan kananan kamfanonin fasaha a nahiyar, kasashen suna kokarin mayar da kansu cibiyoyin kirkire-kirkire da kasuwanci.

Wadannan kasashe sun samu ci gaba ta fuskar aikace-aikacen kananan kamfanonin fasaha, inda wasu daga cikinsu suka samu zuba jari wanda hakan ya taimaka wajen fadada aikace-aikacen kamfanonin zuwa wasu kasashen Afirka.

Wadannan kudaden zuba jarin ba kawai suna wajen bunkasar jarin kamfanonin ba be, amma kuma suna taimaka wa wajen samar da kwararru da cudanya wadanda suke taimakawa wajen nasarar kamfanonin.

Kenya misali ta kasance daya daga cikin na gaba-gaba wajen samar da yanayin da ya dace ga sabbin kamfanonin fasaha.

Kasar ta ja hankalin kasashen duniya ne saboda saurin intanet dinta da yadda take kai wa ga kasuwar Afirka cikin sauki, hakan ya sa ta sama wani wuri da fi dacewa da sabbin kamfanonin fasaha.

Yanzu kasar tana da sabbin kamfanonin fasaha da ke cin moriyar albarkatun Afirka.

Misali wani kamfanin samar da makamashi daga hasken rana M-Kopa Solar yana samar da lantarki daga hasken rana na iya kudin ka, iya shagalinka ga mutane da ba sa kan layin wutar lantarkin kasar.

Kamfanin ya samu masu zuba jari daga ketare, inda wani kamfanin da ke karkashin Bankin Duniya, İnternational Finance Corporation (IFC) ya zuba jarin dala miliyan 50.

Wasu daga cikin sabbin kamfanonin fasaha a Afirka sun fi mayar da hankali kan samar da makamashi daga hasken rana. Hoto: AP

Wadannan kudaden sun taimaka wa kamfanin M-Kopa Solar fadada ayyukansa kuma ya kara samun kwastomomi a Kenya da sauran kasashen Afirka.

Wani misalin kuma shi ne kamfanin aikin gona na zamani na Twiga Foods a Kenya wanda yake sada manoma da masu sayan amfanin gona ta inatanet, inda kamfanin ya kawo sauyi kan yadda ake kai amfanin gonar kasuwa.

Kamfanin ya samu zuba jari daga ketare ciki har da dala miliyan 30 daga bankin masu zuba jari na Goldman Sachs.

Wadannan kudaden sun taimaka wa kamfanin Twiga Foods wajen fadada ayyukansa, taimaka wa manoma kai amfanin gonarsu kasuwa cikin sauki wanda hakan yake taimakon manoma da masu sayan amfanin gonar.

Hakazalika, Rwanda ta samar da yanayin da ya dace ga sabbin kamfanonin fasaha.

Kamfanonin suna cin moriyar taimakon da gwamnati kasar take ba harkokin kasuwanci da kuma inda Rwanda take, sabbin kamfanonin fasaha a Rwanda suna amfani da wadannan damarmaki wajen warware manyan matsaloli da kuma kirkiro wasu hanyoyin ci gaba a sauran fannoni.

Wannan haka yake hatta ga sauran sabbin lamfanoni kamar Zipline – wato wani kamfanin Rwanda wanda yake amfani da jirage marasa matuka wanda aika kayayyakin jinya da magunguna wanda kuma shi ne mafi girma da yake irin wannan aiki a fadin duniya.

Kamfanin ya samu zuba jari sosai daga ketare, ciki har da dala miliyan 190 daga kamfanin Baillie Gifford, wani kamfanin masu zuba jari na kasar Scotland da kuma kamfanin Temasek, wani kamfanin masu zuba jari na kasar Singapore.

Masana sun ce kirkire-kirkire na da muhimmanci wajen bunkasar sabbin kamfanonin fasaha. Hoto: AFP

Wadannan kudin zuba jarin sun taimaka wa kamfanin Zipline ya fadada aikace-aikacensa na raba kayan jinya da magunguna a fadin Rwanda da sauran kasashe, inda yake samar da muhimman kayan jinya da ake bukata a wurare da ke da nisa daga gari.

Kasha wani sabon kamfanin fasaha ne da ya karkata kan mata, wanda yake kokarin samar da daidaiton jinsi a Afirka. Yana samar da kafar kasuwanci ta intanet don kiwon lafiyar mata da kuma abubuwan kula da lafiyar kai.

Kamfanin ya samu zuba jari daga kasashen ketare, ciki har da kamfanin hada-hadar kudi na Finnland wato International Finance Corporation (IFC) and Finnfund.

Wadannan kudi sun taimaki kamfanin Kasha ya fadada ayyukansa da yadda ake gudanar da shi da kuma kai wa ga wasu karin mata da kayayyakinsa na kiwon lafiya da kula da kai.

Nijeriya tana sahun gaba ta fuskar tattalin arziki a Afirka kuma tana samar da yanayin da ya dace ga sabbin kamfanonin fasaha.

Yayin da yawan al'ummarta ke ci gaba da karuwa da wurin da kasar take zaune da yanayi mai karfafa gwiwar fasaha, sabbin kamfanonin fasaha a Nijeriya sun samu kudi daga masu zuba jari sosai.

Wani da ya fice a cikin kamfanonin shi ne kamfanin Andela wanda yake baje-kolin basirar da 'yan kasar matasa suke da ita.

Sabon kamfanin fasaha ne da ya kware wajen samar wa manyan kamfanonin fasaha na duniya kwararru daga Afirka wajen kirkirar manhaja.

Kamfanin ya samu dala miliyan 40 na masu zuba jari daga kamfanonin CRE Venture Capital da kuma DBL Partners.

Abin da ke bayar da kwarin gwiwa

Kudin zuba jarin ya taimaka wa kamfanin Andela wajen fadada ayyukansa da horas da masu kirkirar manhaja da kuma fadada ayyukansa har gaba da Nijeriya zuwa sauran kasashen Afirka.

Akwai kuma kamfanin Kobo360 wanda shi ma misali ne na yadda Afirka take amfani da basirarta wajen magance matsalolinta. Sabon kamfanin fasaha ne da ke hada 'yan kasuwa da kamfanonin jigilar kayayyaki.

Matasa da yawa a Afirka suna rungumar sabbin kamfanonin fasaha. Hoto: Reuters 

Kamfanin ya samu dala miliyan 30 na zuba jari daga kamfanin Goldman Sachs.

Kudin sun taimaka wajen fadada ayyukan Kobo360 da kuma bunkasa fasaharsa da kuma tabbatar da duga-dugansa a fanni jigila a kasashen Afirka.

Sabbin kamfanonin fasaha sun yi tasiri sosai kan ci gaban tattalin arzikin Afirka. Wadannan ayyuka za su yi tasiri kan makomar nahiyar, ko da yake nasarar ta dogara ne kan shawo kan manyan matsaloli da kuma samar da yanayin da ya dace don samun ci gaba.

Magance matsaloli kamar cin hanci da rashawa da tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki da inganta abubuwan more rayuwa hanyoyi ne na shawo kan matsalolin Afirka da kuma samar da bunkasar tattalin arziki.

Tasirin sabbin kamfanonin fasahar Afirka ya wuce gaban bunkasar tattalin arziki kawai; abubuwa ne masu karfafa gwiwa da samar kyakkyawan fata ga 'yan baya.

Bunkasar tattalin arziki da ci gaba da wadannan sabbin kamfanonin fasaha suka samar ga Afirka abubuwa ne da ke ishara ga kyakkyawan makoma da nahiyar za ta samu zuwa gaba.

Yahya Habil wani dan jarida ne dan kasar Libya wanda ya mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi Afirka. A halin yanzu yana aiki ne da wata cibiyar nazari a yankin Gabas ta Tsakiya.

A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.

TRT Afrika