An samu ci gaba a harkar podcast tsawon shekaru a Afirka. Hoto/Getty Images

By Muzhinga Kankinda

Tsarin podcast, wani nau’i ne na watsa labarai ta intanet wanda yake ba mutane damar rarraba sauti ko bidiyo ta intanet.

Podcast ya samo asali a farkon shekarun 2000, a lokacin da na’urorin tafi-da-gidanka suka soma zama ruwan dare, inda masu amfani da su ke sauke sauti ta intanet.

Kusan shekara 20, podcast na kara samun farin jini a fadin duniya. Haka kuma yana kara samun karbuwa a Afirka a matsayin wata hanya ta sadarwa.

Karuwar Podcast a Afirka za a iya danganta shi da abubuwa da dama da suka hada da karuwar wayoyin salula na zamani da kuma bazuwar intanet wadanda duk sun taka muhimmiyar rawa.

Haka kuma soyayyar da ‘yan nahiyar suke yi wa hanyar sadarwar ta taimaka wurin nasararta.

Suna son hanyar sakamakon tana ba su damar gina al’umma da samun karfi da hulda da juna a tsakanin masu sauraro.

Kamar yadda wani bincike da Africa Podfest ya yi, an shafe sama da shekara goma ana samar da podcast a fadin Afirka.

An samu matukar karuwa tsakanin 2017 zuwa 2023 inda Afirka ta Kudu da Nijeriya da Kenya suka fi zama wuraren da aka fi sauraren podcast din a nahiyar.

Samar da murya ga kowa

Podcast ya zama wani babban ginshiki na harkar watsa labaran Afirka inda yake bai wa masu fasaha ta Afirka dama da ‘yanci domin fadin ra’ayinsu ba tare da saka musu takunkumi ko kuma dakatarwa daga gwamnati ba. Sun kuma kara inganta aikin jarida na intanet.

Mai shirin Podcast Michael Baruti yana amfani da podcast domin watsa shirye-shirye kan lafiyar kwakwalwa a Tanzania. Hoto/Baruti

Kamar yadda wani rahoto na IJNet ya bayyana, podcast na taimakon masu dauko rahoto dakile labaran karya a dakunan watsa labaransu na intanet.

A gare su, podcast wata hanya ce mai muhimmanci da samar da ingantattun labarai.

A dayen bangaren, nazarin Africa Podfest ya nuna cewa a kasashe da dama da yankuna, podcast na kara bai wa marasa murya da wadanda aka ware su dama wadanda suka hada da mata da mutane masu bukata ta musamman da masu magana da harshen uwa.

Akwai masu saurare da dama da suka tabbatar da cewa podcast na taimakawa wurin fahimtar abubuwa da dama da suke damun Afirka da kuma bayar da dama ga ‘yan Afirkan su bayar da labaransu.

Haka kuma matasa wadanda ke birni su ma suna son tsarin domin a ganinsu ya zo daidai da abin da suke so da gwagwarmayar da suke yi.

Juriya

Podcast na fuskantar kalubale daban-daban a Afirka.

Tsadar intanet na sa ‘yan Afirka da dama rashin samun podcast musamman wadanda suka dogara kan wayoyinsu domin samun intanet.

Zuwan podcast ya kara fadada watsa labarai a Afrika. Hoto/AA

Bugu da kari, karancin kayayyakin aiki domin samar da ingantaccen sauti shi ma yana kawo cikas wurin habakar podcast.

Akwai mutane da dama da har yanzu ba su san me podcast ke nufi ba, wanda hakan ke nufin akwai masu yin podcast din da suke ta gwagwarmayar kara samun mabiya da kuma samun kudin shiga ta hanyar abubuwan da suke samarwa.

Sai dai masu podcast a Afirka na ta kokarin samun hanyoyi domin wayar da kai kan lamarin.

Misali, an rinka samun karuwar bukukuwan podcast na Afirka a kasashen Afirka da dama kamar Nijeriya da Masar haka kuma akwai ranar Podcast ta Afirka, wadda rana ce ta musamman da aka ware a kowace 12 ga watan Fabrairu domin murnar irin juriya da fasahar da masu podcast.

Haka kuma podcast na bayar da dama ga ‘yan Afirka masu fasaha da son sana’a.

Yawan matasa

Josephine Karianjah, wadda tana daya daga cikin wadanda suka kirkiro Podfest 2020, ta bayyana cewa akwai karuwa a yawan masu sha’awar podcast a Afirka.

Tun bayan nan, adadin masu podcast da kuma kungiyoyinsu ya karu, kuma bukukuwansu sun karu.

Duk da kalubalen da ake fuskanta, Karianjah na ganin “podcast na bayar da dama domin hadin gwiwa da nazari tsakanin ‘yan Afirka masu podcast daga sauran yankuna.”

Sakamakon hasashen cewa Afirka za ta zama ita ke da adadin jama’a mafi yawa na matasa zuwa shekarar 2050, akwai kyakkyawar makoma ga podcast.

Dumbin matasan Afirka za su zama manyan masu sauraren podcast.

Akwai 'yan Afirka da dama da suke amfani da damar da suke da ita intanet domin watsa labarai. Hoto/Reuters

Idan aka hada da sauran masu saurare daga wasu sassan Afirka, akwai tabbaci sosai kan cewa bangaren podcast na Afirka zai habaka.

Rubutu da fassara da shafin intanet da kirkirarriyar basira da podcast na bidiyo duk sun taimaka wa podcast samun sauyi zuwa wata hanya mai zaman kanta ta sadarwa.

Podcast ya kasance wani ginshikin sauyi ga kafofin watsa labarai na Afirka.

Yana kara bayar da karfin gwiwa ga ‘yan Afirka masu fasaha domin bayar da labarinsu tare da kalubalantar kafofin watsa labarai na gargajiya kan yadda suke bayar da rahoto kan Afirka da ‘yan nahiyar.

Ta hakan, podcast na wakiltar ‘‘yancin watsa labarai’ tsantsarta. Wannan ne ya sa kafar ke bukatar karin goyon baya daga Afirka.

Habaka a hankali

Akwai bukatar a tallata podcast a matsayin kafar watsa labarai. Akwai bukatar kwararrun masu podcast su fito da shawarar hada kai da sauran sabon shiga harkar podcast domin taimaka musu.

Wannan zai taimaka wurin habakar podcasting a nahiyar. A wani bangaren, akwai bukatar shugabannin podcasting da kamfanoni da gwamnatoci su yi aiki tare da masu podcast da ke zaman kansu domin habaka labaran Afirka.

Gwamnati za ta iya zuba jari a bangaren podcast da kuma nemo wasu hanyoyi na rage kudin intanet domin mutane su samu kallon podcast.

Daukar nauyi da zuba jari da kuma hada kai wajen bayar da labarai da shirye-shiryen podcast duk suna da muhimmanci.

Su ma masu saurare suna da rawar da za su taka wurin bayar da shawarwari masu kyau kan yadda za a habaka podcast domin ba su abin da suke so.

Idan muka yi aiki tare, za mu iya taimawa podcast ya habaka a Afirka.

Marubuciyar, Muzhinga Kankinda, mai samar da shirye-shirye ce a shafukan sada zumunta sa’annan tana daga wadanda suka tsara shirin The Economic Case of Investing na podcast.

A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.

TRT Afrika