Daga Ozan Ahmet Cetin
A lokacin da Kwamitin Koli kan Masana'antun Tsaro a Turkiyya, wanda kwamiti ne da ke sa ido kan ɓangaren masana'antu da ke samar da kayan tsaro ya sanar da wannan aiki na Steel Dome a makon da ya gabata, hakan ya zama wani babban ci gaba ga ɓangaren tsaro na ƙasar.
A wata sanarwa da ofishin watsa labarai ya fitar, ya bayyana Steel Dome a matsayin wani abu wanda aka ƙirƙira domin inganta tsaro ta sama.
Haluk Gorgun, wanda shi ne sakataren masana'antun tsaro na Turkiyya, ya yi ƙrin bayani kan cewa babban burin wannan aikin shi ne tabbatar da cewa duka waɗannan makaman da sanso-sanso sun yi aiki tare, ta hanyar samar da makamin tsaro na sama daya wanda zai yi aiki. Ya kuma bayyana cewa wannan tsarin zai yi amfani da ƙirƙirarriyar basira domin taimakawa.
Steel Dome ɗin zai ƙunshi Radar da fasahar electro-optical waɗanda za su bayar da damar samar da na'ura ɗaya wadda za ta bi diddiƙi da ganowa da rarrabe yanayin makami idan an harba shi.
Steel Dome ya kasance wani tsari na musamman wanda yake nuna wani babban ci gaba ga masana'antun tsaro na Turkiyya.
Samar da wannan tsarin ba wai shi ne ƙarshe ba, sai dai wani abu da zai rinƙa samun ci gaba. Za a inganta ta har abada, tare da haɗa sabbin fasahohi yayin da suke fitowa.
Tuni dama Turkiyya ta samar da wasu muhimman sassa na Steel Dome. Sai dai kamar yadda jami'a suka jaddada, tsari ne da ke ɗauke da tsare-tsare kafin tabbatar da shi.
Akwai yiwuwar samun cikas kwatankwacin irin wanda aka samu a lokacin da aka yi aikin samar da wasu makaman tsaro irin su jirgin yaƙin nan ƙirar F-35.
Idan za a yi koyi daga irin waɗannan misalan, akwai buƙatar Turkiyya ta kula da irin ƙalubalen da ke tattare da irin wannan jinkirin, da kashe kuɗi da da kuma gazawa ta ɓangare ɗaya. Magance irin waɗannan matsalolin a cikin gaggawa za su iya taimakawa wurin samun nasara a wannan aikin.
Tafiyar Turkiyya wurin samar da tsarin tsaro na sama
Samar da tsaro ta sama na daga cikin abubuwan da Turkiyya ke damuwa a kai, musamman tun bayan da aka yi yaƙin Gulf a shekarun 1990 a lokacin da hare-haren makamai masu linzami suka yawaita.
Domin mayar da martani kan hakan, sai Amurka da Jamus da Netherlands suka kai kai makamin kakkabo da makami mai linzami na Patriot missile systems zuwa Turkiyya ƙarƙashin ƙungiyar NATO. Wannan aikin ya ci gaba inda NATO ta ci gaba da samar da makaman kakkaɓo makamai masu linzami waɗanda Turkiyya ke buƙata.
A shekaru 20 da suka gabata, Turkiyya ta sha fama da matsaloli na yanki waɗanda suka haɗa da rashin kwanciyar hankali da ƙaruwar rikici da kuma ƙara samun barazana daga gwamnatoci da ƙungiyoyi.
A ƙarƙashin wannan, sai Turkiyya ta yanke hukuncin samar da tsarinta na tsaro ta sama domin mayar da martani dangane da irin ƙalubalen da take fuskanta.
Wannan zai bayar da dama ga ƙasar ta kare sararin samaniyarta da kanta, ba tare da ta dogara dangane da matakin siyasa na NATO ba, wanda a wani lokaci take watsi da damuwar da Turkiyya ke da ita dangane da tsaro.
A shekarar 2006, Ankara ta ƙaddamar da shirin samar da T-LORAMIDS (Na'urar tsaro ta daƙile hare-haren makamai masu linzami masu gajere da dogon zango).
Zuwa shekarar 2010, an kammala fitar da tsare-tsaren yadda na'urar za ta kasance, da kuma kira ga kamfanoni su bayar shawarwari. Shirin ya jawo sha'awar kamfanoni da yawa na duniya waɗanda suka haɗa da: kamfanonin Amurka na Raytheon da Lockheed Martin waɗanda suka bayar da shawarar samar tsarin Patriot, kamfanin Eurosam wanda na haɗin gwiwar Faransa da Italiya ne ya bayar da shawara kan samar da SAMP-T, sai kuma kamfanin Rasha na Rosoboronexport ya bayar da shawarar samar da S-300, shi kuma na China na CPMIEC ya bayar da shawarar samar da FD-2000.
A 2013, bayan da Amurka ta ƙi amincewa da amfani da fasahar Patriot, sai Turkiyya ta ɗauki mataki a Satumbar 2013 domin sayen tsarin tsaro na sararin samaniya na China wato FD-2000.
Sai dai zuwa Nuwambar 2015, Turkiyya ta yi watsi da abin da za ta siya daga China, domin samar da shi a cikin ƙasarta. Haka kuma tattaunawa kan siyan Patriot daga Amurka ya bi ruwa.
A wannan lokacin, Turkiyya ta zuba jari matuƙa domin samar da makaminta na daƙile hare-hare ta sama wanda aka harbo daga zango mai tsawo ko gajere waɗanda suka haɗa da KORKUT da HISAR-A da HISAR-O da kuma SIPER.
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa, "Za mu kai wani mataki da za mu iya siyar da na'urorin tsaro na sama ga waɗanda suke bayar da uzuri daban-daban domin ƙin sayar mana."
Tsarin na Steel Dome yana wakiltar wani matakin ƙololuwa na wannan ƙoƙarin.
Na'urar daƙile hare-hare ta sama da aka haɗe wuri ɗaya
Steel Dome a turancin Ingilishi ya kasance abin da ake kira integrated air defence system (IADS), ya kasance na'urar daƙile hare-hare ta sama da aka haɗe wuri ɗaya, wanda tsari ne da ke ɗauke da sanso-sanso daban-daban da makamai da tsarin sadarwa wanda yake ganowa da bin diddiƙi da kuma kawara da duk wata barazana yadda ya kamata.
Komawa tsarin IADS daga tsarin da ake da shi na gargajiya na daƙile hare-hare na sama mataki ne mai ma'ana kuma wajibi ne, yayin da yake inganta tsarin daƙile hare-hare ta sama wanda ake da shi a halin yanzu domin maganace ƙalubalen da ake da su na yaƙi na zamani.
Tsarin na IADS na tabbatar da na'urar daƙile hare-haren ta sama na aiki a tare, yin amfani da ƙarfin kowane ɓangare tare da tare da ƙarfafa wanda yake da rauni.
Haɗe ɓangarori daban na sanso-sanso da na sadarwa a cikin IADS ɗaya na fitar da ainahin tsarin sararin samaniya. Wannan cikakken ra'ayi yana da muhimmanci don ganowa da ba da fifiko ga barazana daga sararin samaniya ta zamani, gami da jiragen sama na ɓoye da makamai masu linzami.
Haɗe gudanarwa da sarrafawa wuri ɗaya yana tabbatar da cewa ana amfani da makamin da ya dace kan kowace irin barazana, da kuma kare ɓarnatar da albarkatu.
Alal misali, tsari na musamman na SAM zai iya harbo makami kai tsaye, haka kuma ba tare da kashe kuɗi sosai ba haka kuma na'urori irin waɗannan a shirye suke su daƙile ƙananan barazana.
HAKIM, wanda shi ne kamfanin ƙasar na farko da ya soma ƙera kayayyakin tsaro na sararin samaniya, zai zama ƙashin bayan Steel Dome domin yin wannan aikin.
HAKIM, wanda baki ɗayansa injiniyoyin Turkiyya ne suka samar da shi, an samar da HAKIM domin taimakawa da haɗe sanso-sanso da makami wuri guda.
Ƙalubalen tsare-tsare da aka haɗe wuri guda
Duk da cewa Steel Dome, a matsayinsa na IADS, na da amfani sosai, hakazalika yana da ƙaluble da hatsari daban-daban da ke tattare da kayayyakin tsaro.
Kamar yadda duk wani tsari na kariya yake, haɗe duka wasu ɓangarori wuri guda na fito da ƙalubale daban-daban wanda sai an tsaya an kula da su domin tabbatar da cewa abubuwa sun tafi daidai.
IADS ya haɗe ɓangarori da dama a wuri guda waɗanda suka haɗa da - radar da makami mai linzami, da jirgin harbo da makami da kuma cibiyoyin kula da na'urorin.
Haɗe waɗannan abubuwan wuri guda na buƙatar amfani da manhaja mai kyau da kayayyaki da kuma yin gwaji sosai tare da kula.
Haɗe abubuwan wuri guda zai iya sakawa a samu matsaloli wurin gudanarwa, inda duk wani ɓangaren ke buƙatar magana da wani ɓangare.
Wannan ya kasance wani ƙalubale a lokacin da ake samar da F-35 project, wanda shi ma yake da irin waɗannan ƙalubalen, inda haɗe duka waɗannan abubuwan na fasaha ke buƙatar natsuwa da kuma gwaji iri-iri.
Samun jinkiri a wani bangare na na’urar ka iya jawo rugujewarsa, har ya shafi illahirin lokacin aikin.
Duk da haka, wasu sassan Steel Dome sun riga sun fara aiki. Halin daɗaɗɗen tsarin na’urar yakan haifar da farashi fiye da yadda ake tsammani.
Buƙatar ciyar da fasaha gaba ta hanyar inganta gwaji da haɓakar ƙima zai jawo kashe kuɗi.
Shirin F-35, alal misali, ya kai kusan dala biliyan 180 akan kiyasin farashin asali. IADS, tare da dogaro da na'urori masu auna firikwensin ci gaba da hanyoyin sadarwar sadarwa, da nagartaccen tsari da tsarin sarrafawa, farashinsu na saurin hauhawa.
Bayan haka, kula da IADS tsawon lokacin amfaninsa yana iya zama ƙalubale da tsada. Haɗe-haɗen yanayin tsarin yana nufin cewa duk wata haɓakawa ko gyara ga sashi ɗaya na iya buƙatar daidaitawa ga wasu.
Wani ƙarin ƙalubale shine rashin lahani ga hare-haren yanar gizo. Haɗa abubuwa da yawa a cikin tsarin guda ɗaya yana ƙara sararin samaniya don yuwuwar harin yanar gizo.
Tabbatar da tsaro ta intanet na IADS yana buƙatar sa ido akai-akai da sabuntawa, saboda rashin lahani a cikin tsarin ƙasa ɗaya na iya yin lahani ga duk hanyar sadarwa.
Aikin F-35 ya fuskanci irin wannan matsalar tsaro ta intanet, idan aka yi la'akari da yadda ya dogara da tsarin sadarwar da kuma raba bayanai mai yawa.
Aikin Steel Dome shaida ce ga ƙarfin haɓakar Turkiyya don haɓaka ƙwararrun hanyoyin tsaro waɗanda suka dace da ƙalubalen tsaro na musamman.
Duk da haka, nasarar aikin ba wai kawai ƙirƙirar fasaha ba ne har ma a kan tsara dabaru da hangen nesa.
Magance matsalolin da za su iya kawo cikas, irin su jinkirin ci gaba da hauhawar farashin kaya, da matsalar intanet, za su kasance masu muhimmanci don tabbatar da ingantaccen tsari da juriya a cikin dogon lokaci.