Daga Wilma S. Nchito
Rahotannin da ake samu dangane da ƙarancin abinci a Afirka sakamakon yaƙe-yaƙe a wasu sassan duniya abu ne na damuwa.
Biranen Afirka na ɗumbin jama'a kuma an yi hasashen cewa zuwa shekarar 2026, kimanin mutum miliyan 722 za su rinƙa zama a cikin birane a nahiyar.
Biranen da ke nahiyar na ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale a wannan ƙarnin da ake ciki. Daga cikin matsalolin akwai batun matsalar ruwa da ƙarancin abinci wanda ke damun mutanen da ke cikin birane.
A daidai lokacin da ake samun ƙarin mutane da ke zama a cikin birane a faɗin duniya, inda kaso 50 cikin 100 na jama'ar Afirka ke zama a biranewanda dole ne su haƙura da ƙarin farashin kayayyaki da sauyin yanayi, akwai buƙatar birane su ƙra fito da tsare-tsaren samar da wadataccen abinci.
Kasashen da ke da rarar abinci, dole ne su magance matsalar tsauraran matakai da kuma irin matsalolin da dokokin ƙasa da ƙasa suka haifar waɗanda suke jawo wargajewar kasuwanni da ɓarnatar abinci.
Ƙarancin hanyoyin da suka haɗa garuruwa a nahiyar suna kawo cikas wurin jigilar abinci cikin sauƙi daga wuraren da ke da rarar abinci zuwa ga masu ƙaranci duk da cewa ƙasashen na da iyaka a tsakaninsu.
A 2020, an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan 281.6 da ke nahiyar na fama da yunwa inda adadi mai yawa na waɗannan mutanen suna a birane ne.
Akwai yarjejeniyoyi da dama na yankuna waɗanda ba a aiwatar da su ba haka kuma ana ci gaba da samun jinkiri wurin tsallakar da abinci ta kan iyakar ƙasashe. A ɗayan ɓangaren kuma sauyin yanayi na ƙara zama wata matsala ga ɓangaren samar da abincin.
Dole ne biranen Afirka su gaggauta nemo hanyoyin tsara tsarin abinci na birane domin inganta hanyoyin.
A tarihi, Afirka na da nau'in shukoki aƙalla 30,000 waɗanda da dama daga cikinsu za a iya girbe su. Sai dai waɗannan ba su kasance abubuwan da ake mayar da hankali a kansu ba ta ɓangaren noma ba.
Waɗannan nau'in abincin na gargajiya za a iya amfani da su domin cike giɓin abinci a birane.
Dole birane su tashi tsaye domin tunkarar wannan ƙalubale
Rashin tsari da umarni da ke ba da damar gano wuraren da aka samu nakasu ya haifar da yanayin da wasu sassan birnin za su samu rarar abinci yayin da wasu ke fama da rashin abinci.
Tambayar ita ce wa ke kula da jigilar abinci daga wurin da ake samar da shi zuwa masu saye?
Rashin kyakkyawan shugabanci a fannin abinci ya sa ƴan kasuwa na gargajiya da na zamani sun mamaye harkar baki ɗaya domin ƙoƙarin samun riba.
Ƴan kasuwar na gargajiya sun haɗa da manoma da yan sari da masu tireda ta kasuwa waɗanda duka ba su da tsari amma su ke da ruwa da tsaki wurin sayar da kayayyaki.
Ƴan kasuwar na birni su ne manoma masu sana'a da sauran ƴan sari na cikin birane da manyan shagunan zaɓi da kanka.
Tsarin abinci bai samu kyakyawan sa ido daga hukumomin birane da gwamnatocin tarayya ba sakamakon tsare-tsaren birane sun sha bamban da na karkara.
Ba a ware wata hukuma ba domin kai abinci zuwa birane kasancewar ana tsarawa ne tare da lura da harkar noma a gwamnatocin daga matakan yankin matakin kasa.
Yanayin cin abinci a matakin birni ana la'akari da shi a yayin da masu samar da abincin ke ƙoƙarin samar da adadin da ake buƙata
Bayan tsada da wadatar abincin yau da kullum a birane, babu wani tsayayyen tsari domin lura da abubuwan da suka shafi abincib, wadanda suka kunshi tun daga noma shi zuwan amfani da kayan abincin a gida.
Wannan ya sa bangaren abincin birane ya zama ba tare da wani tsari ba, wanda hakan ya sa masu ruwa da tsaki a ciki suke yadda suka ga-dama.
Wannan ya sa bangaren abincin birane ya zama ba tare da wani tsari ba, wanda hakan ya sa masu ruwa da tsaki a ciki suke yadda suka ga-dama.
Masu ruwa da tsaki a bangaren samar da abinci a birane ba su da tsarin ririta abin da ke hannu, da rage asara.
Wuraren noma a birane
Wuraren noma a birane Fadada birane da ake yawan yi na taimakawa wajen cinye gonakin da suke kusa. Wannan ya sa dole a rika kawo abincin daga wuraren masu nisa.
A tarihi, ana dan yin noma kadan-kadan a birane, wanda shi ne ya taimaka wajen samar da abinci a birane, amma sai dai yanzu ana fama da karancin gonakin.
Fadada da ake samu a birane sun sa dole daga bayan gari ne ake noma a kawo cikin biranen, wadanda su kansu karkarar suna fuskantar barazanar fadadar biranen.
Ya kamata hukumomi a kasashen Afirka su fara tanadin filaye a cikin birane domin noma. Sannan su rika shiga yarjejeniyar noma tare da samar da ingantaccen kasuwa da manoma za su rika sayar da amfanin gonakinsu.
Daga ciki akwai bukatar a samar da dokokin da za su kare muhalli, musamman wuraren da za a iya nomawa a cikin biranen.
Lura da dumamar yanayi da tsawaitar lokacin rani da ambaliya, akwai bukatar a gaggauta samar da tsare-tsare masu inganci domin kiyaye barazanar yunwa da ake fuskanta a gaba.
Akwai kuma bukatar a koma amfani da abincin da ake nomawa a cikin gida, maimakon yawan ta'allaka da abincin da ake shigowa da su.
Farfesa Wilma S. Nchito masani ne a tsarin birane, wanda ya nazarci yanayin cigaban da kasar Zambia ke samu.
Togaciya: Ra'ayi da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.